Amfanin ruwan ‘glycerin’ domin kwalliya
Ruwan glycerin na da matukar muhimmanci a fatarmu, musanman a wannan lokaci na damina. Za a iya amfani da wannan ruwa ta hanyoyi da dama kamar ta harkar fata da kuraje da tabo da kyasfi da sauransu. Ko na taba gaya muku cewa sanyi da hunturu na lahanta fata wanda ba a shafa mata mai? […]
Ruwan glycerin na da matukar muhimmanci a fatarmu, musanman a wannan lokaci na damina. Za a iya amfani da wannan ruwa ta hanyoyi da dama kamar ta harkar fata da kuraje da tabo da kyasfi da sauransu. Ko na taba gaya muku cewa sanyi da hunturu na lahanta fata wanda ba a shafa mata mai? Ya kamata a dage da tsaftace jiki sosai musamman a wannan lokacin in ba haka ba, sai mutum ya fita kamanninsa.
• A hada ruwan ‘glycerin’ da zuma sannan a dinga shafawa a fuska da wuya sannan a jira da tsawon mintuna 20 kafin a wanke da ruwan sanyi domin magance gautsin fata da hunturu.
• Za a iya hada wannan ruwan da madara da zuma da kuma’oats’; cokali daya na glycerin da cokula biyu na zuma sannan a kwaba sosai kamin a sanya ‘oats’ sai a shafa a fuska domin samun fuska da fata mai sheki.
• Domin magance kyasfi kuwa, za a iya shafa ruwan zalla a inda a ake fama da kyasfin na tsawon watanni uku a kullum safe da yamma.
• A surka ruwan ‘glycerin’ da ruwa kadan kafin a shafa a kan tabo ko ciwo. Hakan na hana fitowar tabo. In kuma tabo ta fito zai iya bacewa, amma yana daukar dan lokaci kafin ya bace.
•Ruwan ‘glycerin’ na magance fitowar kurarraji a fuska. Za a iya shafawa a fuska a mayar da shi kamar man shafawa domin samun sakamako mai kyau.