Amincewa da sakamakon zabe ne zai kawar da rikici -Sheikh Gumi

Ranar Litinin din da ta wuce ne Babban Malamin Addinin Musulunci Shaikh Ahmad Gumi ya roki ’yan Najeriya da su amince da sakamakon zaben 2015, domin kauce wa tashin hankali da kashe-kashe.Shaikh Gumi ya yi kiran ne a lokacin da yake jawabi ga ’yan kabilar Igbo na Ohanaize da suka kai masa ziyara gidansa da […]

Amincewa da sakamakon zabe ne zai kawar da rikici -Sheikh Gumi
Amincewa da sakamakon zabe ne zai kawar da rikici -Sheikh Gumi

Ranar Litinin din da ta wuce ne Babban Malamin Addinin Musulunci Shaikh Ahmad Gumi ya roki ’yan Najeriya da su amince da sakamakon zaben 2015, domin kauce wa tashin hankali da kashe-kashe.
Shaikh Gumi ya yi kiran ne a lokacin da yake jawabi ga ’yan kabilar Igbo na Ohanaize da suka kai masa ziyara gidansa da ke Kaduna.
Ya ce tun yanzu ya kamata jama’a su fara shirin amincewa da sakamakon wannan zabe.
Gumi ya ce dole ne ’yan Najeria su yi kokarin kauce wa duk wani abu da zai kawo yaki da tashin hankali a kasar nan.
“ Dole ne mu kauce wa abin da zai janyo bala’i a kasar nan. Akwai bukatar mu amince da sakamakon zaben. Mu yi hakuri da sakamakon zaben, domin gwara mu yi hakurin shekaru hudu da mu wahala na shekara 40,” inji shi.
Shaikh Ahmad Gumi ya dan nuna shakkunsa ga Hukumar Zabe, inda yake ganin kamar ba ta shirya gudanar da zaben ba.
“ ’Yan Najeriya na bukatar sababbin shugabannin da za su shugabanci kasar nan. Domin a yanzu kusan dukkan  ’yan takarar da aka tsayar mutane ne da suka taba rike mukamin a lokaci daban-daban,” inji shi.
Ya kuma nuna alhininsa akan yadda cin hanji da rashawa yi wa kasar nan katutu, har ya kawo cikas ga ci gaban kasar. Ya ce abu ne mai wuyar gaske a ce an kawar da cin hanci a aikin gwamnati a cikin dan kankanin lokaci.
“ Babu wanda zai iya kawar da da cin hanci da rashawa duk yaudara ce,” inji shi.
A game da rashin iya kawar da da ’yan Boko Haram da sojojin kasar nan suka yi, shahararren Malamin ya ce hakan ya faru ne saboda nuna halin ko in kula da gwamnati ta yi wajen inganta sojojin.
Ya bayyana ayyukan ’yan kungiyar a matsayin wadanda suka saba wa addinin Musulunci, inda ya ce Allah zai hukunta su.
A jawabinsa, shugaban kungiyar ‘’Yan kabilar Ibo, Barista Austin Chenemeze ya ce sun ziyarci malamin ne domin kara karfafa zumunci da kuma fahimta a tsakanin Musulmi da Kiristocin kasar nan.  Ya kuma ce kungiyarsu na matukar tsoron abin da zai faru a zaben shekarar 2015.
A cewarsa, yanzu babu ciniki a kasuwanni saboda jama’a na boye kudi domin gudun abin da zai faru a zaben 2015, wanda ya ce hakan na matukar damun jama’arsu, musamman mazauna yankin Arewacin kasar nan.
Don haka sai ya roki malamin da ya taimaka wajen jan hankalin jama’a da su kauce wa rikici domin babu abin da yake haifarwa sai barna.