Amotekun: Zakaran gwajin dafin ’yan sandan jihohi
A ranar Alhamis 9 ga Janairun nan ne rundunar tsaron nan mai suna ‘Amotekun’ da gwamnonin jihohin yammacin kasar nan suka kafa da nufin tabbatar da tsaro a jihohin da ke yankin Kudu maso Yamma ta fara aiki. Da yake karin haske game da dalilan kafa rundunar, Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, wanda shi ne […]
A ranar Alhamis 9 ga Janairun nan ne rundunar tsaron nan mai suna ‘Amotekun’ da gwamnonin jihohin yammacin kasar nan suka kafa da nufin tabbatar da tsaro a jihohin da ke yankin Kudu maso Yamma ta fara aiki.
Da yake karin haske game da dalilan kafa rundunar, Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, wanda shi ne Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya, ya bayyana cewa, rundunar Amotekun, wadda kuma ake kiranta da ‘Rundunar Tsaro ta Yankin Yammacin Najeriya,’ (WNSN) ba rundunar ’yan sandan yankin yammacin Najeriya ba ce.
Ya ce an kafa rundunar ce domin yaye wa al’ummar yankin Kudu maso Yamma tsoron da ke cikin zukatansu, musamman dangane da matsalar tsaron da ake fama da ita a ’yan kwanakin nan.
Gwamnan wanda ya yi wannan bayani a yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da rundunar ta Amotekun da aka yi a garin Ibadan a Jihar Oyo, ya ce gwamnonin yankin suna samun matsin lamba wajen ganin sun yi wani hobbasa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar da ke yankin.
Ya kara da cewa, matsin lambar ya kara yawa ne a lokacin da aka kashe Funke Olakunrin, ’yar Mista Rubean Fasoranti, Shugaban Kungiyar Kare Muradun Yarbawa ta Afenifere da aka yi a bara.
Ya ce wadansu gwamnonin sun bayar da shawarar a kafa rundunar ’yan sandan jihohi ne, amma sai a karshe aka yanke shawarar kafa wannan rundunar ta Amotekun domin tabbatar da tsaro a yankin na Kudu maso Yamma. Sai dai kuma ya bayar da tabbacin cewa ba an kafa rundunar tsaron ce domin ta yi wa rudunar ’yan sandan Najeriya zagon-kasa ba.
Koda yake gwamnonin yankin Yamma din sun saya wa rundunar ta Amotekun motoci da kayan aiki, amma Rundunar ’Yan sanda ta ce ba za ta yarda jami’an tsaro na Amotekun su rika rike bindigogi masu karfi kamar kirar AK 47 ba, sai dai bindiga irin ta maharba, wato ‘harbi-ruga’.
Yanzu dai an zura ido ne a ga yadda rundunar tsaro ta Amotekun za ta gudanar da ayyukanta, shin za ta kare hakkokin kowa da kowa da ke zaune a yankin ne ko kuwa hakkokin kabilar Yarbawa kawai za ta rika karewa, babu ruwanta da na baki mazauna yankin?
Wata majiya ta bayyana cewa tuni har rundunar ta Amotekun ta fara ginda ya wa Fulani makiyaya da ke zaune a yankin sharudda, wanda hakan ke nuna kamar dai an kafa rundunar ce domin yaki da Fulani makiyaya da ke zaune a yankin. Lokaci ne dai zai nuna inda rundunar ta Amotekun ta dosa.
Wannan rundunar za ta zama zakaran gwajin dafi game da kiraye-kirayen da ake ta yi, musamman daga yankin Kudancin kasar nan, na bukatar samar da rundunar ’yan sanda mallakar jihohi. Da ma yankin Kudu maso Yamma ne kan gaba wajen wannan yunkurin. Yanzu manuniya za ta nuna, shin rundunar za ta rika kare hakkin duk wanda aka zalunta ne, ko kuwa za ta rika zaluntar wadansu ne?
Wannan abu da gwamnoni jihohin Yamma suka yi zai bude kofa ga sauran yankuna su ma su kafa tasu rundunar tsaron, sai dai kuma abin tsoro shi ne, kada irin wadannan rundunonin su zama barazana ga zaman lafiyar kasar nan, domin ga dukkan alamu ana kafa su ne domin kabilanci ba domin kare al’umma baki daya ba.
Muna fata wannan runduna ta Amotekun, wadda take nufin ‘Damisa,’ ba za ta zama barazana ga hadin kan kasar nan ba.