Amfani da tawakkali wajen fuskantar fitina da jarrabawa (1)
Daga hudubar Sheikh Ibrahim bin Muhammad Al-HakilMasallacin Juma’a na Al-Mukil Hamdala da taslimi: Bayan haka, ku ji soron Allah Mdaukaki ku yi maSa da’a, kuma ku tsayar da addini a gare Shi, ku mika masa wuya ku mayar da hankalinku gare Shi. Domin babu wurin gudu face gudu zuwa gare Shi. Babu mai kubutarwa daga […]
Daga hudubar Sheikh Ibrahim bin Muhammad Al-Hakil
Masallacin Juma’a na Al-Mukil
Hamdala da taslimi:
Bayan haka, ku ji soron Allah Mdaukaki ku yi maSa da’a, kuma ku tsayar da addini a gare Shi, ku mika masa wuya ku mayar da hankalinku gare Shi. Domin babu wurin gudu face gudu zuwa gare Shi. Babu mai kubutarwa daga abubuwan ki face yin addu’a a gare Shi. Babu tabbata a kan gaskiya face da tabbatarwarSa. Babu karfi babu dabara ga bayi face naSa. “Ku da’a ga Allah kuma ku yi da’a ga Manzon (Allah), idan kuka juya baya abin sani babu wani abu a kan ManzonMu face isarwa mabayyaniya. Allah Wanda babu abin bautawa da gaskiya face Shi, kuma a kan Allah sai muminai su dogara.” (Tagabun:12-13).
Ya ku mutane! A lokacin da bakin ciki ya sauka ga bawa, bai damuwa da abinci ko abin sha ko barci, har sai ya kawar da ita ko ta gushe masa, zai yi ta neman wanda zai taimaka masa a kanta. Lokacin da mutanen Annabi Lud (AS) suka kewaye shi suna nufin yin ta’addanci ga bakinsa sai ya ce: “Ina ma ina da wani karfi (da zan hana ku) ko kuma in koma ga wani rukuni karfi (da za su taimake ni).” (Hud:80). Annabi (SAW) ya ce “Allah Ya yi rahama ga Lud. Hakika ya koma ga wani rukunin mai karfi.”Muttafakun. Yana nufin rukunin Allah Madaukaki wanda duk ya nemi tsari da Shi ba ya jin kunya. Hakika Lud (AS) da sauran Manzanni (AS) sun nemi tsari da Shi, kuma Allah Madaukaki Ya kubutar da su, kuma Ya halakar da masu karyatawa.
Lallai duniya gidan bala’i ne ga bayi, jarrabawa da wadata da tsanani. “Kuma za mu jarraba ku da sharri da alheri a matsayyin fitina, kuma gare Mu kuke komawa.” (Anbiya:35). Wannan bala’in daga ciki akwai wanda yake shafar mutum shi kadai kamar talauci da ciwo da damuwa da kunci da makamanansu. Daga ciki akwai bala’in da ke game jama’a ta shafi gari ko ta watsu ta shafi kasashe ko ta kasance mafi watsuwa ta shafi daukacin duniya.
Bisa lura da masdarinsa, bala’i na iya kasncewa kaddara yanke ta yadda dan Adam bai iya yin komai a kai, koda ta ksance saboda zunubansu ne ya same su kamar girgizar kasa da ambaliyar ruwa da annoba da makamantansu. Daga ciki akwai abin da ke aukuwa sakamakon zaluncin dan Adam ga dan uwansa, kamar jawo yunwa da talauci da asara da boye kaya da kai hare-hare da sauransu.
Wadannan masifu da bala’o’i suna karuwa kuma suna tagayyara muminai a tsawon zamunna, wannan saboda ka’idar nan ce a wannan sha’ani da ke cewa “Babu wata shekara face mai biye mata ta fi ta sharri, har sai kun koma ga Ubangijinku.” Kamar yadda Annabi (SAW) ya ba da labarin haka.
Idan aka lura bala’o’in wannan lokaci aka lura da masifun a jumlatance, aka bibiye su, za a ga bala’o’i ne da suke shafar mutane da yawa, suna kawo sauye-sauye masu girma, ja’ircinsu na kawo halaka mai yawa da talauci da wargajewar al’amura, masu zuba jari su rasa dukiyarsu baki daya ko mafi yawanta, tsoro mai tsanani ya lizimce su, suna haifar da masifu masu yawa da dayansu ke buwayar masu karfi, to ina ga a ce dukkansu sun hadu?
A lokacin da wadannan masifu suka rika maimaituwa a kasashe da dama, sai wadanda ba su isa gare su ba, su rika tsoron haduwa da su, musamman idan masana da kwararru suka ba da labarin cewa bala’i da annoba da alamun ambaliya ko girgizar kasa suna karuwa, inda masana rayuwa da harkokin siyasa da masu hangen nesa za su hadu kan cewa za a fuskanci matsaloli a fagen tattalin arziki da siyasa da zamanakewar kasa nan gaba.
Don haka babu abin zargi a kan mutane idan suka ji tsoro kan rayuwarsu da ’ya’yansu da gidajensu da dukiyarsu, suka rika tunanin abin da zai faru da su a gaba. Domin jin dadin rayuwa tana tare da zama lafiya ne a koyaushe, kamar yadda tabarbarewar rayuwa ke tare da susucewar zaman lafiya da azabar rayuwa da tashin hankali. Sai dai duk da haka, lallai muminai suna da wurin fakewa da suke komawa a gare shi. Idan suka nemi tsari da shi, shi mai tsarewa ne, idan suka lizimce Shi, zai lizimce su. Shi ne ke ba da kariya idan rayukan da suka samu kansu a matsala suka samu ikon yin imani da shi. Zukatansu suka natsu da shi, koda sauran mutane sun kauce masa.
Lallai wannan abu shi ne tawakkali (dogaro) ga Allah Madaukaki. Duk lokacin da zuciyar bawa ta kullu a kan imani da yakini, ta cika da tawakkali ga Allah, ba ta ta’allaka da kowane sababi ko yaya yake, ba ta kwadayin komai daga wanin Allah Madaukaki, ba ta tsoron waninSa. Ya zamo zuciya tana sane da cewa duk abin da ya auku bisa kaddararSa ce Madaukaki, kuma dukkan komai yana karkashin tankwarawarSa da karfinSa Mai girman daraja. Suna masu mika wuya ga hukuncinSa da umarninSa Madaukakin Sarki. A lokacin ne rayuka za su samu hutu su iya magance bala’insu, kirjinsu ya fadada zukatansu su samu natsuwa, ba su tsoron kowa, ba su tsoron aukuwar komai, hakika Allah Madaukaki Ya ce: “An kankare musu kananan zunubansu, kuma an kyautata rayuwarsu.” (Muhammad:2).
Duk wanda aka kyautata balunsa, sai tunaninsa ya daidaitu shu’urinsa ya daidaitu, zuciyarsa da lamirinsa su natsu, ransa ya samu aminci da zaman lafiya.
Za mu cigaba insha Allah