Amfani da man girki mara inganci na kawo ciwon zuciya —Masani

Masani ya bayyana cewa amfani da man girkin da ba a tantance ingancinsa ba na iya haddasa ciwon zuciya da sauran barazana ga lafiyar dan Adam

Amfani da man girki mara inganci na kawo ciwon zuciya —Masani

Masanin kiwon lafiya, Dokta Musa Adekunle ya gargadi ’yan Najeriya kan amfani da man girkin da ba a tantance ingancinsa ba, wanda ya bayyana cewa barazana ce ga lafiyarsu. 

Dokta Musa Adekunle wanda kwararre ne a fannin laifyar zuciya, ya bayyana cewa man girkin da ba a tantance ingancinsa ba zai iya kasancewa dauke da sinadarin cholesterol fiye da kima, da ma sauran abubuwa masu hadari.

A cewarsa, “Sinadarin cholesterol na iya jawo ciwon zuciya kamar yadda masana lafiya suka gano.

“Gidauniyar Kula da Zuciya ta Najeriya ta sha yin gargaɗi a kan amfani da irin waɗannan man girkin da ba a tantance ingancinsu ba.”

Da yake jawabi a wani taron wayar da kan al’umma game da lafiyarsu da aka yi a Abuja, likitan ya bayyana takaicinsa bisa yadda irin wadannan man girkin da ke jawo cututtuka masu alaka da zuciya, suke ci gaba da cin kasuwa a faɗin Najeriya.

Dokta Musa ya ce hakan barazana ce ga lafiyar mutane da dama da ba su ji ba, ba su gani ba.

A cewarsa, “Talauci da ya addabi kasar na taimakawa wajen rashin kiyayewa, inda dole mutane da dama suke amfani da abin da suka samu maimakon zaɓar abin da ya fi dacewa da lafiyarsu saboda neman sauƙi duk da cewa suna da matsala ga lafiyarsu.”

Ya ƙara da cewa kasuwanni a cike suke da man girki marasa alamar tantanacewa a jiki ko alamar kamfanin da suke tantance man, inda a cewarsa za a gan su ne kara zube.

Sai dai ya yaba da kamfanin Power Oil bisa kokarinsa na wayar da kan mutane a kan illar amfani da man girki da ba a tantance ingancinsa ba.

Kamfanin ya kuma kaddamar da fitaccen jarumin Kannywood Ali Nuhu a matsayin jakadansa na wayar da kan mutane a kan illar amfani da man girkin da ba a tantance ba.