Amfanin itacen ‘sandalwood’ wajen gyaran fata
‘Sandalwood’ itace ne da ake amfani da shi domin hada turaren wuta. Bincike ya nuna cewa amfani da jan itacen ‘sandalwood’ da zuma na magance tabon fuska da kuma na jiki ko da tabon babba ne. Wannan hadin kuma na magance kurajen fuska sakamakon gumi da kuma zafin rana. Garin sandalwood na kara hasken fata […]
‘Sandalwood’ itace ne da ake amfani da shi domin hada turaren wuta. Bincike ya nuna cewa amfani da jan itacen ‘sandalwood’ da zuma na magance tabon fuska da kuma na jiki ko da tabon babba ne. Wannan hadin kuma na magance kurajen fuska sakamakon gumi da kuma zafin rana. Garin sandalwood na kara hasken fata ga wadanda ke amfani da shi a matsayin hoda. Za a iya samin wannan itacen a Maiduguri saboda yawan amfani da turaren wuta da suke yi.
Abubuwan da za a bukata
· Jan itacen sandalwood
· Zuma
Hadi:
Idan an sami itacen sandalwood, sai a daka shi a kuma tankade kamar hoda. Za a iya amfani da shi a matsayin hoda. Za kuma a iya kwaba shi da zuma. Bayan haka, sai a shafa a fuska safe da yamma kafin a kwanta barci. Idan an shafa hadin, sai a bar shi tsawon minti 30 kafin a wanke da ruwan dumi.