Amfani da fasahar na’ura mai qwaqwalwa wajen bibiyan bayanai zai magance ta’addanci – Hukumar NCC
Daraktan sashen hulda da jama’a na Hukumar NCC, Mista Tony Ojob ya ce amfani da na’ura mai qwaqwalwa wajen bibiyan al’amura zai taimaka wajen magance ta’addanci. Da yake jawabi a wajen taron qara wa juna sani na jami’an hulda da jama’a, wanda makarantar karatun hulda da jama’a ta qasa (NIPR) ta shirya a Legas, Ojobo […]
Daraktan sashen hulda da jama’a na Hukumar NCC, Mista Tony Ojob ya ce amfani da na’ura mai qwaqwalwa wajen bibiyan al’amura zai taimaka wajen magance ta’addanci.
Da yake jawabi a wajen taron qara wa juna sani na jami’an hulda da jama’a, wanda makarantar karatun hulda da jama’a ta qasa (NIPR) ta shirya a Legas, Ojobo ya ce bibiyan al’amura ta yanar gizo zai taimaka wajen bunqasa ayyukan kasuwancin Najeriya.
Ya kwakwanta yadda za a riqa bibiyan al’amuran da cewa za a riqa gane mutum ne ta hanyar lura da ababen da yake nunawa kamar hoto da dai sauransu.
A cewarshi “Yanzu ya fi sauqi a gane mutum ta yanar gizo, kuma na’ura mai qwaqwalwa wanda ke da manhajar da za a iya gane mutum.
“Yanzu ana fadada yadda ake gane mutum ta yadda zai hada da bibiyan ababen da ke da alaqa da wayar hannu da sauransu.
“Cigaba da ake samu a bangaren fasahar bayanai na yanar gizo ya nuna yadda za a bibiya al’amura cikin sauqi.
“Don haka, bibiyan al’amura a wannan bangaren, za a iya kiranshi da suna bibiya ta hanyar yanar gizo,” inji shi.
Ojobo ya qara da cewa sanin ainihin bayanan mutane ya zama wani jari ne yanzu, domin yanzu mutane suna qirqiran manhajan tattara bayanai da zai taimaka wajen gane ayyuka ko mutane.
Ya ce duk da cewa asalin yadda ake gane mutane shi ne ta lambobin sirri na password ko PINs da sauransu, amfani da hoton shatan hannu da qwayar ido shi ne mafi nagarta da aminci.
Hakanan kuma ya ce amfani da shatan hannu ya fi aminci wajen gano wanda ya aikata wani abu, don haka shi ne ya fi nagarta wajen yaqi da ta’addanci.
Ya ce saboda tunanin hakan ne yasa NCC ta qirqiro da rajistan layin waya a Najeriya a shekarar 2011, wanda aka kammala a ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2013.
“Dalilin da yasa muka qirqiro wannan shirin shi ne yadda ake amfani da wayar salula wajen ta’adi da kuma jami’an tsaro ke shan wahala wajen magance ta’adi.
“Shirin ya qunshi yin rajista cikakke da hoton shatan hannun mai wayar.
“Wannan shi ne manhajar tattara bayanan ’yan Najerita mafi inganci a yanar gizo wanda ya kai kimanin miliyan 133
“Ayyukan cigaban da ICT ta samar zai taimaka wajen tsabtace harkar kasuwanci.
“Masu amfani da yanar gizo a Najeriya sun kai kimanin miliyan 91.6 a watan Yuli na shekarar 2017. Wannan ya nuna cewa bibiyan ainihin mutane ta yanar gizo a Najeriya zai yi sauqi ta hanyar wayoyi salula,” inji Ojobo.
Ya ce yadda ake samun ci gaba a bangaren amfani da wayar salula a Najeriya zai taimaka wajen bibiyan al’amuran mutane, wanda kuma zai taimaka wajen yin kasuwanci.
Daraktan ya ce sayayya ta yanar gizo a shaguna, ta’ammali da bankuna, otel da sauransu wanda dole sai an bayar da ainihin bayanai yana samun ci gaba sosai a Najeriya.
A cewar mai magana da yawun Hukumar ta NCC, dole ne ayi amfani da fasahar ICT domin bibiyan ainihin bayanan mutane, sannan kuma bangaren ya taimaka wajen sauqaqe kasuwanci.