Ammani Inuwa ya kwanta dama

Fitaccen dan siyasar nan Alhaji Ammani Inuwa ya rasu a ranar Litinin da ta gabata. Marigayin wanda tsohon Shugaban Jam’iyyar ANPP ne na Jihar Kano ya rasu ne a waniasibiti mai zaman kansa bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.daya daga cikin ’ya’yan marigayin, Nasiru Ammani Inuwa ya shaida wa Aminiya cewamahaifnsu […]

Ammani Inuwa ya kwanta dama
Ammani Inuwa ya kwanta dama

Fitaccen dan siyasar nan Alhaji Ammani Inuwa ya rasu a ranar Litinin da ta gabata.

Marigayin wanda tsohon Shugaban Jam’iyyar ANPP ne na Jihar Kano ya rasu ne a wani
asibiti mai zaman kansa bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.
daya daga cikin ’ya’yan marigayin, Nasiru Ammani Inuwa ya shaida wa Aminiya cewa
mahaifnsu ya jima ba ya da lafiya duk da cewa bai jima a kwance a asibiti ba. “Ya dauki tsawon lokaci ba ya da lafiya duk da cewa bai dade a kwance asibiti ba. A wannan karon ne jikin ya yi tsanani har aka garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa inda Allah Ya yi masa cikawa a safiyar Litinin,” inji shi.
Marigayi Alhaji Ammani Inuwa ya rasu yana da shekara 80, kuma ya rasu ya bar matan aure tare da ’ya’ya 17.
An yi jana’izar marigayin tare da binne shi a makabartar Wali Maigiginya, inda manyan mutane da dama da suka hada da ’yan siyasa da ’yan kasuwa suka halarci jana’izar.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista