Amfanin karas ga fata
Assalamu alaikum ’yan uwana mata. Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Kamar yadda aka sani cewa karas na dauke da sinadarin bitamin A domin gyara ido da ganin mutum, bayan haka, akwai ababe da yawa da karas yake yi domin inganta fata. Domin sanin muhimmancin karas, shi y asa […]
Assalamu alaikum ’yan uwana mata. Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Kamar yadda aka sani cewa karas na dauke da sinadarin bitamin A domin gyara ido da ganin mutum, bayan haka, akwai ababe da yawa da karas yake yi domin inganta fata. Domin sanin muhimmancin karas, shi y asa a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da shi domin magance cututtukan fata da dama.
- Cin karas na sanya fata sheki da laushi ga kuma gyara ido domin yana dauke da sinadarin bitamin A da wasu sinadaran gyara jiki.
- A markada karas a sha ruwansa domin magance tabon fuska da kuma sanya ciwo a fata warkewa da wuri.
- Karas na dauke da bitamin A don haka yana taimakawa wajen rage tsufar fata. Don haka a rika yawan markada shi a shafa a fata ko a sha akalla kullum a rana.
- Shan jus din karas musamman lokacin zafi na magance tabon rana da yake fesowa a fuska. Sai a ga fuska ta yi dabbare-dabbare launi daban-daban. Yana da kyau a yawaita shan jus dinsa a lokacin zafi.
- Rashin cin kanwa a abinci na janyo gautsin fata don haka, sai a rika shan jus din karas domin samun fata mai sulbi.
- Domin sinadaran da karas ke dauke da su, yana taimakawa wajen magance kurajen fuska da sauransu. Fesowar kurajen na faruwa ne idan an rasa sinadarin bitamin A a fata don haka sai a ci karas. Amma yawan cin karas na iya canja launin fata.
- Idan an ji ciwo za a iya shafa dakakken karas a wurin domin yana taimakawa wajen warkar da ciwo.
- A markada karas sannan a zuba madara da zaitun kadan da kuma zuma sannan a kwaba a shafa a fuska na tsawon minti 30. Hakan na magance fesowar kurajen fuska.