Amfani da sinadarin Bitamin E, wajen gyaran jiki
Sinadarin Bitamin E yana nan kamar magani. Kuma za a iya samunsa a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya ko na koli. Sinadarin na gyara jiki sosai. Da yawa mata za su ga wannan sinadarin a shago amma ba su san amfaninsa ga jiki ba. A yau na kawo muku yadda za a yi […]
Sinadarin Bitamin E yana nan kamar magani. Kuma za a iya samunsa a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya ko na koli. Sinadarin na gyara jiki sosai. Da yawa mata za su ga wannan sinadarin a shago amma ba su san amfaninsa ga jiki ba. A yau na kawo muku yadda za a yi amfani da wannan sinadari wajen gyara jiki. Wannan sinadari na nan iri daban-daban amma zan lissafo muku yadda za a yi amfani da su. Kada a yi amfani da na sha wajen gyara fuska. A tabbatar da cewa, wanda za ku yi amfani da shi na magani ne kuma za a iya tantance su idan an tambaya a wajen masu sayar da magunguna.
- Bitamin E na ruwa:
A matso sinadarin a hannaye, sannan sai a shafa a fuska da daddare kafin a kwanta. Kada a sanya da yawa a fuska don kada maikon ya yi yawa a fuska. Wannan sinadari na gyara fuska da kuma rage kurajen fuska.
- Ruwan Bitamin E na gashi:
A bude sinadarin Bitamin E 2 ko 3 daidai tsayin gashinki. Sai a shafa man a gashi da kuma fatar kai. Sai a wanke gashin bayan minti 30 ko sa’a 1.
- Kwayar Bitamin E:
Wannan sinadarin ya fi amfani a jiki. A hadiye kwaya daya kullum na tsawon kwana 15. Yana taimakawa wajen sanya fata sheki da laushi, kuma yana sanya tsirar gashi da wuri.
- Man Bitamin E:
A matse ruwan man a cikin man shafawa, sannan sai a kwaba su. Man na gyara fatar jiki.
- Za a iya hada wannan sinadarin da man baki don samun lebe mai laushi.