Amfanin cin fara ga lafiyar jiki

Amfanin cin fara ga lafiyar dan Adam.

Amfanin cin fara ga lafiyar jiki

Fara na daga cikin dangin kwari, amma duk da haka, cin ta na da  amfani ga jikin dan Adam kamar sauran dabbobi.

Ana cin fara a sassan duniya daban-daban tun daga nahiyar Turai har zuwa Afirka da Asiya.

A nan Najeriya ana cin farar sosai, ta yadda har a yankin Jihar Borno wasu sun dauke ta matsayin abin marmari da kusan kowa ke ci.

Akan soya farar kamar yadda ake soya nama, amma sai an fara tafasa ta kafin a zuba kayan hadi sannan a soye ta.

Fara na dauke da sinadaran vitamin A, B da D, wadanda duk suna taka muhimmiyar rawa wajen gina jiki.

Bugu da kari, fara na dauke da sinadarin Protein wanda yawansa har ya fi wanda yake cikin kifi da nama.

Wani babban likita a kasar Meziko, Dokta José Pino, ya tabbatar cewa fara na dauke da kashi 62.93 cikin 100 na sinadarin Protein, wanda kashi 89.63 cikin 100 dinsa ke bin lafiyar jiki.  

Har ila yau fara na dauke da sinadaran calcium, magnesium da zinc wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen gina kashi.