Aminu Ado Bayero ya zama sabon Sarkin Kano

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da cewa, gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin, jim kadan bayan tube Sarki Sanusi II, ta nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano. Kafin nadin nasa shi ne sarkin sabuwar masarautar Bichi, kuma daya daga cikin hudu na sabbin Masarautu da Gwamna Ganduje […]

Aminu Ado Bayero ya zama sabon Sarkin Kano

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da cewa, gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin, jim kadan bayan tube Sarki Sanusi II, ta nada Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano.

Kafin nadin nasa shi ne sarkin sabuwar masarautar Bichi, kuma daya daga cikin hudu na sabbin Masarautu da Gwamna Ganduje ya kirkira a shekarar 2019.

Aminu Ado Bayero wanda da ne ga marigayi Sarki Ado Bayero, hakan yasa ya zama sarki na 15 a jerin Sarakunan Fulani na Kano.