Amfanin karas ga fata

Assalamu alaikum ‘yan uwana mata. Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Kamar yadda aka sani cewa karas na dauke da sinadarin bitamin A domin gyara ido da kuma ganin mutum. Bayan haka, akwai abubuwa da yawa da karas yake yi domin inganta fata. Domin sanin mahimmancin karas, shi ya […]

Amfanin karas ga fata
Amfanin karas ga fata

 KarasAssalamu alaikum ‘yan uwana mata. Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Kamar yadda aka sani cewa karas na dauke da sinadarin bitamin A domin gyara ido da kuma ganin mutum. Bayan haka, akwai abubuwa da yawa da karas yake yi domin inganta fata. Domin sanin mahimmancin karas, shi ya sa a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da shi domin magance cututtukan fata da dama.
•Cin karas na sanya fata sheki da laushi ga kuma gyara ido domin yana dauke da sinadarin bitamin A da wadansu sinadaren gyara jiki.
• A markada karas sannan a sha ruwansa domin magance tabon fuska da kuma sanya ciwon fata warkewa da wuri.
•  Karas na dauke da bitamin A, shi ya sa yake taimakawa wajen rage tsufan fata. Don haka ana yawan markada shi a shafa a fata ko kuma a sha a kalla kullum a rana.
•Shan jus din karas (markadadden rowan karas), musamman lokacin zafi na magance tabon rana da yake fesowa a fuska. Sai a ga fuska ta yi dabbare-dabbare launi daban-daban. Yana da kyau a  yawaita shan jus din a lokacin zafi.
•Rashin cin kanwa a abinci na janyo gautsin fata, don haka sai a shan jus din karas domin samun fata mai sulbi.
•Domin sinadaren da karas ke dauke da su, yana taimakawa wajen magance kurajen fuska da sauransu. Fesowar kurajen na faruwa ne idan an rasa sinadarin bitamin A a fata. Don haka sai a ci karas. Amma yawan cin karas na iya canza launin fata.
•Idan an ji ciwo za a iya shafa dakakken karas a wurin domin yana taimakawa wajen warkar da ciwo.
• A markada karas sannan a zuba madara da zaitun kadan da zuma, sannan a kwaba a shafa a fuska na tsawon mintuna 30. Hakan na magance fesowar kurajen fuska.