Amincinmu da Sarkin Daura ya sa Shata ya yi mini waka – Sultan na Damagaram
“Ku kau Duwan ku dan mani hanya, In je wajen dan Umaru Sarki.”Amshi: Abubakar dan Ummaru Sarki, “Mai birnin Zandar har daji, Abubakar dan Ummaru Sarki”Amshi: Abubakar dan Ummaru Sarki, Mai horo mutumen Mai Daura zaki, Abubakar dan Ummaru Sarki”Amshi: Abubakar dan Ummaru Sarki, Sultan na Damagaram, Alhaji Aboubakar Umaru Sanda na daya daga cikin […]

“Ku kau Duwan ku dan mani hanya,
In je wajen dan Umaru Sarki.”
Amshi: Abubakar dan Ummaru Sarki,
“Mai birnin Zandar har daji,
Abubakar dan Ummaru Sarki”
Amshi: Abubakar dan Ummaru Sarki,
Mai horo mutumen Mai Daura zaki,
Abubakar dan Ummaru Sarki”
Amshi: Abubakar dan Ummaru Sarki,
Sultan na Damagaram, Alhaji Aboubakar Umaru Sanda na daya daga cikin manyan Sarakunan Musulunci masu wukar yanka a Jamhuriyar Nijar. Tun kafin zuwar Turawan mulkin mallaka kasar Faransa ake kiran sarautar ta Damagaram da sunan Sultan har zuwa yau. Sarki Aboubakar Umaru Sanda wanda ya hau karagar sarautar Damagaram a 1978 bayan mutuwar mahaifinsa ya shaida wa wakilin Aminiya a Damagaram irin yadda ya hadu da Shata har ya yi waka:
Aminiya: Allah Ya ja zamanin Mai martaba. Yaya aka yi kuka hadu da Mamman Shata har ya yi maka waka?
Sultan Aboubakar: A’uzubillahi minashshaidanir rajim. Bismillahir Rahmanir Rahim. Akwai dalilai da suka hada ni da Dokta Alhaji Mamman Shata, har ya yi mini waka. Na farko shi ne, amincinmu da Daura da amincinmu da marigayi Mamman Bashar Sarkin Daura. Kowa ya san Shata ya san shi da Sarkin Daura Alhaji Muhammad Bashar. To saboda haka sai in ce maka ko hutu Sarkin Daura yake so ya yi yakan zo nan wajena ya huta, ya yi mako ya koma gida ya ci gaba da aiki. To haka, mukan zauna da ni da Sarki tare da shi Shata a yi hira a nan masaukin baki da ke nan fada. Ni da kaina nake tashi in je can a yi hira. Shata ya zo mu zauna da shi a yi hirar. Hirar komai ana yi da shi. To dalilin wannan sai shakuwa ta shiga tsakaninmu da shi. Sai ya kasance duk abin da ya taso nan Damagaram a Nijar, Alhaji Muhammadu Bashar yakan taso ya zo ya wakilci Najeriya, yakan zo ya wakilci Jihar Katsina domin aminci da makwabtaka da kara dankon zumunci tsakanin Katsina da Damagaram da kuma Nijar da Najeriya. Saboda haka, shakuwar nan da muka yi da Shata sai ya zamo Shugaban kasar Nijar marigayi Seini Kountchie (Saini Kunche), zai zo nan Damagaram ziyara. Sai aka gayyaci Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar sai suka zo tare da Shata. Da ya zo, kamar yadda muka saba, aka tarbe su aka kai su masauki. To lokacin nan cikin hidimomin da ake yi har aka zo lokacin da aka ba Shata fage don ya yi wasa a wajen dinar da aka shirya wa Shugaban kasa. To! Jama’ar da ke nan farko sai suka nemi Shata ya yi musu wakar Shehun Borno, na biyu ya yi musu ta Sarkin Daura Muhammadu Bashar, karshe kafin su tambaye shi, sai ya ce, zai yi musu wakata. To a nan ne ya yi wakata kuma a wakar da ya yi ina tunani cewa irin bayanai da kalaman da ya fadi a ciki, yana ambatar iyayenmu da kakanninmu da wadanda suka kafa masarautar nan. Wannan abu ya shiga cikin kwakwalwarmu, kuma bayan wannan, yana kara jaddada amincinmu da shi Sarkin Daura, kuma ya nuna ba tun yau ba ne tun lokacin tsofoffi na baya ake cikin amincin nan har zuwa yau. Ka ji dalilan da suka sa Shata ya yi waka. Bayan wannan, akwai bikin Sallah da ake yi a nan a ranar 18 ga Disamban kowace shekara wadda ake zabar jiha guda a yi bikin a cikinta. To sai ta zo a kan Damagaram. Lokacin da za a tarbo su sai ya kasance ba ni nan, na je kasashen waje sai ana kamar gobe ne za a yi muka dawo. To a waka shi ne Shata yake cewa, da an fada masa tarbona ya je ya tarbo ni a cikin hikima ta mawaki. Ka san akwai soyayyar masoyin da take shafar wani masoyin. Shata mutum ne mushakkar. Mukan yi wasa da shi na yana Bafillace ina Babarbare.
Aminiya: Me za ka iya tunawa a kan kalmomin wakar tasa?
Sultan Aboubakar: To kalmomin wakarsa ka ji can na yi maka zancen batun tarbo ni da ya yi a cikin hikimarsa ta waka, wannan abu ya shiga cikin kai. Kuma yakan kawo maganar amincinmu da Sarkin Daura, yau da babu su nakan tuna da wannan, kuma yakan kawo alakar Nijar da Najeriya ta nuna addini da al’adunmu duk daya ne, muna tamkar Hasan ne da Husaini. Duk lokacin da na tuna su (Sarkin Daura Bashar da shi Shata) nakan yi addu’ar Allah Ya yi musu rahama.
Aminiya: Wace shekara ce Shata ya yi maka wakar?
Sultan Aboubakar: Wakar da ya yi mini ta farko ya yi ta a 1985, ya kuma yi a 1986 da sauran lokuta da ba zan iya tunawa ba.
Aminiya: Ke nan ba waka daya ya yi maka ba?
Sultan Aboubakar: Ba daya ba ce, akwai su da dama, na da din ma da ya yi ya maimaita su kuma ya kara inganta su.
Aminiya: Allah Ya ba ka nasara ba ka yi mamakin Shata da ya kawo wakar kalangu a fada ba?
Sultan Aboubakar: To abin da zai hana ni mamaki shi ne, mu ma a nan akwai makadin da yake da kalangu, wato Alhaji Ma’azu dan- Alalo, shi ma tsohon mawaki ne, ka san da shi wanda kuma tushensa mutumin Katsina ne. Ya zo nan tun yana da auren fari wajen 1940 da wani abu, har yanzu kuma zuri’arsa na nan, kuma da su ake komai a fada. Akan haka kalangu a masarautar Damagaram ba bakon abu ba ne. Kuma kowa ya san duk inda fada take tana tare da makada da mawaka iri-iri.
Aminiya: To me kuke gani ya bambanta Shata da sauran mawaka?
Sultan Aboubakar: To gaskiya ka san ko a cikin wakarsa yana cewa, har yanzu ba a samo canjinsa ba. Ka san a cikin mutane Allah Yana fifita wani Ya ba shi hikimar da wani ba ya da ita. To ko itace ne Shata ya duba ya yi masa waka, za ta yi dadi za a kuma fahimci abin da ya ce. Wannan ba karamar kyauta ba ce Allah Ya yi masa kuma a kan sana’arsa. Kuma da aka ba shi Dokta, lallai in ka dauki wakar Shata ka bi ta kana so kana iya yin littafi guda. In ka dauki wakarsa kana samun wata hikimar da kai ba ka da ita. A kan haka za ka ga masu neman ilimi ko a jami’o’i a kan dauki wasu kalmomi na Shata a sa a cikin koyar da harshe da ake yi. Shata ba shirya waka yake yi ba, da ya fara Allah zai sa masa a cikin kai zuwa harshe har ya fitar da abin da kai ba ka tsammani.
Aminiya: Ke nan ya taimaka wajen habaka harshen Hausa?
Sultan Aboubakar: Ba karamin taimako ya yi ba. In ka duba duk wadanda ke karanta littattafan Hausa ya ga akwai alamomi da kalaman Shata a cikin harshen da ake koyarwa.
Aminiya: Marokinsa na cewa” “Ruwan dare ne gama duniya” shin ya tabbata hakan?
Sultan Aboubakar: Wannan ma ya wuce haka, domin in ka dauki kasashenmu na Hausa wadannan ba a ma maganarsu domin ya gama da su, kai ka tafi har Amurka, yau ka je jami’a a Amurka za ka samu wani abu wanda yake daga Shata ya fito. Ka gani ai ya game duniya ke nan. karshe dai ai Amurka ko?
Aminiya: Allah Ya ba ka nasara yaya kuke kallon wake-waken yanzu idan aka kwatanta su da irin na su Shata?
Sultan Aboubakar: To, bambancinsu yana da yawa. Wake-waken yanzu akwai wasu kalmomi da suke shan bamban, akwai wasu abubuwan da za ka ga makadin yanzu ya yi su ba a cikin ladabi ba. Su kuwa irin su Shata sukan yi abu a cikin ladabi wanda kai da ake ma ko da wakar ce zai zamanto soyayya ta shiga tsakaninku. Saboda sun san yadda za su zo wajen babba, sun san yadda za su gaishe da babba, sun san yadda za su fadi kalamu a wajen babba wanda zai masa dadi ya yi na’am da su. Ka ga ba daya ba ne da wanda zai zo a tsaitsaye askin doki duk da a kan samu jefi-jefi amma wani abin yana rage musu ba kamar irin na su Shata ba.