Amfanin man zaitun wajen gyaran gashi
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda za ku yi amfani da man zaitun wajen gyaran gashi. Man zaitun na da matukar muhimmanci a jikinmu. Ana amfani da shi a matsayin man kitso.Da farko a samu man zaitun mai […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku bayanin yadda za ku yi amfani da man zaitun wajen gyaran gashi.
Man zaitun na da matukar muhimmanci a jikinmu. Ana amfani da shi a matsayin man kitso.
Da farko a samu man zaitun mai kyau, sai a sanya shi a murhun zamani da ake kira ‘microwabe’ ko a sanya a cikin tukunya, sai a dora shi a murhu, sannan a bar shi ya yi dumi kamar tsawon minti 10.
• Daga nan a rika amfani da hannu wajen dibar man zaitun din ana shafa wa shi a karkashin gashin kai. Haka za a rika shafawa har sai gashin ya gaurayu da man gaba daya.
• A tabbata gashin a tsefe yake, sai a rufe shi da hular leda kamar na tsawon minti talatin.
• Bayan minti talatin, sai a wanke kan da man ‘shampoo’ da na ‘conditioner’.
Idan aka ci gaba da wanke gashin kai za a samu canji, domin gashin zai zama mai sheki da santsi da laushi da kuma tsayi.