Amina: Fim din tarihin Sarauniya Amina ya tayar da kura

Fim din an shirya shi ne kacokan a kan Sarauniya Amina ta Zazzau.

Amina: Fim din tarihin Sarauniya Amina ya tayar da kura

Fostar fim din Amina

Fim din Aminiya, shiri ne da aka yi da Ingilishi, wanda Okechukwu Ogunjiofor ya shirya, sannan Izu Okukwa ya bayar da umarni.

A fim din, jarumar Kudu, Lucy Ameh ce ta fito a matsayin Sarauniya Amina, sannan akwai jarumai ’yan Arewa a ciki, irin su Ali Nuhu da Magaji Mijinyawa da Asabe Madaki da Yakubu Muhammad da sauransu.

Aminiya ta kalli tallar fim din, inda aka nuna Sarauniya Aminiya tana karama, inda ta fuskanci mahaifinta take ce masa tana so ta zama soja kamar sauran mayakan mahaifin nata.

Sai dai wani bafade (Magaji Mijinyawa) ya so ya kawo mata tsaiko, inda ya fada wa mahaifinta cewa ba a taba samu ba a tarihi inda mace ta shiga cikin mayakan Zazzau, inda nan take mahaifin ya ce masa yana so ya gwada a kanta ya ga yadda za ta kaya.

Fim din an shirya shi ne kacokan a kan Sarauniya Amina, wadda tarihi ya nuna ta yi rayuwa a Karni na 16.

Sai dai fim din, duk da cewa wadansu mutane musamman na Kudu sun ji dadinsa, kuma wadansu masu ruwa-da-tsaki a harkar fim a Najeriya na farin ciki kasancewar an nuna fim din a Mahanjar Netflix ce, wadda kusan duniya ce za ta gani, wadansu kuma musamman ’yan Arewa sun nuna rashin jin dadinsu a kan abin da suke cewa an jirkirta tarihin.

Dokta Furera Bagel, malama ce a Jami’ar Jihar Bauchi, ta ce an yi kokari amma akwai kurakurai. A cewarta, “Na samu damar kallon fim din nan da aka dade ana tsimaya wato Amina a Manhajar Netflix.

Zan iya cewa daraktocin sun yi kokarin fito da jarumtar Sarauniya Amina.

Da farko na ji tsoron ba zai iya yin abin da ya dace musamman lokacin da na ga an rubuta cewa, “A lokacin da ake danne hakkin mata,”

Haba! Muna maganar mace ta jagoranci maza a filin daga, wa yake maganar danne hakki?

Haka kuma Dokta Bagel ta kara da cewa akwai wasu kurakuran, kamar inda a cewarta Mukaddashin Sarkin Igala ya kira Madakin Zazzau da ‘Abokina daga Sahara,” inda ta ce ko Maiduguri ba Sahara ba ce ballantana Zazzau.

Ta kara da cewa Turawa ne suka kawo amfani da Sandar Mulki Zazzau, don haka a lokacin Amina babu wannan.

Sai dai ta yaba suturar da aka yi amfani da su da wajen daukar shirin da kwalliya, sannan ya nuna wakar da wani mai suna Kabarkai a fim din ya yi lokacin da ya bugu, inda ya rera wakar, “Rana, rana, bude, bude, in yanka maki rago baba ki sha jini shar-shar,” wanda a cewarta yana cikin dalilan da marigayi Danmasanin Kano ya bayar cewa Hausawa asalinsu daga Habasha suke kuma bautar rana suke yi a wata lacca da ya gabatar a Ranar Hausa ta 1975 a Jami’ar Bayero da ke Kano.

A karshe sai ta ce, “Ina fata Kannywood ta gwada ko da kwatankwacin wannan.”

A kasan rubutunta, Ibrahim Sheme ya yi martani, inda ya yaba mata, sai shi kuma Farfesa Audee T. Giwa ya ce, “To ai ka gama sharhi. Yaya zan kalli fim din?,”, sai Sheme ya ce masa, “ Ba ni na yi ba, ga sunan mai sharhin nan a farkon rubutun. Idan za ka kalla sai ka yi rajista da Neflid. Babu wahala. Ka duba google.

Wani mai suna Ahmed Musa Husaini ya fadi a Facebook cewa, “Fim din Amina din nan da aka ta tallatawa kuma aka yi ta jira ya ban kunya. Tun daga daukar shirin da tsara labarin da kwalliyar duk ba su yi ba, sannan an bata tarihin Zazzau. Ko Kannywood za ta yi abin da ya fi wannan.”

Shi ma Fatuhu Mustapha da ya kalli shirin cewa ya yi, “A nawa tunanin, kuskuren da masu shirya fim din suka yi shi ne rashin gudanar da cikakken bincike a kan Masarautar Zazzau da Sarauniya Amina din,” sannan ya kara da cewa ya aminta da batun cewa gara mu fara bayar da labarinmu da kanmu ko kuma wadansu su bayar yadda suka so kuma babu abin da za mu yi.

Nasir Jajere cewa ya yi, “Na bata lokacina a banza ina kallon shirin. Kura-kurai da yawa a tarihin da kuskuren hada wasuabubuwa da ake gudanarwa kafin jaddada Muslunci da bayansa. Haka ma kona wadanda suka mutu bai da asali a Afirka, musamman ma a yi kamar na Indiya. Ban san yadda ’yan Kannywood suka ji ba da suke fitowa a fim din Nollywood da aka yi kura-kurai da dama game da mutanensu.”

Sai dai shi Al’amin Ciroma cewa ya yi a kasan rubutun Bagel, “Wannan sharhi ya yi. Kin tattaro dukkan muhimman abubuwa da shirin ya kunsa. Amma ina tunanin jaruman za su yi kokari sama da haka. Akwai wurare da dama da jaruman ba su nuna kwarewa ba.”

Sai Ibrahim Sheme ya sake wani rubutun, inda ya ce, “Wannan sharhin ya yi kyau, kuma kin yi adalci. Na tura wa Daraktan Shirin, Izu Ojukwu da wadansu daga cikin manyan jaruman shirin irin su Lucy Ameh. Haka kuma na jawo hankalin Ali Nuhu da Asabe Madaki da sauransu.”

Shi kuma Malam Yakubu Musa cewa ya yi cikin barkwanci, “Amina an bata asalin tarihi. Babu wani abin burgewa a shirin da ya nuna Amina ko al’adunta. Daga gani marubucin shirin nan masoyin Kungiyar Manchester United ne.”

Gaskiya akwai laifinmu – Furodusan Kannywood

Aminiya ta tuntubi furodusa a Masana’antar Kannywood, Alhaji Naziru Dan Hajiya domin amsar maganar da mutane suke yi cewa wannan fim ne da ya kamata a ce Kannywood ce ta shirya ba ’yan Kudu ba.

A cewarsa, “Lallai na samu labarin wadansu sun shirya fim din Amina kuma sun bata tarihi.”

Da aka tambaye shi ko akwai laifin masu ruwa-da-tsaki na Kannywood a lamarin, sai ya ce, “Gaskiya mu ne ba ma tsayawa mu jajirce wajen nemo babban labari irin wannan.