Amorim ya zama sabon kocin Manchester United

Amorim ne koci na shida da zai horar da ƙungiyar tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya.

Amorim ya zama sabon kocin Manchester United

Ruben Amorim ya zama sabon kocin Manchester United kamar yadda ƙungiyar ta tabbatar.

Kocin mai shekara 39, wanda ɗan ƙasar Portugal ne, zai fara ne aiki ne bayan hutun wasan ƙasa da ƙasa daga ranar 11 ga Nuwamban 2024, bayan ya sanya hannu a kwantiragin aiki zuwa shekarar 2027.

Yanzu dai tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar, Ruud van Nistelrooy ne ke kocin riƙon ƙwarya, kuma zai ci gaba da riƙon har zuwa lokacin da Amorim zai fara aiki.

Amorim ne koci na shida da zai horar da ƙungiyar tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya, bayan shekara 26 yana horar da ’yan wasan ƙungiyar. Sannan akwai wasu guda huɗu da suka yi riƙon ƙwarya.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce, “Ruben na cikin zaƙaƙuran masu horar da ’yan wasa da suke ganiya a turai a yanzu.”

Wasan farko da Amorim zai fara a ƙungiyar shi ne wasan Manchester United da ƙungiyar Ipswich a ranar 24 ga Nuwamba, sannan a ranar 28 ga Nuwamba zai jagoranci ƙungiyar domin fafatawa da Bodo/Glimt a gasar Europa.

Sakin Amorim ya zo da wasu sharuɗɗa — da suka haɗa da ci gaba da zama a Sporting don kula da wasanni uku masu muhimmanci, ciki har da wasan da za a yi da Manchester City, kafin ya koma Old Trafford.

United ta amince ta biya ƙarin Yuro miliyan 1 don tsawaita wa’adinsa, yayin da Sporting kuma ta buƙaci kusan Yuro miliyan 5 don ba da damar wasu manyan ma’aikatan Amorim, ciki har da kociyan ƙungiyar farko Emanuel Ferro da Adelio Candido da Carlos Fernandes su bi shi zuwa gasar Premier.

Amorim ya bayyana sha’awarsa na ficewa daga Sporting cikin sauƙi, inda ya ƙulla alaƙa mai ƙarfi da magoya bayan ƙungiyar bayan ya jagorance ta zuwa gasar lig biyu, na farko cikin shekaru kusan ashirin.

Rahotanni sun ce United ta amince da waɗannan sharudda, inda ta amince Amorim ya jajirce a ƙungiyar da ya jagoranta tsawon shekaru hudu.

A farkon makon nan ne Manchester United ta kori kocinta Erik ten Hag sakamakon rashin kataɓus da kungiyar ta yi a kakar wasa ta bana.

United ta koma mataki na 14 a teburin gasar bayan ta sha kashi karo na huɗu a wasanni tara a West Ham ranar Lahadi, inda wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce: “Erik ten Hag ya bar muƙaminsa na kocin Manchester United na maza.”