Amfanin ’ya’yan itatuwa hudu a jiki

A yau na kawo muku yadda ake amfani da ’ya’yan itatuwa hudu; lemu da kankana da mangwaro da kuma abarba, domin inganta fata da kuma haskaka ta. Mata da dama na zuwa shaguna su kashe kudi mai yawa domin neman inganta fatarsu amma abin ba ya aiki. Don haka a yau na kawo muku hanyoyi masu […]

Amfanin ’ya’yan itatuwa hudu a jiki

Amfanin ’ya’yan itatuwa huxu a jiki

A yau na kawo muku yadda ake amfani da ’ya’yan itatuwa hudu; lemu da kankana da mangwaro da kuma abarba, domin inganta fata da kuma haskaka ta. Mata da dama na zuwa shaguna su kashe kudi mai yawa domin neman inganta fatarsu amma abin ba ya aiki. Don haka a yau na kawo muku hanyoyi masu sauki da za a bi domin ingantawa da haskaka fatar jiki.

• Lemu na dauke da sinadarin bitamin C don haka yana kare fuska daga fesowar kuraje da kuma haskakata. A samu lemun zaki mai ruwa sai a matse ruwan. Bayan haka, sai a fasa kwai a dauki doruwan cikinta a zuba a cikin ruwan lemun. Sannan a dauko cokali a auna zuma cokali karami sai a zuba. Sannan a kwaba su sosai. Bayan haka, sai a shafa a fuska na tsawon minti 15 zuwa 20, sannan a wanke. Wannan hadin na haskaka fata sosai.

• Kankana na dauke da sinadaran gyara fata kuma tana hana ramukan gumi budewa domin idan ramukan gumi na nan a bude, datti zai shiga wanda zai haifar da fesowar kuraje. A samu kankana zalla a markada ta  sannan a shafa a fuska na tsawon minti 15 zuwa 20. Bayan haka, sai a wanke da ruwan sanyi. Yawan yin hakan na haskaka fata sosai kuma na rage fesowar kuraje a fuska.

• A bare mangwaro da wuka sannan a cire bawon da kwallon. Sannan sai a markada da zuma sai a kwaba su sosai. Daga nan sai a shafa a gashin kai a bari ya jima na tsawon awa daya. Sannan a wanke kan da man ‘shampoo.’ Wannan irin hadin na karfafa gashi kuma yana sanya shi tsayi da kuma laushi.

• Abarba na dauke da sinadaran da ke gyaran fata sosai. A markada abarba sannan a diga man zaitun. Sannan a shafa a fatar jiki. Bayan haka, sai a shafa a fatar jiki na tsawon minti 15 zuwa 20. Irin wannan hadin na warkar da kurajen fuska kuma da sanya fuska haske da sulbi da kuma kyalli.