Ambaliyar ta hallaka mutum 30, 9,366 sun rasa muhalli a Jigawa

Sai dai hukumomi a jihar na ƙoƙarin tallafawa waɗanda lamarin ya shafa.

Ambaliyar ta hallaka mutum 30, 9,366 sun rasa muhalli a Jigawa

Hoton wata ambaliyar ruwa

Aƙalla mutum 30 ne suka rasu, yayin da wasu 9,366 suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa.

Ambaliyar ta lalata gonaki da kuma gidaje ku san 4,699.

Iftila’in na bana ya samo asali ne sakamakon mamakon ruwan sama, wanda ya shafi yankuna 90 a faɗin jihar.

Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasar (NIMET), ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi 18 na Jihar Jigawa, kuma hasashen ya tabbata.

Dokta Haruna Mairiga, Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Jigawa (JSEMA), ya sanar da cewa gwamnatin jiha tana taimaka wa wadanda abin ya shafa.

Taimakon ya haɗa da ba su buhun shinkafa, masara, gero, gari da kuma magani ga waɗanda ambaliyar ta raba da gidajensu.

Mairiga, ya ƙara da cewa yara biyu sun mutu, wasu kuma na fama da gudawa a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Makarantar Firamare ta Yanduna a Ƙaramar Hukumar Miga da Ayo.

Ya tabbatar da cewa kwamitin gaggawa na ƙananan hukumomi na aiki tuƙuru wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

Azumi Garba Tsakuwawa, wata da ke zaune a ƙaramar makarantar sakandaren ta Tsakuwawa, ta ce sun kwashe kwana uku ba tare da isasshen abinci ba, sai da taimakon gwamnati ya iso.

Azumi ta ce yaransu, sun kamu da zazzabi da wasu cututtuka.

Ta gode wa gwamnatin jihar saboda amsa kiraye-kirayensu, sannan ta roƙi jami’an gwamnati da ta tabbatar da cewa taimakon ya kai ga duk masu buƙata.

Aisha Yakubu Tsakuwawa, wadda ita ma ke zaune a ƙaramar makarantar sakandare ta Tsakuwawa, ta bayyana Iftila’in a matsayin abin da ba za a iya kaucewa ba, amma ta gode wa gwamnati kan ba su tallafi.

Ta ce ta rasa dukkanin kayanta da na ’ya’yanta a ambaliyar.

Mas’uda Nasiru Tsakuwawa, ta ce ambaliyar ta lalata musu dukiya gaba ɗaya, ta kuma gode wa gwamnan jihar bisa taimakon da aka kai musu.

Idi Inuwa daga Unguwar Arewa Tsakuwawa, cewa ya yi ambaliyar ta lalata duk kayansa, kuma ya yi kira ga gwamnati ta ci gaba da taimaka musu.

Wakilin Aminiya ya lura cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, tana aiki ba dare ba rana don tantance halin da ake ciki da kuma haɗa kai wajen ɗaukar matakan gaggawa.