Amfani da tafarnuwa wajen magance rubewar hakori

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon na kawo muku bayani kan yadda tafarnuwa ke magance rubewar hakori. Ina fata za a bi bayanin sau da kafa don cin gajiyarsa.An fara amfani da tafarnuwa ne a Yankin Asiya ta Tsakiya fiye da shekara dubu 6, ana amfani da ita a […]

Amfani da tafarnuwa wajen magance rubewar hakori
Amfani da tafarnuwa wajen magance rubewar hakori

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A wannan makon na kawo muku bayani kan yadda tafarnuwa ke magance rubewar hakori. Ina fata za a bi bayanin sau da kafa don cin gajiyarsa.
An fara amfani da tafarnuwa ne a Yankin Asiya ta Tsakiya fiye da shekara dubu 6, ana amfani da ita a bangaren abinci da kuma magani. A yanzu ana amfani da tafarnuwa a Gabas ta Tsakiya da Afirka da Nahiyar Amurka ta Kudu da ta Tsakiya da kuma Turai.
Yadda ake hada man tafarnuwa
A samu tafarnuwa sai saka ta a turmi, sai a zuba man zaitun, sannan a daka sosai, daga nan a tace da rariya ko tsumman da ake tatar gasarar koko, bayan an tace sai a ajiye man a cikin roba ko kwano.
Yadda za a magance rubewar hakori
Abubuwan bukata
Tafarnuwa
Turmi da tabarya
Yadda ake hadawa:
A samu danyar tafarnuwa, sai a daka ta a turmi, sannan sai goge hakori da ita ko kuma da ruwanta. Za a yi hakan ne sau uku a rana. Idan kuma hakori na ciwo, sai a diga ruwan tafarnuwar a kan hakori, za a yi hakan sau uku a rana.
A samu man tafarnuwa, sai a yi amfani da auduga, sannan a goge hakori, hakan na magance rubewar hakori, sannan na kara wa hakori karfi da kuma lafiya.