Gwamnatin Sokkwato na shirin daure matashi a kurkuku kan soshiyal midiya —Amnesty

Gwamnatin Sakkwato na shirin tura matashin zuwa kotu domin aika shi gidan gyaran hali, a cewar Amnesty International

Gwamnatin Sokkwato na shirin daure matashi a kurkuku kan soshiyal midiya —Amnesty

Kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta zargi Gwamnatin Sakkwato da kama wani mai amfani da shafukan sada zumunta Shafi’u Umar Tureta.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce tsare matashin ya saɓa ƙa’ida saboda ya wallafa wani bidiyon da ake zargin mai ɗakin gwamnan jihar ce ake yi wa ‘liƙi’ da kuɗi a wajen bikin tunawa da ranar haihuwarta.

Kungiyar ta ce “Gwamnatin Sakkwato na shirin tura matashin zuwa kotu domin aika shi gidan yari da kuma yunƙurin ɗaura mishi laifukan da bai aikata ba.”

“Ya kamata gwamnan ya maida hankali daƙile matsalar tsaron da ke damun jihar Sakkwato, da magance matsalar yaran da ba su zuwa makaranta a jihar, ba ƙoƙarin kulle bakin ’yan adawa ba” inji kungiyar.

Tuni dai matasa ke ta cece-kuce kan kama matashin da ’yan sanda suka yi a jihar, inda suka ce gwamnatin ce ta ba su umarnin kama Tureta.

Ita ma jam’iyar PDP a jihar ta fitar da sanarwar neman a saki matashin.

Zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta fitar da wata sanarwa game da batun da ake zargin tana da hannu a ciki ba.