Aminiya ta kaddamar da sabon tambarinta

Mun sauya taku da salo wajen gudanar da aikin jarida ta hanyar tsage gaskiya da kuma tafiya daidadai da zamani.

Aminiya ta kaddamar da sabon tambarinta

Sabon Tambarin Aminiya

Kafar Yada Labarai ta Aminiya ta kaddamar da sabon tambarinta domin tafiya daidai da zamani da kuma biya bukatun abokan huldarmu.

Kaddamar da sabon tambarinsu yana daga cikin sabon yunkurin Aminiya da Daily Trust da sauran dangoginsu da kamfanin Media Trust ke wallafa na sauya salo da fasali da kama wajen gudanar da sahihin aikin jarida cikin kwarewa,  daidai da zamani.

Sabon tambarin ya fara aiki ne a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, 2022 tamkar wani sabon shafi ne da ke alamta irin sabbin abubuwa masu kayatarwa da masu bibiyarmu za su fara gami daga wannan rana.

Hakan kuma ya zo daidai da shirin kamfanin Media Trust masu Aminiya da Daily Trust da dangoginsu na ci gaba da kare manufofinsu da suka gini a kan amana da nagarta da kuma jajircewa wajen tsage gaskiya.

Za kuma mu yi hakan ne ta hanyar amfani da dabaru da kuma fasaha da sauran kirkire-kirkiren zamani gami da fadada hanyoyin biyan bukatun masu bibiyar mu.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe