Amincewa a ciwo bashi da Majalisa ta yi

Editan Aminiya, ka ba ni dama a yau in yi tsokaci a kan amincewa da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wa Shugaba Buhari a kokarinsa na ciyo wa Najeriya bashin kudi daga kasashen waje, domin cike gibin kasafin kudin wannan shekara ta 2017 da ke shirin karewa.  Hakika mun yarda cewa Shugaba Buhari yana da […]

Amincewa a ciwo bashi da Majalisa ta yi

Editan Aminiya, ka ba ni dama a yau in yi tsokaci a kan amincewa da Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wa Shugaba Buhari a kokarinsa na ciyo wa Najeriya bashin kudi daga kasashen waje, domin cike gibin kasafin kudin wannan shekara ta 2017 da ke shirin karewa. 

Hakika mun yarda cewa Shugaba Buhari yana da kyakykyawar niya ga al’ummar Najeriya, kuma mun yarda ba zai aminta da duk abin da yake ganin zai iya cutarwa ko kawo wa kasar cikas ga cigabanta ba, amma abin tambaya anan, wai me ya sa gwamnatocinmu suke kokari wajen ciwo wa kasarmu bashi? 

Sannan me ya sa ba sa tunanin biyan basussukan da ake bin kasarmu da gwamnatocin baya suka ciwo mata? 

Ko kuna tunanin duk kasar da ake binta bashi za ta iya samun cigaban da ake bukata acikin wannan hali? Sannan su yan majalisa me ya sa ba sa amincewa da kudurorin da shugaban kasa ya gabatar musu, wadanda ake ganin za su amfani ’yan Najeriya sai abin da zai amfanesu kawai? Don haka ba mu goyan ciwo wa kasarmu bashi a wannan hali. 

Daga Shugaban kungiyar Muryar Talaka na karamar hHukumar Mani a Jihar Katsina, Aabdulsalam Lema Tsagem: 08038792668: Abdulsalam Mohammed <[email protected]>