Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (10)
Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aka ji da kokari? Ni ma a taimaka mini da bayani a kan yadda zan kare shafin Facebook dina daga masu kutse. Na gode. Daga Haruna Usman: [email protected]. Wa alaikumus salam, barka dai Malam Haruna. Idan kana son tsare shafinka na Facebook ko akwatin Imel dinka daga sharrin masu kutse […]
Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aka ji da kokari? Ni ma a taimaka mini da bayani a kan yadda zan kare shafin Facebook dina daga masu kutse. Na gode.
Daga Haruna Usman: [email protected].
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Haruna. Idan kana son tsare shafinka na Facebook ko akwatin Imel dinka daga sharrin masu kutse (Hackers), na farko ka zabi kalmar sirri (Password) mai tsauri, mai dauke da haruffa da lambobi da kuma alamomin rubutu (irin su @ ko # ko $ misali), kuma kada ta kasance gajeriya. Ana son adadin kalmar sirrinka ya fara daga takwas zuwa sama, iya abin da za ka iya tunawa. Kada ka sa lambar wayarka. Kada ka sa sunanka. Kada ka sa sunan gari ko danka ko wani na kusa da kai.
Kada ka sa ranar haihuwarka. A takaice dai, ka zabi abin da idan ba kai ba, babu wanda zai iya hararo shi, sai in ka gaya masa.
Na biyu ka tanadi lambar waya da kuma adireshin Imel a shafinka, saboda bacin rana. Na uku, ka boye su daga shafinka, ma’ana ka je bangaren “Settings” ka canja tsare-tsaren da ke can, ya zama ba kowa zai ga lambar wayarka ba, ko adireshin Imel dinka, sai wanda ka ga damar bayyana masa bayan ya nema.
Abu na hudu, kada ka taba bai wa wani kalmar sirrinka. Idan har bukata ta sa ka ba wani ya sani, to, da zarar dalilin ya wuce ka yi maza ka canja. Na biyar, idan a waya kake amfani da Facebook, ya zama duk saa’r da ka gama aika sako ko karantawa, ka sauka, ma’ana: “Sign Out.” Wannan zai taimaka maka matuka idan wayar ta fadi ko wani ya sace, ba zai iya isa ga shafi ko sakonninka ba. Amma idan kullun a kan shafin kake, don kawai kana son ka rika ganin sakonnin da ke shigowa, to ana samun matsala nan take wanda ya dauke wayar zai iya ganin dukkan sirrinka.
Abu na shida, ka san da wa za ka rika abota, sannan da wa za ka rika hira a Facebook. Sannan wasu kalmomi kake fada ko rubutawa. Duk wata kalma da kana yawan ambatonta a Facebook, kada ta zama cikin Password dinka.
Wadannan, a takaice, su ne matakan da a yanzu zan iya hararowa. Allah Ya yi mana tsari da miyagu, amin. Na gode.