Aminu Dantata ya ba mutanen Maiduguri tallafin N1.5bn

Dantata ya ja hankalin shugabanni da su kasance masu tsoron Allah a duk al’amuransu domin akwai ranar hisabi

Aminu Dantata ya ba mutanen Maiduguri tallafin N1.5bn

Babban attajirin Jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata, ya ba da tallafin Naira biliyan 1.5 a matsayin gudummawarsa ga mutanen da ambaliya ta shafa a Maiduguri, Jihar Borno.

Dantata ya ba da gudummawarsa ne a safiyar Talata, lokacin da ya jagoranci wata tawaga daga Jihar Kano domin ziyarar jaje a Gidan Gwamnatin Jihar Borno, sakamakon ambaliyar.

Aminu Ɗantata wanda hamshakin dan kasuwa ne, a ya jajanta musamman ga wadanda suka rasa makusantansu a ambliyar.

Dattijon mai shekaru 96, ya roki Allah ya kawo dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin Jihar Borno da ma Najeriya.

Sai dai ya koka bisa yadda ake fama da matsin rayuwa da tabarbarwar tattalin arziki a Najeriya.

Daga nan sai ya ja hankalin shugabanni da su kasance masu tsoron Allah a duk al’amuransu domin akwai ranar hisabi.

Da yake nasa jawabin, Gwamna Babagana Zulum, ya yaba wa Alhaji Aminu Dantata, wanda yawan shekaru ba su sa shi kasa a gwiwa wajen tasowa takanas domin yin jaje da kuma tallafa wa mutane jihar da ibtil’in ya shafa ba.

“Muna godi baba, Allah saka da alheri. Sannan ina sanar da ku cewa babanmu ya ba wa mutanen da ambaliya ta shafa tallafin Niara biliyan 1.5,” in ji gwamnan Zulum.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa