Amina Shamaki: Dalilan da suka sanya na zama likita

Dokta Amina Shamaki kwararriyar likita ce, kuma jami’ar harkokin mulki ce. A hirar da ta yi da Aminiya ta bayyana yadda ta taso tundaga kuruciya da karatunta da ayyukan da ta yi a tsakanin asibitoci da ma’aikatun gwamnati, har ma da wasu al’amura da suka shafi rayuwarta. Ga dai yadda hirar ta kasance: Daga Mulikat […]

Amina Shamaki: Dalilan da suka sanya na zama likita
Amina Shamaki: Dalilan da suka sanya na zama likita

Dokta Amina Shamaki kwararriyar likita ce, kuma jami’ar harkokin mulki ce. A hirar da ta yi da Aminiya ta bayyana yadda ta taso tundaga kuruciya da karatunta da ayyukan da ta yi a tsakanin asibitoci da ma’aikatun gwamnati, har ma da wasu al’amura da suka shafi rayuwarta. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Daga Mulikat Mukaila da Abubakar AbdurRahaman Dodo

Tarihin rayuwa
An haifi Amina Muhammadu Shamaki, a shekarar 1960, a garin Jega da ke Jihar Kebbi. Kuma ta fito ne daga zuri’ar Sarkin Kebbin Jega, Alhaji Muhammadu Dodo, wato wand aya fara rike Sarautar Bunu, kuma Hakimin Dumbego. Mahaifinta kuwa, shi ne Muhamamdu Bello Dumbego Dodo, wato shi ne babbban da a gidan, kuma ya kasance a Hakimi a garin Dumbego, kfin daga bisani ya zama Sarkin Kebbin Jega.
Dokta Amina ta fara karatunta ne a makarantar Firamare ta Turaki da ke Sakkwato, amma ta kammala karatun Maiyamma, inda ta zauna tare kakanta na wajen uwa. Ita kadai ta ci jarabawar shiga kwalejin Gwamnatin Tarayya a garinsu, don haka ta smau shiga Kwalejin Gwmanatin Tarayya ta Odogbolu, a Jihar Osun, inda ta kammala karatunta na Sakandare. Bayan ta kammala karatun share fagen Shiga Jami’a a Sakkwato, a tsakanin 1978 zuwa 1979, sai ta halarci Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a tsakanin shekarun 1979 zuwa 1984. Ta yi koyon aikin Likitanci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Sakkwato, inda daga bisani ta tafi hidimar kasa (NYSC) a Jihar Legas, inda ta yi a aiki a wani asibiti Global Clinic da ke karamar Hukumar Etiosa.
A shekarar 1990, ta yi babban digiri a fannin sarrafa rugugin sinadarai don warkar da cututtuka da daukar hoton sassan jiki (Radiology), a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas a shekarar 1995. Dokta Amina ta samu horo a Cibiyar kula da lafiyar iyali ta Bristol Royal and Family da ke kasar Birtaniya. Kuma daga bisani ta samu shaidar kwarewa ta kololuwa a harkar lafiya daga Kwalejin kwararrun Likitocin Fida ta Afirka ta Yamma.
Don kwadayinta na fadada iliminta, sai ta yi difuloma a fannin harkokin kasuwanci. Ta kuma yi digiri na biyu a wnanan fanni na nazarin harkokin kasuwanci, a tsakanin shekarun 2009 zuwa 2011. Amina ta halarci Cibiyar Bayar Nazarin Muhimman Bukatu na kasa da ke Kuru a Jos, baya ga dimbin kwasa-kwasan da ta yi. A halin yanzu Dokta Amina ita ce babbar sakatariya ayyuka na musamman a ofishin Shugaban Ma’aikata na kasa.
Ayyukan da ta yi
Bayan na kammala koyon aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Sakkwato, a shekarar 1984, na yi aiki na wasu shekaru a Hukumar Ma’aikata ta Tarayya, inda aka tura ni Ma’aikatar Tsaro a shekarar 1986. Na yi aiki da Cibiyar daukar Kula da Lafiyar Sojoji, inda aka tura ni Asibitin Sojoji na Creek da ke kan titin Awolowo, a Legas, inda na zama jami’ar Lafiya ta Mata a shekarar 1990. A lokacin da nike wancn aiki, sai Asibitin Gidan Shugaban kasa ya bukaci a turo ni, domin in bude Sashen Sarrafa Rugugin Sinadarai da daukar Hioton sassan Jiki (Radiology), a Legas da Abuja. Sannan a shekarar 1998, Asibitin kasa da ke Abuja ya bukaci kwararru, wadanda suka hada da masanan sarrafa rugugin sinadarai da daukar hoton sassan jiki, don bude asibitin, wanda uwar gidan Shugaban kasa Maryam Abacha ta gina, don kula da lafiyar mata da kannanan yara, na aiki a matsayin ma’aikaciyar aro a wannan asibiti har zuwa shekarar 2009, inda daga bisani a ka mayar da ni ma’aikatar lafiya ta tarayya. Da komawata sai aka dora mini alhakin kula da asibitocin koyarwa, a karkashin sashen kula da ayyukan asibitoci, tun daga shekarar 2009 zuwa 2010. Daga bisani na zama Shugabar Sashen Kyautata ayyuka da makarantun horar da kwararru.
A shekarar 2011, na halarci Cibiyar Nazarin Muhimman Bukatu da ke Jos, da na dawo sai aka nada ni Shugabar tsohuwar Hukumar Kula da Asibitocin Manyan Makarantun kasa, a matsayin mukamin riko. Sai kuma aka mayar da ni Shugabar Sashen Kula da aikace-aikacen asibitoci. Daga nan ne sai aka kara mini girma zuwa Babbar Sakatariya a ofishin a Hukumar daukar Ma’aikata ta Tarayya, cikin Oktobar 2014. A halin yanzu ina rike da mukamin babbar sakatariya, mai kula da ayyukan musamman a ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya.
Yadda na zabi zama likita
Dalilai da dama suka sanya na yi sha’war zama likita. Na farko dai wani al’amari mara dadi da aya auku ga mahaifiyata, inda ta sha wani magani day a yi mata illa, a lokacin muna hutun makarantar sakandare, hart a kai ga ya zama ajalinta.. A lokacin ina karama, na damu matuka wajen son in gano hakikanin abin da ya faru. Don haka na ce zan yi kokarin gano abin d aya faru, domin in bai wa sauran mutane kariya daga fadawa cikin irin wannan mummunar matsalar. Wannan shi ne daya daga cikin dalilan, don haka na yi karatun aikin likita. Sai dai kafin aukuwar wancan al’amari, lokacin d anike sakandare, tunanina y rabu biyu. Domin sha’awata na tsakanin zama injiyar sarrafa sinadarai ko likita, don haka a lokacin da nike cike takardar shiga babbar makaranta, sai na zabi kwasa-kwasai biyu. Ina cikin karatu, sai Allah ya hada ni da wani mai karatun aikin likita, sai ya karfafa mini gwiwa kan in yi wannan karatu, kuma da kamala karatun share fagen shiga jami’a sai aka ba ni kwas din koyon aikin likita. Don haka ina iya cewa, sha’awa da kwarin gwiwa da kaddara, tare da abin day a auku a rayuwata, suka zama sanadin zamana likita.
Yadda na ji rashin mahaifiyata
Mahaifiyata, mai suna Fatima Yarfarin Aliyu. Iyayena dai ‘’yan uwan juna ne. Na yi rashin kauna da kulawar mahaifiya. Domin soyayyar uwa ba za a iya auna kimarta ba, musamman a lokacin da mutum ke girma a tsakanin yarinta da rayuwar matasa, a daidai lokacin da ake bukatar shawarwarin a daukacin harkokin rayuwa. Mahaifina ya yi matukar kokarinsa, saboda haka ma muke kiransa ‘uwa da uba.’ Mahaifiyarmu ta mutu ta bar ’ya’ya mata biyar da namiji daya. Sai dai danta namiji ya rasu bayan mutuwarta da wasu ’yan shekaru. Mahaifinmu, wanda mutum ne mai son ilimi, sai da ya tabbatar daukacin ’ya’yans amata biyar duk sun yi karatun zamani, duk da kyarar da a ke nuna wa tsarin a zamantaekwar al’umma. Ya ba mu kwarin gwiwa, don haka muke godiya ga Allah.
Abin da nike matukar jin dadinsa a aiki
Ina matukar jin dadin aikin likita, saboda duk abin da za ka aikata, mutum yak an yi iya kokarinsa. Na kan yi iya kokarina wajen kula d amara lafiyar da ke karkashin kulawata. Sannan a aikin gudanar da harkokin mulki, nan ma akwai wnai abin sha’awa, sai dai akwai bukatar hadin kan mutane don cimma manufa. A hakiknain gaskiya na ji dadin aikin likita fiye da komai.
Abin dab a na mantawa
Ina tuna lokacin da mahaifina ke koyarwa, yakan dauke ni zuwa makaranta tun kafin in shiga. Wannan shi ne dalilin da ya snaya na shiga makaranta da wuri.
Sannan ina tuna yadda na ji dadin zama da kakata a Maiyamma. Mace mai tsauri wajen tarbiyya,, amma duk da haka ta san yadda take jan mutum a jika. A can rayuwar bat a makaranta kadai ba ce, domin har gona muke zuwa. Kuma mukan hadu da yawa mu tafi, saboda akwai jikoki da yawa a gidan. Sannan mun kai mu 20 da ke cin abincin a kwano guda. Wani abu da ba zan taba manta bawa, shi ne irin tarbiyyar mahaifina. Ya tafiyar da rayuwarmu ta yadda kusan daukacin yini akwai abin da muke yi. Don ba mu da lokacin wasa. Ya koyar da mu kur’ani da kansa. Da safe ya rika koyar da mu, ta yadda kowa sai ya karanta abin da ya koya. Wanda duk ya kasa biya karatunsa, to ba za a ba shi Karin kumallo ba. Wannan dai wata dabara ce ta sanya mutum ya jajirce kan duk abin da ya sa a gaba. Ga shi muna aiki da abin day a koyar da mu a aikace.

Abin da na koya a wurin mahaifina
Ina ganin horon tarbiyya na smau. Domin mutane ba su cika son a horar da su kan tafarkin ladabi da tarbiyya ba. Kai hatta ’ya’yana sukan ce ina da tsanani, saboda ba ni da sauki akan abin da ya shafi adalci. Kuma na damfaru da tunanin ganin an aikata abin da duk ya fi dacewa.
Yadda nike hutawa
Ina da sha’awar girki. Ina son karanta littattafai. Don haka na yi karatu a fannonin ilimi da dama. Na kuma gano cewa, nazarin halayyar al’umma ya fi komai ban sha’awa. Hidima ga al’umma tamkar magani ne, amma sanin dabi’un dan adam na da matukar alfanu, saboda suna bai wa mutum karin haske kan yadda zai yi hulda da mutane. A lokacin hutuna ina na fi son zuwa gida Jega, domin a can ina yin ayyuka da dama. Sannan ina smaun damar mu’amala da mutane. Don haka ba hutawa nike yi ba idan na je gida.
 A lokacin da na zama uwa
A lokacin haihuwata ta farko, ban ma san ina dauke da juna biyu ba, duk da cewa ni likita ce. daukar juna biyu na tattare da al’amuran ban mamaki. Ina da ’ya’ya uku, biyu mata, daya namiji, kuma cikin yardar Allah suna tafiyar da rayuwarsu a fannonin da suka dauka, ba tare da wata tangarda ba.
Hada aiki da kula da ’ya’ya
Dole ne in ce maigidana ya yi matukar taimaka mini. Yana matukar son in yi masa girki, don haka nike tashi da wuri in girka masa abinci. Da na yi sa’a, sai ya kasance lokacin da nike aiki a asibitin Creek muna tashi da karfe biyu da rabi na rana, sai kawai in tafi in dauko ’ya’yana daga makaranta, in koma gida in girka musu abinci; kusan kullum haka al’amarin ke kasancewa, sai dai in ana bukatar ganina a asibiti.. Kuma nakan kais u makarantar koyon karatun Alkur’ani. A lokacin da aka sauya wa mijina wurin aiki zuwa Fatakwal, sai na samu damar yin babban digiri, saboda haka a lokacin da ya dawo a shekarar 1995 na kamala karatuna. Gaskiyar lamari, abin babu sauki wajen kula da miji da ’ya’ya, ga aiki, sannan ga zuwa makaranta.
Yadda na hadu da maigidana
Na hadu da maigidana a shekarar 1978 a gidan su kawata da na kai mata ziyara. Shekarunmu daya da ita, amma ita ta riga ta yi aure. Dan a ziyarce ta sai abokin mijinta ya rage mini hanya zuw amakaranta, amma a lokacin bai ce da ni komai ba. Sai kawai ya koma gidan abokinsa ya byyana masa cewa yana son ya aure ni. Cikin kaddarar Allah sai ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello ya yi karatun digirinsa, a daidai lokacin da nike karatun aikin likita. Duk da haka babu wani abu day a wakana a tsakaninmu har sia da na kammala karatuna.
Abin da nike son a tuna da ni
Ina son kyautata rayuwar mutane, ta yadda zan bar abin koyi ga na baya. Don haka nike ganin Allah Ya halicci mutane ne don su kula da rayuwar junansu.  A wasu lokuta ina jan hankalin likitoci abokan aikina kan cewa, aikinmu dam ace ta kula da dan adam.