Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (6)

Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik yana lafiya. Don  Allah  Baban  Sadik ina  son  a yi min bayani kan abin  da  zan yi la’akari  da shi  in  zan sayi kwamfuta (Laptop  ko  Desktop). Kuma wace kirar kwamfuta  ta  kamata  in  saya (HP, Dell, Acer etc)?  Hassan Abdul: 08033390046 Wa alaikumus salam, barka dai Malam Hassan.  […]

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (6)

Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik yana lafiya. Don  Allah  Baban  Sadik ina  son  a yi min bayani kan abin  da  zan yi la’akari  da shi  in  zan sayi kwamfuta (Laptop  ko  Desktop). Kuma wace kirar kwamfuta  ta  kamata  in  saya (HP, Dell, Acer etc)? 

Hassan Abdul: 08033390046

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Hassan.  Da fatan kana lafiya.  Bayani kan me ya kamata ka yi la’akari dashi wajen sayen kwamfuta sabuwa, wannan ya danganci abubuwa da dama.  Na farko nawa ka tanada?  Na biyu, me kake son yi da kwamfutar?  Akwai kwamfutoci nau’o’i daban-daban, daga kamfanonin kwamfuta daban-daban.  Wasu masu dan karen tsada, wasu kuma masu araha.  Wasu kuma sun hada tsakanin masu tsada da masu araha.  Kamar masu son sayen kwamfutocinsu, kamfanonin kera kwamfuta su ma suna da nasu manufofin na kasuwanci da suke la’akari da su yayin kera kwamfutocin da kake gani a shaguna ko a hannun mutane ana amfani da su.

Amma duk da haka, akwai wasu kebantattun siffofi da suka kama ta a yi la’akari da su wajen sayen kowace irin kwamfuta ce ma.  Na farko kuma wanda ya fi kowanne muhimanci, shi ne na’urar sarrafa bayanai ko umarnin da ake bai wa kwamfuta lokacin da ake amfani da ita.  Wannan shi ake kira: “System Processor.”  A duk sa’ar da ka latsa wani abu a jikin kwamfuta wanda ya danganci ba da umarnin ta yi wani abu, za ka so nan take ka ga ta aiwatar maka da shi.  Idan ka latsa wata manhaja, kana son nan take ka ga manhajar ta budo ba bata lokaci.  Idan ka kunna kwamfutar, nan ma kana son kafin kiftawa da bisimillah, ta farka firgigi.  Haka idan ka ta shi zuba mata bayanai daga wata ma’adanar, za ka so nan take ka ga ta karbe su ba da jinkiri ba.  Abin da ke sanya kwamfuta ta zama hakan kuwa shi ne wannan na’ura ta “Processor.”

Wannan na’ura ta Processor dai tana nan mizani-mizani.  Akwai babba akwai karami.  Kwamfutoci masu araha kan zo da mafi karancin mizanin “Processor” ne.  Galibi bai wuce 1.4Ghzt. Ko kuma 1.6Ghzt. “Processor” mai irin wannan mizanin dai za ta yi maka aiki, amma ba cikin kazar-kazar da kuzari ba.  Akwai kuma mizani babba wanda ke faraway galibi daga 2.4Ghzt, har zuwa 3.2Ghzt.  Kwamfutoci masu dauke da irin wannan mizani ba su da matsala.  Kuma za ka same su a guje, sai ka ce an koro su, da zarar ka ba su umarni.  Wannan na’ura ta “Processor” dai a gine take a kan kwarangwal din kwamfuta, wato: “Motherboard,” muddin kana son canja ta, sai dai ka canja “Motherboard” din gaba daya.  Wannan bai cika faruwa ba sosai.

Abu na biyu mai muhimmanci kuma shi ne masarrafar bidiyo (Bideo Card) da masarrafar nuna hotuna da rubutu da zane (Graphics Card), da Ma’adanarta (Memory).  Na biyun farko su ne ke taimaka maka wajen mu’amala da bidiyo – ka gan shirau-rau-da hotuna ko rubutun da talabijin da kwamfutar ke nuna maka.  Shi kuma ma’adana ko kwakwalwarta shi ne ke taskance dukan manhajojin da kwamfutar ta zo da su da wadanda nan gaba za ka zuba mata, sannan ta ba ka damar mu’amala da su a duk sa’ar da ka budo su, ta hanyar tanada musu wurin da za su zauna na wucin-gadi.  Aikin farko na faruwa ne a babbar ma’adana,  wato “System Hard Dribe,” na biyu kuma a wata ma’adana ta wucin-gadi da ake kira: “Random Access Memory,” wato: “RAM” ke nan a takaice.  Su ma, kamar masarrafar “Processor,” suna da nasu mizanin daban-daban.  Amma bambancin shi ne, su ana iya canja su cikin sauki.  Kamar RAM, idan ka sayi kwamfuta mai dauke da 2GB RAM, kana iya kara mata wani 2GB RAM din.  Haka idan 4GB RAM ne, kana iya kara mata kodai 2GB ko wani 4GB din; ya danganci girma da mizanin “Motherboard” dinta. Haka a bangaren bidiyo da masarrafar sarrafa hotuna da rubutu, duk kana iya sayen wani ka dora mata.

Sauran abubuwan da ake la’akari da su sun hada da girman fuskar kwamfutar (Screen Size) da mizanin batirinta wajen rike caji da ingancin sinadaran da aka kera kwarangwal dinta da su da dai sauransu.  Kari a kan haka, yana da kyau ka yi la’akari da yaduwar irin kwamfutar da za ka saya.  Akwai wasu kwamfutoci da ba su yadu ba sosai, kamar mota ce, idan ka saye ta kuma daga baya ta samu matsalar da ake bukatar canja wani bangarenta, ba a samu cikin sauki ba. A karshe dai, kwamfutocin da suka shahara a nan sosai su ne HP da Dell da Acer.  Akwai wasu nau’o’in daban, irin su Samsung da Toshiba da MacBook na kamfanin Apple da sauransu.  In da hali ka sayi HP, don ta fi saukin kudi, ko da babba ce, idan aka kwatanta ta da Dell.  Dell tana da inganci amma tana da tsada matuka. Daga HP sai Acer wajen saukin kudi.  In kuma kana da hali sosai sai ka sayi Dell din. Iya abin da zan iya cewa ke nan a halinyanzu.  Allah Ya sa a dace, amin.

 

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Ni mutum ne mai sha’awar harkar Intanet.  Amma ba ni da ilimi mai zurfi na zamani, sai harshen Hausa. Ta yaya zan yi burina ya cika? 

Nuhu Adamu Nyalun, Wase, JiharFilato.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nuhu.  Tu’ammali da fasahar Intanet ba ta bukatar dole sai ka iya Turanci.  A takaicen takaitawa ma dai, harshen Turancin Ingilishi daya ne daga cikin harsunan da ake amfani da su a Intanet duk duniya.  Bayan shi akwai harshen Mandarin (Chinese) da harshen Spanish da sauransu.  Tabbas wadannan harsuna sun fi shahara ne saboda galibin bangarorin Intanet da giza-gizan sadarwa na duniya tare da manhajojin da ke tafiyar da fasahar, an tsara su ne cikin harsunan.  Wanda wannan ya sha bamban da harshen Hausa.

Duk da ba ka yi bayanin me kake nufi da cikar burinka ba, ina zaton kana nufinsamun damar iya mu’amala da fasahar ne ko dai wajen sadarwa ko wajen kasuwanci da sauransu. In don wannan ne, abin da kake bukata shi ne wanda zai dora ka a hanya.  Ka samu wanda zai karantar da kai a aikace, hanyoyin da za ka rika bibiya wajen yin abin da kake son yi.  Cikin kankanen lokaci za ka samu cikar burinka.  Idan kuma ban fahimci tambayarka ba ce  sosai, to kana iya aiko mini sako na musamman sai in kira ka mu tattauna.

Ina yi maka fatar alheri a koyaushe.  Allah Ya sa a dace, amin.