Amfani da tashoshi ruwa don safarar jiragen dakon kaya zai amfani Gwamnati da masu fito – Shugaban NSC
Babban Sakataren Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya, Barista Hassan Belllo, ya ce amfani da tashoshin jiragen ruwan Najeriya don safarar kayayyaki zai yi matukar amfani ga masu fito da tattalin arziki baki daya. Don cimma haka, Bello ya shawarci Kamfanin Maerskline Nigeria ya matso da jirgin dakon kayansa zuwa tashoshin jiragen ruwan Najeriya Babban […]
Babban Sakataren Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya, Barista Hassan Belllo, ya ce amfani da tashoshin jiragen ruwan Najeriya don safarar kayayyaki zai yi matukar amfani ga masu fito da tattalin arziki baki daya.
Don cimma haka, Bello ya shawarci Kamfanin Maerskline Nigeria ya matso da jirgin dakon kayansa zuwa tashoshin jiragen ruwan Najeriya
Babban Sakataren ya yi kiran ne lokacin da Manajan Daraktan Kamfanin Maerskline Nigeria, Mista Gildas Tobouo Tobouo ya kai ziyarar girmamawa ofishin Hukumar NSC a Legas.
Ya nanata kwarin gwiwarsa kan cewa idan aka yi cikakken amfani da tashoshin jiragen ruwan kasar nan don safarar sundukai zai yi matukar amfanar kowa, don haka ya bukaci karin hadin gwiwa tsakanin Hukumar NSC da Kamfanin Maerskline Nigeria, inda ya ce tashar jirgin ruwa za ta kara nagarta da tasiri ne idan masu ruwa-da-tsaki suka daddale matsalolin da suka addabi tashar tare da samar da mafita.
Bello ya jawo hankalin Manajan Daraktan kan wasu kalubalen da ke fuskantar tashoshin jiragen ruwan Najeriya, wadanda ya ce sun hada da sauke manyan sundukai a kan kari da rashin na’urorin tarairyar kaya da rashin tabbatar da gaskiya wajen aiwatar da ayyukan tashoshin, inda ya ce wasu daga cikin matsalolin za a iya shawo kansu ta hanyar hadin gwiwa da tatttaunawa.
Ya yaba wa Kamfanin Maerskline kan dimbin gudunmawar da yake bayarwa kan harkar sufurin jiragen ruwa a kasar nan, sannan ya yi kira kan a kara karfafa dabarun hadin gwiwa da kamfanin don hada-hadar tashar Teku-Huta ta Kaduna da sauran wuraren sauke sundukan da suka fito da mashigar ruwan kasar nan.
A jawabinsa, Tobouo ya bayyana shirin kamfanin, na ba Hukumar NSC goyon baya don cimma nasarorin mai da tashoshin masu dadin harka.
Ya yi maraba da hadin gwiwa da tattaunawar da hukumar ta tsara, sannan ya yi alkawarin ba da dukan gudunmawar da ta dace wajen bunkasa kasar nan.