Aminu Ado Bayero ya daga tuta a Fadar Nassarawa

Ita tutar alamar iko ce kuma tana nuna cewa sarki yana cikin fada.

Aminu Ado Bayero ya daga tuta a Fadar Nassarawa

An daga tuta a Fadar Nassarawa ranar Alhamis

Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya daga tutar mulki a karamar fadar da ke unguwar Nassarawa inda yake zaune.

A bisa al’ada, tutar na zama ne a matsayin alamar iko, kuma daga ta na alamta cewa sarki yana cikin fada.

Wannan kuwa na zuwa ne duk da umarnin gwamnatin Kano ga Sarki Aminu ya fice daga fadar a yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano.

Akan daga tutar ce da misalin karfe 6 na safe a kuma sauke ta 6 na yamma ko idan sarki ya yi bulaguron aiki.

Aminiya ta gano cewa ba a daga tutar ba a Fadar Nassarawa ba sai a safiyar Alhamis, duk da cewa an sanya karfenta a safiyar Laraba.

An yi ta ji-ta-ji-ta ranar Laraba cewa an sanya tutar, amma Aminiya ta gano cewa karfen kawai aka sa, Alhamis da safe kuma aka daga tutar.

Daga tutar a karamar Fadar Nassarawa na zuwa ne a yayin da ake ci gaba da shari’ar da Gwamnatin Kano ke neman kotu ta hana Aminu Ado Bayero Aminu gabatar da kansa a matsayin Sarkin Kano bayan ta maye gurbinsa sa Muhammadu Sanuni II, Sarkin Kano na 16.

Gwamnatin jihar ta je kotu ne tana neman a hana duk sarakuna biyar da ta rushe masarautunsu a jihar gabatar da kansu a matsayin sarakunan masarautun.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos