Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (5)

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya ibada? Na yi rajistar akwatin imail na Gmail amma ba na iya bude shi, kuma na shigar da komai daidai. Ina matsalar take? Daga A. A. Hashim. 08061308265 Wa alaikumus salam, Malam Hashim barka ka dai. A ka’idar mu’amala da kayayyaki da hanyoyin sadarwa na zamani, duk bayanin da ka […]

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (5)

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya ibada? Na yi rajistar akwatin imail na Gmail amma ba na iya bude shi, kuma na shigar da komai daidai. Ina matsalar take?

Daga A. A. Hashim. 08061308265

Wa alaikumus salam, Malam Hashim barka ka dai. A ka’idar mu’amala da kayayyaki da hanyoyin sadarwa na zamani, duk bayanin da ka shigar, to, sakamakonsa ne ake aiko maka a matsayin jawabi. Wannan ka’ida ita ake kira: “Garbage-in-garbage-out,” ko “GIGO” a gajarce. Abin da nake cewa a nan shi ne, muddin ka yi rajista ta hanyoyin da aka tanada, ba matsala. Sannan ka shigar da bayanan da ka yi rajista da su wajen bude akwatin Imel din, su ma daidai kamar yadda ka ba da su a farkon budewa, to, ban ga dalilin da zai sa a hana ka shiga ba. Domin koda kulle akwatin suka yi sanadiyyar tsawon lokaci na rashin amfani da shi (wanda yanzu ma an daina rufe akwatin Imel don wannan dalili), to, za su sanar da kai cewa an rufe akwatin na wucin-gadi. Wannan shi ake kira: “Deactibation of Account,” kamar yadda bankuna kan yi, idan ka dauki tsawon lokaci ba ka yi amfani da taskar ajiyarka ba.

A yanzu kamfanonin manhajar Imel na Intanet sun daina rufe akwatin Imel don rashin amfani da shi na tsawon lokaci.  Don haka, ka bincika dai. Ina kyautata zaton dai akwai abin da ba ka shigar da shi daidai ba, musamman kalmar sirri, wato: “Password.” Amma a babin tunatarwa, idan ka tashi hawa akwatin Imel, za ka budo manhajar ne idan ta wayar salula kake amfani, ko ka je shafin ta hanyar manhajar lilo, wato: “Browser” – Chrome ko Edge ko Opera da sauransu – ka shigar da adireshin: <https://m.google.com>.  Nan take shafin da ake shigar da suna (username) da kalmar sirri (password) zai budo.  Sai ka shigar da sunan da ka bayar wajen yin rajista, sannan da kalmar sirrin da ka zaba a wancan wuri ko lokaci.  Muddin ka shigar da komai daidai, za a zarce da kai akwatin Imel dinka kai-tsaye. Idan hakan bai faru ba, to watakila ka mance kalmar sirrinka ce. Ga abin da za ka yi nan kasa:

A nan shafin shigar da suna daga kasa, ka duba za ka ga inda aka rubuta: “Forgot your password?” Ka matsa, shafi zai budo inda za a tambaye ka ka shigar da ranar haihuwarka wadda ka bayar sa’ar da kake rajista. Sannan za a tambaye ka kalmar sirri na karshe da ka yi amfani da ita wajen hawa. Idan ba ka iya tunawa, ka sanya abin da kake da yakinin shi ne ka shigar.  Idan bayanan sun yi daidai da abin da ka bayar, za su ba ka damar canja kalmar sirrinka. Idan ba su yi daidai ba, za a tambaye ka lambar waya ko adireshin Imel din za a iya tuntubarka don warware matsalar.  Ba komai suke son yi ba illa tantance ko kai ne hakikanin mai akwatin Imel din. Idan sa’ar da kake rajista ba ka ba da wani adireshin Imel ko lambar wayar da za a iya tuntubarka ba, kuma a nan ka rubuta, to, za su ce ba kai ba ne mai akwatin Imel din, sai su rufe shafin su ba ka hakuri. Ba za ka ji dadi ba saboda rashin biyan bukata, amma sun yi haka ne don kariya gare ka.

Wannan shi ne dan abin da zan iya bayarwa na agaji. Ina yi maka fatar alheri kuma Allah Ya sa a dace, amin.  Na gode.

 

Salamun alaikum Baban Sadik, Allah Ya kara basira.  An sace min shafin Facebook dina wata biyar da suka gabata. Na bi duk hanyoyin da zan bi amma na gagara gyarawa.  Daga karshe sun ban wata uku cewa za su gyara mini, amma da suka saki shafin, iya sunana ne kawai ya dawo da abokaina.  Amma hotunana ba su dawo ba.  Shi ne nake tambaya ko akwai wasu hanyoyin da zan bi su dawo. Na gode.

Daga: Ayuba Umar, Dutse, Jigawa: 08032702234

Wa alaikumus salam Malam Ayuba da fatar kana lafiya. Lallai wannan abin a damu ne, kuma ruwan dare ne a Facebook. Kamar yadda suka yi maka alkawari kuma suka cika, sai dai ba yadda kaso ba, haka lamarin yake. Akwai dalilai kusan dari ba daya da suka sa hakan ke faruwa.  Idan ka ga an dawo maka da shafinka na Facebook amma babu wasu abubuwan naka, ko dai ya zama wani ne ya sace ko ya kwace shafin a farkon lamari, kuma ya goge maka wadannan bayanai naka.  Wannan zai sa idan aka kwato shafin, ya zama ka rasa su. Na biyu kuma ta yiwu sa’ar da aka kwace shafin an yi amfani da bayanan da ke kan shafin ta hanyoyin da suka saba wa ka’idojin Facebook.  Wannan zai sa idan suka gane cewa ba laifinka ba ne, su dawo maka da shafin amma kuma su goge abin da ya saba wa ka’idarsu.

Don haka, tunda har ka rasa wadannan hotuna, babu wata hanya da za ka iya dawo da su, sai dai ka sake dora su in har kana da su a waya ko kwamfutarka. Domin duk abin da aka goge a shafin Facebook, babu wata hanya ta musamman da suka tanada don dawo da su.  Don haka ne ma ya sa suka tanadi wata hanya da kowane mai shafi a Facebook zai yi amfani da ita wajen taskance dukkan bayanan da ke shafinsa. Ma’ana za ka iya saukar da dukkan bayanan da ke kan shafinka na Facebook a kan waya ko kwamfutarka, don adana su. Sun yi haka ne don bacin rana.  Shi ya sa ma idan ka yi yunkurin gogewa (Delete) ko rufe shafinka na Facebook (Deactibate) ta hanyar da suka tanada a bangaren tsare-tsare (Settings), kafin ka latsa maballin gogewa sai sun tallata maka cewa ko za ka taskance bayananka kafin gogewa?

Wannan dan abin da ya samu ke nan na karin haske. Allah kare gaba kuma Ya sa a dace. Na gode.