Amfanin sinadarin bitamin E wajen gyaran jiki

Sinadarin bitamin E yakan taka muhimmiyar rawa yayin gyaran jiki. Kuma za ki iya samunsa a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya ko na koli. Sinadarin na gyara jiki sosai. Da yawa mata za su ga wannan sinadarin a shaguna, amma ba su san amfaninsa ga jiki ba. A yau mun kawo miki yadda […]

Amfanin sinadarin bitamin E wajen gyaran jiki
Amfanin sinadarin bitamin E wajen gyaran jiki

Sinadarin bitamin E yakan taka muhimmiyar rawa yayin gyaran jiki. Kuma za ki iya samunsa a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya ko na koli. Sinadarin na gyara jiki sosai. Da yawa mata za su ga wannan sinadarin a shaguna, amma ba su san amfaninsa ga jiki ba.
A yau mun kawo miki yadda za ki yi amfani da wannan sinadarin wajen gyara jikinki. Sinadarin ya kasu kashi-kashi, don haka za mu lissafo miki da kuma yadda za ki yi amfani da su. Kada ki yi amfani da na sha wajen gyara fuskarki. Ki tabbata wadanda za ki yi amfani da su ana amfani da su ne wajen gyaran jiki.
·         Sinadarin bitamin E serum: Ki matsa sinadarin a hannuwanki, sannan sai ki shafa a fuskarki da daddare kafin ki kwanta. Kada ki shafa da yawa a fuskarki don kada maikon ya yi yawa. Wannan sinadarin na gyara fuska da kuma rage kurajen fuska.
·         Serum na gashi : Ki bude sinadarin bitamin E2 ko 3 daidai tsawon gashinki. Sai ki shafa man a gashinki da kuma fatar kanki. Sai ki wanke gashin bayan minti 30 ko awa daya.
·         Supplement na sinadarin bitamin E: Wannan sinadarin ya fi amfani a jiki. Ki hadiye kwaya daya kullum na tsawon kwanaki 15. Yana taimakawa wajen sanya fata sheki da kuma laushi; yakan kuma sanya gashi ya tsiro da wuri.
·         Man sinadarin bitamin E: Ki matse ruwan sinadarin a cikin man shafawarki, sannan sai ki kwaba su . Man na gyara fatar jiki.
·         Za ki iya hada wannan sinadarin da man baki don samun leba masu laushi.