Amfanin lalle a fatar jiki
Barkanmu da sake haduwa a wannan fili na kwalliya. Shin kun san cewa amfani da lalle ko ruwansa na taimakawa wajen gyaran fata da kuma magance cututtukan fata? Lalle na dauke da sinadaran bitamin C da K don haka, yana magance amosanin ka da kara cikar gashi da kuma dada tsawon gashi. Lalle na kara […]
Barkanmu da sake haduwa a wannan fili na kwalliya. Shin kun san cewa amfani da lalle ko ruwansa na taimakawa wajen gyaran fata da kuma magance cututtukan fata? Lalle na dauke da sinadaran bitamin C da K don haka, yana magance amosanin ka da kara cikar gashi da kuma dada tsawon gashi. Lalle na kara hasken fata da kuma sanya sulbinta. Idan ba a damu da amfani da shi ba, ya kamata a fara domin amfana da shi.
• kurajen fuska: Idan kuraje musamman kanana masu yawan naci suka feso a fuska, a samu garin lalle sannan a zuba tafasasshen ruwa kadan a ciki da man zaitun da kuma gunduwar kwai sannan a kwaba sai a shafa a fuska na tsawon minti goma zuwa sha biyar sannan a wanke. Yana da kyau a rika yin haka kamar sau daya a mako domin samun fata mai sulbi.
• Don kwalliya: A samu jan lalle a kwaba da lemun tsami da man lalle sannan a shafa a tafin kafa ko fata na tsawon awa uku sannan a wanke da ruwa. Yin hakan na kare mutum daga sihiri da kuma gyara fatar tafin hannu da kuma ta kafa.
• Amosanin ka da cikar gashi: A kwaba lalle da dan ruwa amma ba sosai ba sannan a tsaga gashin ka a zuba a fatar kai kowane sako sannan a rufe gashin da leda na tsawon minti talatin sannan a wanke da ruwan dumi da kuma man wanke gashi domin samun cika da tsawo da kuma warkar da amosanin ka.
• Hasken fuska: A samu ruwan lalle sannan a rika shafawa a fuska a kullum da auduga kafin a shiga wanka. Yana da kyau idan an shafa ruwan a fuska sai a rika dada wani ruwan a kan fuskar da zarar ya bushe har tsawon minti goma domin samun sakamako mai kyau sannan a wanke fuska a shiga wanka. Za a iya yin wanka da ruwan lalle idan amarya ce ana shirin yin aure domin dada hasken fatar baki daya.
• Man lalle: Amfani da man lalle a fatar kai ko lokacin kitso ba karamin dada tsayin gashi yake yi ba. Za a iya samun man gashin kai a manyan shagunan da ke sayar da man kwalliya. Za a iya ganin sakamako cikin mako biyu zuwa uku da fara amfani da hadin.