Amfanin lallen gargajiya

Bincike ya nuna amfani da lalle ko ruwansa na taimakawa wajen gyaran fata da kuma magance cututtukan fata.

Amfanin lallen gargajiya

Mata da yawa a wannan zamani sun koma yin amfani da lallen zamani da ake shigowa da shi daga kasashen waje, wanda ake kwabawa da wani ruwan sinadari da kan zo tare da lallen a cikin wani mazubi a cikin kwali. Duk da irin wannan sauyi da zamani ya zo da shi, amma har yanzu mata da dama sun gwammace, su yi amfani da lalle na asali, wanda aka gada tun kaka da kakani kuma ake shukawa a gonaki.

Ana shuka lalle ne a wuraren da ke da zafi. Yanayin ruwa da zafin wuri ke nuna kyawun launin lalle. Lalle dai tsiro ne da bai faye girma sosai ba kuma ganyensa ne ake amfani da shi bayan an busar da shi, an mayar da shi gari.

Bincike ya nuna amfani da lalle ko ruwansa na taimakawa wajen gyaran fata da kuma magance cututtukan fata. Lalle na dauke da sinadaran bitamin C da K, don haka yana magance amosanin ka da kara cikar gashi da kuma dada tsawon gashi.

Lalle na kara hasken fata da kuma sanya sulbinta. Idan ba a damu da amfani da shi ba, ya kamata a fara domin amfana da shi.

Amfanin lalle

Lalle yana da matukar amfani. Wasu daga cikin sun hada da:

Ciwon kafa

Yin lalle a kafa na rage ciwon kafa da kaushin kafa. A kwaba lalle da ruwa ya yi kauri, a shafa wa kafar na tsayon lokacin da ake bukata, sannan a wanke. Yin haka na rage radadi da zugin da ke damun mutun a kafarsa.

Dattin ciki

Shan ruwan lalle na wanke dattin da ke ciki. Idan aka jiga lalle da ruwa a tace, sai a sha ruwan daidai gwargwado. Yin hakan na wanke dattin ciki.

Gyaran fata

Ana amfani da lalle wajen gyara fatar jiki da kawar da datti da kuma sanya fata haske mai kyau. Domin haka, sai a zuba lalle da ruwa a rika wanka da ruwa lallen akalla sau daya a rana.

Fatar fuska

Lalle na sa fuska ta yi laushi da haske. Bayan an kwaba lallen da kauri a rika gogawa a fuska. Bayan minti 20 zuwa 30 sai a wanke fuskar da ruwa. Za a iya yi sau daya zuwa uku a rana.

Kurajen fuska

Ga masu fama da kurajen ‘pimples’ sai su kwaba lalle da ruwan lemon tsami ya yi kauri, suka rika shafa kwabin a fuskar. Zuwa wani lokaci kurajen za su bace.

Amosanin kai

Ana a wanke gashin kai da ruwan lalle, domin maganin amosanin gashi. Ana yin hakan ne, ta hanyar kwaba lalle a ruwa ya yi dan ruwa-ruwa, sannan a jika gashin a cikin ruwan. Bayan minti 20 sai a wanke kan. Yawan yin hakan na kashe amosanin kai.

Ciwon yatsa (kakkare)

Masu gyambon yatsa na amfani da lalle wajen neman sauki. A kan kwaba shi a sanya a wurin da ke da gyambon a yatsan, don neman waraka ko busar da shi.

Kwalliyar gashi

Maza da mata na amfanin da shi, domin kwaliya a gashin kansu da kuma gemu. Domin yin hakan, sai a kwaba lalle da ruwa a shafa a waurin da ake bukata na ‘yan mintuna, sannan a wanke.

Zayyana fata

Ana kuma amfani da lalle wajen yin ado ta hanyar yin zayyana a fatar jiki. A kan kwaba lalle ya yi kauri, sannna a lika leda mai dauke da nau’in zayyanar da za a yi a fatar, sannan a shafa lallen a sama.

Daga nan sai a bar shi ya yi awanni kafin a wanke. Ana kuma iya yin zayyarar kai-tsaye da kwababben lallen ba tare da sanya ledar ado ba.

Kananan kurajen fuska

Idan kuraje, musamman kanana masu yawan naci suka feso a fuska, a samu garin lalle sannan a zuba tafasasshen ruwa kadan a ciki da man zaitun da kuma kwanduwar kwai, sannan a kwaba sai a shafa a fuska na tsawon minti goma zuwa sha biyar, sannan a wanke. Yana da kyau a rika yin haka kamar sau daya a mako, domin samun fata mai sulbi.

Kwalliya

A samu jan lalle a kwaba da lemon tsami da man lalle sannan a shafa a tafin kafa ko fata na tsawon awa uku, sannan a wanke da ruwa. Yin hakan na kare mutum daga sihiri da kuma gyara fatar tafin hannu da kuma ta kafa.

Amosanin ka da cikar gashi

A kwaba lalle da dan ruwa, amma ba sosai ba sannan a tsaga gashin ka, a zuba a fatar kai a kowane sako, sannan a rufe gashin da leda na tsawon minti talatin, sannan a wanke da ruwan dumi da kuma man wanke gashi, domin samun cika da tsawo da kuma warkar da amosanin ka.

Hasken fuska

A samu ruwan lalle sannan a rika shafawa a fuska a kullum da auduga kafin a shiga wanka. Yana da kyau idan an shafa ruwan a fuska sai a rika dada wani ruwan a kan fuskar da zarar ya bushe har tsawon minti goma, domin samun sakamako mai kyau, sannan a wanke fuska a shiga wanka. Za a iya yin wanka da ruwan lalle, idan amarya ce da ake shirin yi mata aure, domin dada hasken fatar baki daya.

Man lalle

Amfani da man lalle a fatar kai ko lokacin kitso ba karamin dada tsayin gashi yake yi ba. Za a iya samun man gashin kai a manyan shagunan da ke sayar da man kwalliya. Za a iya ganin sakamako cikin mako biyu zuwa uku da fara amfani da hadin