Amfani 4 na kurkum ga lafiyar dan Adam

Cututtukan da amfani da kurkum ke hana kamuwa da su.

Amfani 4 na kurkum ga lafiyar dan Adam

Kurkum maganin gargajiya ne da ake amfani da shi ta hanyoyi masu tarin yawa, musamman a wajen kwalliya da gyaran fatar jiki.

Yawancin mutane sun fi sanin kurkum, wato turmeric a turance, a matsayin kayan gyaran fata, amma yana da amfani wajen kara lafiyar jikin mutum gaba daya, wanda yawancin mutane ba su sani ba.

Ga kadan daga ciki:

1 – Baya ga gyara fatar jiki, kurkum yana kawar da tabo, kyasfi da kuma kurajen fuska. Hakan ne ya sa ake yawan amfani da shi a kayan gyaran jikin amare da ’yan mata.

2 – Kariya daga cutar daji, daya daga cikin cuttutukan ke sanya kumburin jiki da kuma ajalin masu dauke da cutar. Kurkum yana dauke da sinadarai da ke bayar da kariya daga kamuwa da cutar daji na dogon lokaci.

3 – Kariya daga cutar suga. Kurkum na taimakawa wajen hana kamuwa ciwon suga. Shan kurkum yana rage yawan suga a jikin dan Adam, yana kuma samar wa jiki sinadarin insulin, da ke taimakawa wajen rage ciwon suga.

4 – Amfani da kurkum yana rage hadarin kamuwa da cuttutukan zuciya. Yana da kyau a rika cin danyensa ko kuma a abinci saboda yana dauke da sindaran da ke ba wa zuciyar mutum kariya daga daga cututttuka.