Amfanin sinadarin Bitamin E wajen gyaran jiki
Sinadarin Bitamin E yana nan kamar magani. Kuma za a iya samunsa a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya ko na koli. Sinadarin na gyara jiki sosai. Da yawa mata za su ga wannan sinadarin a shago amma ba su san amfaninsa a jiki ba. A yau na kawo maku yadda za a yi […]
Sinadarin Bitamin E yana nan kamar magani. Kuma za a iya samunsa a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya ko na koli. Sinadarin na gyara jiki sosai. Da yawa mata za su ga wannan sinadarin a shago amma ba su san amfaninsa a jiki ba.
A yau na kawo maku yadda za a yi amfani da wannan sinadarin wajen gyaran jiki. Wannan sinadarin na nan daban-daban amma zan lissafo maku yadda za a yi amfani da su. Kar a yi amfani da na sha wajen gyaran fuska. A tabbata cewa wanda za ku yi amfani da shi na magani ne kuma za a iya tantance su idan an tambaya a wajen masu sayar da magani.
- Sinadarin Bitamin E Serum: A matso sinadarin a hannaye, sannan sai a shafa a fuska da dare kafin a kwanta. Kar a sanya da yawa a fuska don kar maikon ya yi yawa a fuska. Wannan sinadarin na gyara fuska da kuma rage kurajen fuska.
- Serum na gashi : A bude sinadarin Bitamin E 2 ko 3 dai-dai tsayin gashinki. Sai a shafa man a gashi da kuma fatar kai. Sai a wanke gashin bayan mintuna 30 ko awa daya.
- Supplement na sinadarin Bitamin E: wannan sinadarin ya fi amfani a jiki. A hadiye kwaya daya kullum na tsawon kwanaki 15. Yana taimakawa wajen sanya fata sheki da kuma laushi. Kuma yana sanya tsirowar gashi da wuri.
- Man sinadarin Bitamin E: A matse ruwan sinadarin a cikin man shafawa, sannan sai a kwaba shi man na gyara fatar jiki.
- Za a iya hada wannan sinadarin da man baki don samun lebba masu laushi.