Amina Aliyu: Yarinya mai rayuwa da man fetur
A garin Gandi cikin karamar hukumar Rabah da ke jihar Sakkwato akwai wata yarinya ‘yar shakara bakwai mai suna Amina Aliyu da ke rayuwarta ta hanyar shakar man fetur a kullum kuma ba ya bugar da ita, ba domin ta yi maye take shakarsa ba, hayar gudanar da rayuwarta ce da ta fi bukatarsa fiye […]

A garin Gandi cikin karamar hukumar Rabah da ke jihar Sakkwato akwai wata yarinya ‘yar shakara bakwai mai suna Amina Aliyu da ke rayuwarta ta hanyar shakar man fetur a kullum kuma ba ya bugar da ita, ba domin ta yi maye take shakarsa ba, hayar gudanar da rayuwarta ce da ta fi bukatarsa fiye da ruwa da abinci, wanda ya sanya iyayenta ba su da kwanciyar hankali sai sun tanadar da man fetur a cikin gorarta.
Aminiya ta tafi garin Gandi don ganin yadda yarinyar ke wannan rayuwa da kuma mataki ko wahalar da iyayen yarinyar ke dauka kan lamarin.
‘’Wannan lamarin na wannan yarinya yana ba mu mamaki don ba haka muka haife ta ba, a lokacin da take ‘yar shekara daya wani ciwon zazzabi ya same ta day a sanya take jin tsoro a yayin barcinta, aka nemi magani ta samu sauki, daga nan ne bayan wani dan lokaci idan ta zo shagona sai ta dauki man fetur ta shaka, idan na kwabeta sai ta ki ji, in buge ta ba zata bari ba, haka ta ci gaba, idan ma ta zo wajena babu sai ta je duk inda za ta samo shi a garin nan, kuma ba ta barci ko cin abinci matukar ba ta shaki fetur ba,’’ a cewar mahaifinta Malam Aliyu Bala.
Ya ci gaba da cewa, ‘mun sha kyale ta mu hana ta fetur din domin ko za ta ji yunwa ta ci abinci, amma ta ki, duk da wahalar da za ta sha, tsakanin da da mahaifa, dole mu ba ta man, haka muka yi ta shan wahala da ita har muka hakura muka dauki dawainiyar samo mata man da magani, don mun san ba aikin lafiya ba ne, duk da ba mu taba ganin ya cutar da lafiyarta ba, lafiyar jikin garau, kuma babu wani abu mai kama da maye (buguwa) a tattare da ita,’ in ji mahaifin nata.
Malam Aliyu, mai shekara 42 da ‘ya’ya tara, mata biyar maza hudu, ya kara da cewa, ‘A duk cikin ‘ya’yana babu wani mai yin wani abu da ya saba wa tafiyar rayuwar mutane, sai wannan yarinyar Amina, yanzu shekara shida tana shakar fetur ba dare ba rana, a kullum tana shanye fiye da lita daya ta man, matukar za ta same shi, mu kam ba mu ba ta, don halinmu ba zai iya biya mata bukatarta a kullum ba, mun nemi magani na gargajiya ba mu dace ba, duk da ba mu taba zuwa asibiti ba.’
Da wakilinmu ya tuntubi Dakta Larai Aliyu Tambuwal, wadda likita ce kwararra a fannin lafiyar mata a jihar Sakkwato, ta ce, ‘Wannan lamarin ban taba jinsa ba, a ce wata ba za ta iya zama ba sai ta shaki fetur kuma ba harkar maye ba, yakamata iyayen yarinyar su zo da ita asibiti don a auna ta a gane ko akwai wani abin ne a jikinta da ke bukatar sinadari irin wannan kafin ya yi rayuwa a jikinta, akwai bukatar yin bincike kan wannan yarinyar kafin girmanta, duk da ta dauki tsawon lokaci cikin wannan abin al’ajabi, waton shan Fetur,’ a cewar Dakta.