Amotekun ta ceto manomi bayan kwanaki 5 da garkuwa da shi a Ondo

A tsawon kwanakin da na shafe a hannunsu babu abin da nake ci sai busasshen garin kwaki.

Amotekun ta ceto manomi bayan kwanaki 5 da garkuwa da shi a Ondo

Rundunar tsaro ta Amotekun a Jihar Ondo ta yi nasarar kubutar da wani manomi mai suna Bello Audu da aka yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki 5 tare da kama mutane 9 da ake zargi da sace shi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an yi garkuwa da manomin ne a daidai lokacin da yake yin Salla a kofar gidansa a garin Akunnu-Akoko a Karamar Hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma.

Da yake holen ababen zargin da aka kama ga manema labarai a Litinin a ofishin sa da ke birnin Akure, Kwamandan Rundunar, Cif Adetunji Adeleye ya ce jami’an nasa sun yi badda-kama wajen shiga dajin da aka boye Bello Audu a matsayin iyalinsa da suka je biyan kudin fansa ga mutanen da suka sace shi.

Kwamandan ya ce a nan take jami’an suka kama uku daga cikin wadannan mutane da suka fito daga cikin dajin domin karbar kudin fansa.

Ya ce daga bisani kuma aka kama sauran shida a maboyarsu tare da kubutar da wanda abin ya shafa.

Da yake yi wa ’yan jarida bayanin yadda lamarin ya auku, Bello Audu wanda mutumin garin Olorun a Jihar Kwara ne, ya ce “da misalin karfe 7 na yammacin wannan rana ce wasu mutane shida rike da sanduna da bindiga a hannunsu suka same ni ina yin Salla a kofar gidana a garin Akunnu-Akoko.

“A daidai lokacin ne suka umarci da na bi su cikin dajin da suka yi garkuwa da ni na tsawon kwanaki 5 kafin jami’an Amotekun su kubutar da ni daga hannun su.”

Bello Audu ya ce ya shafe kwanaki 5 yana cin busasshen Garin-Kwaki dan kadan da suke ba shi a matsayin abinci ba tare da ruwan sha ba a kullum.

Ya ce “sun tuntubi iyali na a game da yadda za a biya su kudin fansa kafin su sake ni.

“Ba tare da saninsu ba jami’an Amotekun suka yi badda-kama a matsayin iyali na da suka je biyan kudin fansa, inda suka kama su kuma suka ceto ni.”