Amnesty ta zargi sojoji da keta hakkin dan Adam a Najeriya *Za mu bincika – Rundunar Soja

kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya (Amnesty International) ta ce ta bankado bayanan da ke nuna cewa sojojin Najeriya sun aikata laifuffukan yaki a yankin Arewa maso Gabas. Ta kuma zargi Boko Haram da aikata miyagun laifuffukan yaki.A ranar Litinin ne Amnesty ta saki wani faifan bidiyo da ta ce na nuna sojoji suna […]

Amnesty ta zargi sojoji da keta hakkin dan Adam a Najeriya *Za mu bincika – Rundunar Soja

kungiyar kare hakkin dan Adam ta duniya (Amnesty International) ta ce ta bankado bayanan da ke nuna cewa sojojin Najeriya sun aikata laifuffukan yaki a yankin Arewa maso Gabas. Ta kuma zargi Boko Haram da aikata miyagun laifuffukan yaki.
A ranar Litinin ne Amnesty ta saki wani faifan bidiyo da ta ce na nuna sojoji suna yi mutane da ake zargi ’yan Boko Haram ne yankan rago, tare da taimakon ’yan bangar da ake kira sibiliyan JTF, inda ake jefa gawarwakin wadanda aka kashe a wani babban kabari.
Amnesty ta ce ta samu wani yanki na bidiyo da zai iya zama hujja ta aikata laifin yaki da sojoji suka yi ne daga majiyoyi da dama a lokacin wani bulaguro a Jihar Borno.
“Wannan sabuwar shaida ta dada nuna miyagun ayyukan da dukan bangarorin suka aikata a yayin rikicin. Me za a ce idan sojoji za su iya aikata irin wannan mugun aiki da aka nuna a faifan? Babban Sakataren Amnesty Salil Shetty, ya bayyana.
Ya kara da cewa “Wadannan ba hotuna da muke fatar gani daga gwamnatin da take ganin kanta a matsayin shugabar Afirka b ace. Munanan hotunan da shaidun da muka samu suka karfafa su na nuna yadda sojoji da sibiliyan JTF ke kashe jama’a ba tare da shari’a ba a kai a kai.”
kungiyar ta Amnesty ta nemi a gudanar da bincike a kan abin da ta kira yawaitar keta hakkin dan Adam daga bangarorin biyu.
A martanin Rundunar Sojojin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan zargin da kungiyar Amnesty ta yi wa dakarunta.
Wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun Kakinta Manjo Janar Chris Olukolade, ta ce za ta dauki wannan batu da muhimmanci, kuma ta damu matuka da hotunan bidiyon da ake ta yadawa da suka zama hujja ga kungiyar ta Amnesty.
Haka rundunar sojin ta ce baya ga binciken hadin gwiwa ta kuma kafa wani kwamitin manyan jami’an soja da kwararru a fannin kimiyya domin nazarin hotunan bidiyon.
Sanarwar ta kuma ce duk wanda aka samu hannunsa a cikin wannan lamari zai fuskanci shari’a kamar yadda doka ta tanada.