Amincewa da ’yancin kananan hukumomi da shugabanin majalisu suka yi
Takaddamar da ake yi game da ’yancin cin gashin kai ga kananan Hukumomin Najeriya ya samu tagomashi a yayin da taron da Shugabannin Majalisun Dokokin jihohi suka amince tare da nuna goyan bayansu ga sakar wa kananan hukumomin mara. A yayin taron da shugabannin kananan hukumomin suka gudanar makonni biyu da suka gabata a Yola, […]
Takaddamar da ake yi game da ’yancin cin gashin kai ga kananan Hukumomin Najeriya ya samu tagomashi a yayin da taron da Shugabannin Majalisun Dokokin jihohi suka amince tare da nuna goyan bayansu ga sakar wa kananan hukumomin mara.
A yayin taron da shugabannin kananan hukumomin suka gudanar makonni biyu da suka gabata a Yola, sun bayyana kananan hukumomin a matsayin ginshikin samar da cigaban al’umma a matakin farko, sannan suka tabbatar da bukatuwar da ake da ita wajen sakar masu mara a sha’anin siyasar kasar, bayan doguwar tuntuba daga sassan kasar baki daya.
Shugaban zauren shugabannin majalisun jihohin, kuma shugaban majalisar dokoki na Jihar Kebbi, Hon. Isma’il Abdulmumini Kamba, ya bayyana cewa, manufar taron ita ce kade dattin dake kan ’yancin kason kananan hukumomin wanda kundin tsarin mulki ya yarda da shi, da kuma neman ra’ayin jama’a game da yadda za a samu haduwar muryoyin al’ummomin da abin ya shafa kai tsaye. Haka kuma taron ya nemi majalisun da zama mambobin tafiyar da sha’anin wadda kuma a taron na Yola dukkan shugabannin majalisun sun samu halarta.
A yayin da muke kokari wajen samar da sahihin cigaba a Najeriya ta fuskar dimokuradiyya, ba kawai mun gamsu da matakin da shugabannin majalisun suka dauka ba ne, tuni matsayar tasu ta ma kai gaya wajen la’akari da cewa kundin tsarin mulkin kansa ya baiwa majalisun nasu dukkan hurumin yin dokar da za ta kyautata jin dadin jama’a a kananan hukumomin kasar nan baki daya. Don haka ya kamata su dandana gardin ikon da kundin mulkin ya ba su wajen yi wa tufkar hanci. Sannan kuma su kara yin la’akari da irin rauni da kuma rudanin da kananan hukumomin suka fada.
A yayin nuna goyan bayan shugabannin majalisun game da kason kananan hukumomin, ya kamata shugabannin su nemi cikakken amincewar al’ummar kasar nan wadanda suke ganin hadarin ci gaba da kasancewar kananan hukumomin a karkashin wannan rudanin na rashin ‘yancin. Domin kundin tsarin mulki ya fayyace karara cewa kananan hukumomi zababbu ne kuma suna da ’yancin cin gashin kansu, amma sai aiwatar da hakan ya yi hannun riga da tsarin mulkin.
A sarari yake cewa fiye da kashi 85 cikin 100 na kananan hukumomi 774 na Najeriya ana gudanar da su ne a bisa tsarin rikon kwarya, wadanda gwamnonin jihohi ke nadawa don samun damar cimma wasu bukatunsu. Ba wannan ba ma, abu ne sananne cewa mafi yawan kananan hukumomin ba su da zababbun shugabanni tsawon shekaru. Sannan ita kuma Gwamnatin Tarayya ta yi biris da batun, inda ta ke cigaba da saba wa kundin tsarin mulkin ta hanya tura kudaden kason ga shugabannin kananan hukumomi wadanda ba zababbu ba.
Wani daga cikin manyan turakun dake cigaba da kawo cikas ga kason kananan hukumomin ma shi ne yadda ake kirkiro wani asusun hadin gwiwa na jiha da kananan hukumomi, inda gwamnoni ke sarrafa kudaden a tsarin kashin dankali bisa son zuciya. Wannan lamarin kuma na haddasa gagarumin tarnaki wajen hana kananan hukumomin aiwatar da ayyukan cigaba a yankunansu. Wannan kuma shi ne gimshikin tauye hurumin daya daga cikin bangarorin gwamnati uku da ake da su.
Don haka wannan habbosa na shugabannin majalun jihohi ya zama tamkar farkarwa ga dukkan masu kishin kasa da sauran ma su ruwa da tsaki a farfajiyar dimokuradiyyar kasar nan, sannan a rashin cika wannan buri, abu ne mai wahalar gaske kasar nan ta iya kaiwa ga romon dimokuradiyya. Saboda haka wajibi ne ga dukkan bangarori su bada gudumar da ta kamata su bayar. Babu raba daya biyu, wannan yunkuri na shugabannin majalisun na bukatar karin wayar da kan jama’a don kaiwa ga gaci, domin ba za ayi zaton samun nasara cikin sauki ba kasancewar abu ne da zai ci karo da muradun mafi yawan gwamnonin kasar nan.
Hakazalika akwai bukatar Majalisun Tarayya su shiga lamarin wajen karfafa gwiwar majalisun jihohin don ingiza kudurin ‘yancin kananan hukumomin cikin sauri tare da rabbata shi. A bisa himmar tabbatar da wannan manufa, dole dukkan jam’iyyun siyasa su sanya hannu tare da bada cikakken goyan baya wajen kawo karshen tauye hakki da kuma mika kudaden kason ga wadanda ba zababbu ba.