Aminu Kano da Janar Buhari: Samma kal-kal
Masu hikima suna cewa idan mutuwa na da wani magani, to bai wuce ayyukan kirki da na alheri wanda mutum ya yi a rayuwarsa ba, wadanda za su kasance masa sadakatul-jariyah, ko kuma wadanda za su amfani daukacin al’umman kasarsa. Hakika rayuwar Malam Aminu Kano ta burge kowa dangane da halayyarsa na gaskiya, da rikon […]
Masu hikima suna cewa idan mutuwa na da wani magani, to bai wuce ayyukan kirki da na alheri wanda mutum ya yi a rayuwarsa ba, wadanda za su kasance masa sadakatul-jariyah, ko kuma wadanda za su amfani daukacin al’umman kasarsa. Hakika rayuwar Malam Aminu Kano ta burge kowa dangane da halayyarsa na gaskiya, da rikon amana, da gudun abin duniya, da kawar da kai daga kazantar cikinta. Shi ya sa a kowace shekara akan tuna da marigayi Malam Aminu Kano, a ranar 17 ga wata Afrilu, watau ranar da ya koma ga Mahaliccinsa, a shekarar 1983.
A fafitikarsa na wayar da kawunan jama’a, ta yadda za su yi rayuwa mai ban sha’awa, Malam Aminu ya sha horon magoya bayansa da su kasance masu halaye nagari da aikata ayyukan kwarai, wadanda wasu za su rubuta don amfanin na baya, ko kuma su daddage don rubuta wani abin da na bayan za su kamanta. A ko da yaushe malam Aminu yana mayar da hankali ne ga harkokin da suka jibanci mata da matasa da kuma karfafa masu gwiwa yadda za su samu sukunin bayar da tasu ‘yar gudumowar wajen gina kasa.
A ‘yan shekarun baya, mata a nan jihohin Arewa, ba su da ‘yancin tsayawa zabe ko kuma fita don zaben wanda ya tsaya, sai lokacin da aka zo jamhuriya ta biyu ne suka samu wannan damar, kuma hakan ya biyo bayan dagewar da malam Aminu Kano ya yi don a kai ga haka. To amma ba ga jajircewa don ganin mata sun samu ’yancinsu kadai malam Aminu ya tsaya ba. Tun tasowarsa ya tsani zalunci da rashin adalci da jahilci da lalaci. Dalili ke nan da shi da jam’iyyarsa ta NEPU Sawaba suka mayar da hankali wajen sukar tsarin da Turawa suka fito da shi na amfani da sarakuna wajen takura wa talakawa don samun sauki a salonsu na mulkin-mallaka.
A wancan lokaci, kafin a kai ga samun ‘yancin kasar nan, jam’iyyar NEPU Sawaba ce a kan gaba wajen hankoron kawo gyara a harkar mulkin sarakuna, wadanda Turawan suka bai wa ikon da ya mayar da su ababen tsoro ga talakawa domin kasancewarsu manyan alkalai masu wukar yanka, masu nada sauran alkalai da gidan yarin da yake daure jama’a. Su ne suke da ‘yan doka, kuma shugabannin kanannan hukunomin da suke aiwatar da ayyukan inganta rayuwar talakawa, watau en’e-en’e.
Sanin kowa ne a wancan lokacin sarakuna sun yi amfani da wannan damar don kuntata wa talakawa, a sakamakon haka ne kuma gwamnatin mulkin soja ta farko a Nijeriya, ta Janar Ironsi, ta dauki matakan share wa talakawa, musamman ’ya’yan jam’iyyar NEPU, hawayen kukan da suke yi game da muzgunawar sarakuna. A watan Mayun shekarar 1966 ne aka karbe ‘yan doka da gidajen yari daga hannun sarakuna, aka mayar da su kurkashin gwamnatin tarayya, aka kuma yi gyara a harkar kotuna ta yadda sarakuna ba su da iko a kan alkalai, aka kuma kawar da ikon sarakunan na yin shari’ar da za ta kai su ga amfani da wukar yanka. Amma duk da haka nan sarakunan su ne suke damawa a majalisun kananan hukumomin da ake kira en’e-en’e, ta hanyar fasa haraji da amfanin da kudaden da aka samu dangane da haka. Sai a shekarar 1976 ne aka kirkiro tsarin kananan hukumomi don a bai wa talakawa damar zaben wadanda za su shugabance su, wato ciyaman a madadin sarki da kansiloli a madadin ‘yan majalisar sarkin, kuma dukkansu talakawa ne ‘yan uwansu.
Koda yake an samu gagarumar nasara wajen haka, talakawa dai ba su gamsu ba kwarai, domin suna gani an kashe maciji ne ba a sare kansa ba. Saboda dai an bar batun karbar haraji a hannun wakilan sarakuna, watau masu unguwanni wadanda ke wulakanta su idan sun kasa biyan harajin ketar da ake labta masu. Sai a shekarar 1979 ne, bayan jam’iyyar PRP, watu gyauron NEPU Sawaba ta kafa gwamnati a jihohin Kano da Kaduna, ta soke batun karbar haraji, ba domin ba shi da wani amfani ne a gare su ba, a’a, sai dai domin ana fakewa da batun harajin ne ana uzzura wa talakawa. Wannan ne ya sa aka kai ga ba kare bin damo tsakanin dangantakar talaka da sarakuna.
Ta fannoni da yawa za a fahimci cewa rayuwa irin ta malam Aminu ta yi armashi, ta kuma amfani talaka, ta taimaka wajen ingantuwar al’amuran siyasa. Saboda haka nan take da wuyar kwaikwaya, sai ga wanda ya kawar da kai daga abin duniya, ya kuma kyamaci kazantar cikinta. Lokacin da talakawa suke kukan rashin masoyinsu, jagorarsu ga alheri, wanda ya yi fafutuka don ganin sun zama wani abu a cikin harkokin mulki da na siyasa har da al’amuran kasuwanci, sai ga Janar Muhammadu Buhari wanda ya bayyana bayan watanni takwas da rasuwar Aminu Kano, a matsayin shugaban mulkin sojan da ya shimfida adalci ya kamanta gaskiya don kawar da zaluncin da ya yi wa talakawa katutu, ya kuma hana su more gardin rayuwa.
Jama’a sun amince da Janar Buhari don sun san shi mutum ne mai kamanta gaskiya da aikata kyawawan halayen da suka sanya malam Aminu Kano ya shiga zukatan talkawa. Dangane da haka suka raja’a a gare shi a gwagwarmaya da gwa-gwa-gwar da aka dade ana yi don ceton talaka daga kangin zalunci da dabaibayin fatara da mayata da danniyar shugabanni masu tsananin son-kai. Ala kulli halin dai yanzu Buhari ne makwafin Malam Aminu, kuma jama’a sun tabatar shi ne zai kwatanta halaye irin na Malam Aminu don daukaka matsayin ‘yan Arewa da ma Nijeriya baki daya. Lokacin da talakawa suke yawan tunawa da malam Aminu, suke kuma kwanzarta shi, sai ga shi sun kuma dukufa wajen yi wa Janar Muhammadu Buhari fatan alheri da samun nasara a dambarwar da zai yi da makiya talakawa da wadanda suke neman su kawo cikas cikin rayuwarsu. Malam Aminu da Janar Buhari samma kal-kal ne, duk daya suke ba su amincewa da danniya da zalunci, watau abin da ake kira kashin dankali a harkokin zamantakewa da na mulki.