Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (9)
Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah Ya kara maka kwarin gwiwa da kwakwalwa da basira a kan wannan shafi naka. Allah Ya kare mana kai daga sharrin masharranta. Domin kana ilimantar da mu ta bangarori da dama a rayuwa kamar: fannin sadarwar waya da kwamfuta da ilimin sararin samaniya da fasahar haske da tauhidi da asalin […]
Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah Ya kara maka kwarin gwiwa da kwakwalwa da basira a kan wannan shafi naka. Allah Ya kare mana kai daga sharrin masharranta. Domin kana ilimantar da mu ta bangarori da dama a rayuwa kamar: fannin sadarwar waya da kwamfuta da ilimin sararin samaniya da fasahar haske da tauhidi da asalin hallita da sauransu. Allah Ya jarabce ni da son kwamfuta da kuma ilimin waya, ina karuwa sosai. Sanadiyyar haka na soma kasuwancin sayar da kwamfuta har ma da TB Plasma daga Legas zuwa Kaduna. Sunana: Nuhu Abdullahi.
Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nuhu. Ina matukar farin cikin jin cewa wannan shafi ya taimaka wajen jefa maka sha’awa da son wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa, kuma cikin dacewar Allah har ya zama sanadiyyar hanyar kasuwanci gare ka. Na gode matuka da addu’o’inka. Ina rokon Allah Ya tabbatar da kai kan wannan kasuwanci sannan ya albarkaci dukkan abin da ka taba ko zuba na jari a ciki.
Daman rayuwa haka take; a yayin da wadansu ke karatu su bar karatun a inda suka karanta shi, wadansu kan karanta ne su dauke shi cikin kwakwalwa da zuciyarsu. Hakika ana son duk abin da ka karanta, ka nanata shi cikin zuciyarka, ka jinjina shi cikin kwakwalwarka, sannan tsinci abin da ka tsinta a ciki. Wannan zai taimaka maka a duk sa’ar da ka ci karo da wani abu mai alaka da shi. In da hali ma ya zama sanadiyyar tsira a gare ka duniya da Lahira.
Kamar yadda na sha nanatawa a wannan shafi, wannan fanni na bincike kan kimiyya da fasaha, asali ba a makaranta na karance shi ba, kai-tsaye. Hasali ma, idan ka kebe tilasci na tsarin makaranta da ya ce dole kowane dalibi ya dauki darussan kimiyyar sinadari da kere-kere (Physics and Chemistry) a ajinsa na hudu a sakandare sa’ar da nake makaranta, ban taba karantar wadannan fannoni ba sai bayan shekaru kusan goma. Amma a hakan, abubuwan da nake rubutawa a wannan shafi ya yi tasiri ga daliban da ke karantar wannan fanni ba wai a sakandare kadai ba, hatta ga wadanda ke matakin jami’a. Kai, hatta wadanda ke karantar digiri na uku sun amfana da rubuce-rubucen da wannan shafi ke bugawa a duk mako.
Don haka, ina kara godiya ga Allah sannan ga hukumar Kamfanin Media Trust da suke daukar nauyin buga wadannan rubuce-rubuce tun shekarar 2006. Allah Ya saka wa kowa da alheri, amin. Na gode.
Assalamu alaikum Baban Sadik, ina so a yi mini cikakken bayani kan gaske ne na’urar “Power Bank” tana kashe batirin waya? Daga Abdul Gwangwan.
Wa alaikumus salam Malam Abdul Gwangwan. Na’urar “Power Bank” dai na’ura ce da ke taimakawa wajen cajin batirin wayar salula lokacin da mutum ke nesa da na’urar cajinsa ko aka dauke wutar lantarki. Wannan na’ura tana dauke da bangarori uku ne. Bangaren farko shi ne asalin gangar-jiki da ke dauke da kayan da ke ciki. Bangare na biyu kuma kwayar batirin da ke bayar da makamashin caji, wato: “Battery Cell” ke nan. Sai bangare na uku, wato allon da ke dauke da batirin da sauran hanyoyin da makamashin lantarki ke bi don isa ga batirin wayar. Wannan allo shi ake kira “Printed Circuit Board” ko “PCB” a gajarce. Shi ne bangare mafi muhimmanci a jikin na’urar “Power Bank.” Kusan galibin na’urorin sadarwa na lantarki na zamani suna amfani da wannan allo. Idan ka bude za ka gan shi a kwance, sauran kayayyaki na kansa. Yana da zane-zane da ramuka kanana, inda wayoyi ke kutsawa ciki. Wannan shi ne “Printed Circuit Board” ko “PCB” a gajarce.
Wannan na’ura ta “Power Bank” dai na da matakan caji guda uku ne, da zarar ka jona ta da wayarka don yin caji. A matakin farko na’urar na bulluko makamashin lantarki ne cikin gaggawa don ingiza kaso mafi yawa na caji zuwa cikin batirin wayarka. Wannan mataki shi ake kira “Rapid Charging Stage.” Sai matakin caji na biyu, wanda ke ci gaba da aika makamashin lantarki a-kai-a-kai, amma ba da gaggawa irin yanayin mataki na farko ba. Wannan mataki shi ake kira: “Continuous Charging Stage.” Sai mataki na uku kuma na karshe, wanda ke aika makamashin caji kadan-kadan, don cika batirin wayar, tare da karfafa sinadaran cajin da ke cikin batirin wayarka, don daukar lokaci mai tsawo kafin cajin ya fara sauka. Wannan mataki shi ake kira: “Trickle Charging State.” Idan aka yi kuskuren zare waya daga jikin wannan na’ura ko jikin makamashin lantarki yayin da take wannan mataki na caji, to, cajin bazai dade ba zai kare.
Tambayarka na son sanin ko wannan na’ura tana lalata ko kashe batirin wayar salula ne idan aka lazimci caji da ita? Amsar ita ce, ya danganta. Shi amfani da na’urar “Power Bank” wajen cajin waya yana da ka’idoji. Na farko shi ne, ya zama mizanin batirin wayarka kasa yake da mizanin batirin “Power Bank”, ko daidai da shi. Abin da wannan ke nufi shi ne; kowane batir na da mizani. Misali, idan mizanin batirin wayarka 2,500 mAh ne, to, ya zama mizanin “Power Bank” dinka ya dara shi – ya zama kamar 3,000 mAh ne. Amma idan mizanin batirin wayarka ya fi na na’urar “Power Bank”, to, ba zai iya cajin wayarka ba daga 0- 100% ba.
Na biyu, ya zama karfin sinadarin batirin wayarka (Boltage) ya dara na na’urar “Power Bank.” Misali, idan karfin sinadarin batirin wayarka boltej biyar ne (5B), na na’urar “Power Bank” kuma hudu da rabi (4.5B), nan ma za a samu matsala. Dole na na’urar “Power Bank” ta dara na wayarka. Amma idan na wayarka ne ya dara na “Power Bank”, to duk sa’ar da ka jona wayarka maimakon na’urar “Power Bank” ta caja maka batirin, sai ya zama raguwa cajin da ke batirin wayarka ne zai rika komawa jikin na “Power Bank” din. Ma’ana, karfin sinadarin batirin wayarka ya gaza ke nan. Sai ka’ida ta karshe, shi ne ka samu na’urar “Power Bank” mai inganci, na asali, gangariya daga kamfani sananne. Idan ya zama bangaren PCB dinta jabu ne, to duk saa’r da ka tashi caji za ka ji wayarka ta dauki zafi, kamar za ta kone. Idan ka ga haka, to, hanya mafi sauki kawai ka zare wayarka, in ba haka ba tana iya bindiga ta kone, ko ta babbake muddin hakan ya ci gaba. Kuma alamar cewa lallai sinadaran batirin wayarka sun gaza na na’urar “Power Bank” din da kake caji da ita ke nan.
Daga bayanan da suka gabata zai bayyana maka cewa lallai muddin ba a bi ka’idar cajin waya da na’urar “Power Bank” ba, to, a karshe hakan zai iya sabbaba matsi ga batirin har ma wayar. Da fatan ka gamsu. Na gode.