Amokachi ya zama koci a Finland

Tsohon mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Daniel Amokachi ya zama kocin wani kulob mai suna JS Hercules a Finland da ke Nahiyar Turai.Amokachi wanda ya taba horar da  kulob din Enyimba International da Nasarawa United da kuma Ifeanyi Uba a Najeriya ya sanya wa kulob din hannu ne a kwantaragin shekara daya […]

Amokachi ya zama koci a Finland
Amokachi ya zama koci a Finland

Tsohon mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Daniel Amokachi ya zama kocin wani kulob mai suna JS Hercules a Finland da ke Nahiyar Turai.
Amokachi wanda ya taba horar da  kulob din Enyimba International da Nasarawa United da kuma Ifeanyi Uba a Najeriya ya sanya wa kulob din hannu ne a kwantaragin shekara daya kamar yadda wata sanarwa da kulob din ya fitar ta nuna.
Tsohon dan kwallon Eberton na Ingila da Besiktas na Turkiyya, Daniel Amokachi kulob din karshe da ya horar a Najeriya shi ne Ifeanyi Ubah na Najeriya  kafin ya wuce Turai don cigaba da horar da kulob din JS Hercules na Finland.
Sanarwar da kulob din ya fitar ta nuna kulob din JS Hercules da ke garin Oulu na Finland ya kulla yarjejeniyar shekara daya da Daniel Amokachi  sannan tsohon kocin kulob din Pekka Haarmen, yanzu ya koma mataimakin Amokachi.
Shi dai kulob din Hercules ya samu nasarar hayewa zuwa gasar firimiya mataki na biyu ne a bara inda ake sa ran Amokachi zai cigaba da horar da ’yan kwallonsa don ganin sun samu hayewa matakin farko na gasar firimiya ta kasar a bana.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa