Amir Hassan: dan shekara 12 mai wakar fadakarwa
Amir Hassan mawaki dan shekara 12 ne, ya bayyana dalilin da ya sa ya fara waka da burinsa dangane da waka da kuma dalilin da ya sa ya zabi jigon fadakarwa duk da karancin shekarunsa. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Za mu fara da tarihinka a takaice?Sunana Amir Hassan, an haife ni a watan Maris, […]
Amir Hassan mawaki dan shekara 12 ne, ya bayyana dalilin da ya sa ya fara waka da burinsa dangane da waka da kuma dalilin da ya sa ya zabi jigon fadakarwa duk da karancin shekarunsa. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Za mu fara da tarihinka a takaice?
Sunana Amir Hassan, an haife ni a watan Maris, shekarar 2002 a Unguwar Tarauni da ke Kano. Ni ne na uku a gidanmu. Ina da yayu mata biyu da kanne biyu. Ina aji biyu a makarantar sakandare mai suna Amazing Secondary School.
Me ya hankalinka har ka fara waka?
Abin da ya ja hankalina na fara waka shi ne, a yawan lokuta nakan kalli yadda ’ya’yan Turawa da Larabawa suke waka, hakan ya ba ni sha’awa, inda nake so in zama na daya a Arewacin Najeriya.
A yanzu ka yi wakoki kamar nawa?
Na yi wakoki kamar 10, a ciki akwai ‘Ilimin Addini Da Na Zamani’ da ‘Zaman Lafiya’ da ‘Sabon Sarkin Kano’ da ‘Mahaifiyata’ da ‘Waka Baiwa Ce’, sannan ina wakokin zagayowar haihuwa ta yara da kuma tallace-tallacen da ake bukatar muryar yaro.
Wacce waka ka fi so a cikin wakokinka?
Gaskiya na fi son wakar ‘Zaman Lafiya’, saboda tana kira ne a rika zaman lafiya, wanda ka sani idan babu zaman lafiya babu abin da zai tafi daidai.
Yaya kake hada karatu da kuma waka?
Gaskiya lokacin karatuna daban, haka shi ma na waka daban.
Wa yake daukar nauyinka?
Mahaifana, mahaifiyata ita ce furodusata, tana yi mini dukkan abin da nake so.
Da wadanne mawaka ka fi jin dadin waka?
Ibrahim Sadi da Ummi Nagarta.
Me mahaifinka ya ce lokacin da ka sanar masa za ka yi waka?
Mahaifina ya ji dadi sosai, kuma ya yi mini addu’ar samun nasara, sannan na mayar da hankalina a kan karatu da wakar da na sa a gaba.
Kai kake rubuta wakokinka?
A gaskiya ba ni nake rubuta wakokina ba, mawaki Ibrahim Sadi ne yake rubuta mini.
Kana da burin yin wakokin fina-finai?
Ina da burin yin wakokin fina-finai, musamman idan wanda zai hau wakar yaro ne, kuma ko yanzu aka ba ni zan iya.
Yanzu wane shiri kake yi a harkar waka?
Zan fitar da albam nan gaba in sha Allahu.
Wadanne matsaloli kake fuskanta a halin yanzu?
Gaskiya ba ni da wata matsala idan a kan waka ne, domin ina tare da Sadi Sidi Sharifai.
Me ’yan uwa da abokai suka ce dangane da wakar da kake yi?
Ba ni da matsala da ’yan uwana, domin murna suke yi. Abokaina ma sha’awa nake ba su har akwai wanda ya ce yana so ya zama mawaki. Ina godiya ga Allah da Ya ba ni baiwar waka.
Wane buri kake da shi a harkar waka?
Burina shi ne in fadakar da al’umma, su amfana da wakokina kuma in bar tarihi, sannan ina mika godiyata ga Ibrahim Sadi wanda ya tsaya don komai ya tafi yadda ake so, kama daga yadda zan dinga fitar da kalmomi da salon da na dauka wajen rera wakokina har zuwa lokacin da zan kammala, kuma ni ma nan gaba in sha Allahu zan fara rubuta waka da kaina.