Ambasada Mamman Daura ya kwanta

Allah Ya yi wa tsohon Darakta kuma Shugaban Hukumar Tallafa wa kasashen Waje (TAC), Ambasada Mamman Daura rasuwa. Marigayin ya rasu ne a shekaranjiya Laraba bayan doguwar jinya. Marigayin, wanda shi ne Sarkin Yakin Daura, ya taba zama Jakadan Najeriya a kasar Uganda na shekara takwas, kuma ya yi a kasashen Saudiyya da Koriya ta […]

Ambasada Mamman Daura ya kwanta

Allah Ya yi wa tsohon Darakta kuma Shugaban Hukumar Tallafa wa kasashen Waje (TAC), Ambasada Mamman Daura rasuwa. Marigayin ya rasu ne a shekaranjiya Laraba bayan doguwar jinya.

Marigayin, wanda shi ne Sarkin Yakin Daura, ya taba zama Jakadan Najeriya a kasar Uganda na shekara takwas, kuma ya yi a kasashen Saudiyya da Koriya ta Kudu da Beljiyom da Kamaru. Ya rike Shugaban Hukumar TAC har zango biyu, kafin ya ajiye a shekarar 2013.

Ya rasu ya bar mahaifiyarsa da matarsa da kuma ’ya’ya, cikinsu har da Manajan Al’amuran Kudi na Kamfanin Media Trust Ltd, mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam Nura Mamman Daura.

Allah Ya jikansa da rahama, amin.