Amfanin man lemon tsami a jiki da fata da kuma yadda ake hada shi

Man lemon tsami yana da mahimmanci sosai musamman ma a fata. Domin yana dauke da sinadarin bitamin C. Wannan sinadarin kuma yana kara lafiya ne a jiki da fata. Man yana warkar da kurajen fuska da kwarkwata. Yana taimakawa wajen kara wa fatar fuska haske ba tare da yin bilicin ba. Uwa uba kuma yana […]

Amfanin man lemon tsami a jiki da fata da kuma yadda ake hada shi
Amfanin man lemon tsami a jiki da fata da kuma yadda ake hada shi

Man lemon tsami yana da mahimmanci sosai musamman ma a fata. Domin yana dauke da sinadarin bitamin C. Wannan sinadarin kuma yana kara lafiya ne a jiki da fata. Man yana warkar da kurajen fuska da kwarkwata. Yana taimakawa wajen kara wa fatar fuska haske ba tare da yin bilicin ba. Uwa uba kuma yana taimakawa wajen magance mura. Ana amfani da man ‘sunscreen’ idan za a shiga rana. Kada a shiga rana da man lemon tsami a fuska domin zai iya illata fatar. Don haka an fi son a shafa shi da safe ko da yamma domin samun sakamako mafi inganci.

Yadda za a hada man lemon tsami
A samu lemon tsami sai a bare fatar kada a yi amfani da ruwan lemon tsami wajen hada man lemon tsami. Sannan sai a samu man kwa-kwa (idan ba a manta ba, mun rubuto muku yadda ake hada man kwa-kwa kwanakin baya).
Bayan an bare bawon, sai a shanya a karkashin fanka kamar tsawon awa daya. Bayan ya dan bushe, sai a saka a gora sannan a zuba man kwa-kwa a gauraya bawan da man a gorar sannan a rufe.
Sai a samu gurin da babu rana ko daki ko kicin a ajiye kamar tsawon sati biyu. Amma a kullum a rika zuwa ana girgizawa. Shi ke nan! Man lemon tsami ya samu.
Za a iya amfani da man zaitun ma idan babu man kwa-kwa.
Idan ba za a iya bin wanyan hanyar ba akwai wata hanya da za a bi don hada man lemon tsami.
A sa bawon a tukunya sannan sai a zuba man kwa-kwa a dora a wuta amma kada wuta ta yi yawa. A rika gaurayawa tsawon minti biyar. Bayan haka, sai a sauke ya huce sannan sai a zuba a kwalba.