Amsoshin sakonnin masu karatu (03)

Assalaamu alaikum, da fatan Allah Ya sa Malam Baban Sadik yana lafiya.  Don Allah ina so a taimaka a sanar da ni yadda ake shiga tsarin nan da ke ba da damar mu’amala da fasahar Intanet na tsawon wata guda a Naira dubu daya kacal, a wayar Tecno D5, Android.  Kuma, ita ma wannan wayar […]

Amsoshin sakonnin masu karatu (03)

Assalaamu alaikum, da fatan Allah Ya sa Malam Baban Sadik yana lafiya.  Don Allah ina so a taimaka a sanar da ni yadda ake shiga tsarin nan da ke ba da damar mu’amala da fasahar Intanet na tsawon wata guda a Naira dubu daya kacal, a wayar Tecno D5, Android.  Kuma, ita ma wannan wayar ana sa mata wasu “Settings” ne don yin mu’amala da fasahar Intanet?  Na gode, Allah Ya kara budi da basira da taimako a kan dukkan lamarinka, amin.  Daga: Babani A. Garba, Malam-madori, Jigawa.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Babani.  Ban san da wani kamfanin waya kake son yin amfani da shi ba.  Kowane kamfanin waya na da nasa tsarin.  Don haka kana iya tuntubar kamfanin wayar da kake amfani da layinsa, ko kake son yin amfani da layinsa.  Ko kuma ka tambaya abokanka ko kwararru a harkar waya a inda kake, za su taimaka maka wajen ba ka bayanai masu gamsarwa.  Sai dai kuma, sabanin yadda kake tunani, shi wannan tsari ba wai daga farkon wata zuwa karshe za a ba ka damar mu’amala da Intanet kai tsaye babu kakkautawa ba.  Ya danganci yadda kake mu’amala da shi.  Za su ba ka bayanai ne (Data) wadanda za su zama mizani a gare ka duk sadda kake shiga Intanet.  Idan har ka cinye wadannan bayanai naka kafin wata ya kare, shi ke nan, ba za ka iya mu’amala da fasahar Intanet ba. In kana da kudi a katin wayarka, nan take za su fara jan kudin kai-tsaye.  Amma idan ba ka cinye wadannan bayanai ba, kana iya mu’amala da Intanet har na tsawon wata guda.  Idan wata ya kare ba ka cinye ba, sai a sandarar da su, har sai ka sake sa kudi ka sayi wasu bayanan, sai a hada maka da na baya.  Da fatan ka fahimci wannan tsari daga wannan dan gajeren bayani.

Assalaamu alaikum, Allah Ya kara maka daukaka, amin.  Tun shekara biyu ke nan ina neman adireshinka, sai yanzu Allah Ya sa na samu.  Allah Ya kara maka fasaha amin.  Yaya ake yin rajista ne da Yahoo!?  Daga: 07065102625
Wa alaikumus salaam, ina godiya matuka da wannan yunkuri mai kyau.  Allah saka da alheri da wadannan addu’o’i, Ya kuma kara dankon kauna a tsakaninmu.  Dangane da tambaya kan rajista a shafin Yahoo!.  Idan kana iya mu’amala da fasahar Intanet a waya ko kwamfutarka, ka shiga wannan shafi www.yahoo.com daga can sama ta bangaren dama za ka ga inda aka rubuta “Sign Up for Yahoo! Mail,” sai ka matsa.  Kana shiga wajen za a budo maka fom da za ka cika, ka zabi sunan (username) da kake bukata, tare da kalmar shiga (password).  Samun wannan akwatin Imel ne zai ba ka damar shiga dukkan shafukan gidan yanar sadarwa na Yahoo!  Da fatan ka gamsu.  

Assalaamu alaikum, Baban Sadik don Allah a aiko mini da kasidar nan ta “Tsibirin Bamuda” zuwa adireshin Imel dina da ke: [email protected]. Daga: 08093476575
Wa alaikumus salam, Malam AbdurRahman, sai ka duba akwatin Imel dinka, tuni na cillo maka kasidar. Allah sa a amfana da abin da ke ciki, amin.  Na gode.

Salaamun alaikum, da fatan Baban Sadik yana lafiya tare da daukacin ’yan makaranta.  Tambayata ita ce: don Allah meye ma’anar wannan kalma ko haruffa ke nufi: ‘.ng’ wacce take zuwa a kashen sunan layin adireshi kamar ‘www.glo.com.ng’.  Allah Ya ba ka ikon amsawa, amin.  Daga: Rahinat, Kano.
Wa alaikumus salam.  Wannan harafi ko haruffa da ake gani, wato ‘.ng’ ana kiransa “Top Lebel Domain Name.”  bangaren karshe ne na adireshin gidan yanar sadarwa, wanda ke da rajista da asali a Najeriya.  Lafazin ‘ng’ na nufin ‘Nigeria’ ne.  Na kasar Amurka shi ne ‘gob’.  Na kasar Ingila kuma ‘.co.uk’.  Na kasar Kanada kuma ‘.ca’.  Na kasar Afirka ta Kudu kuma ‘.za’.  Kowace kasa a duniya tana da nata wanda ya kebance ta.  Da fatan an gamsu.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki kuma yaya fama da jama’a?  Allah dai Ya saka maka da alheri, amin.  Wai don Allah ko akwai wata na’ura da za ta iya taskance magana ta mayar da ita rubutu?  Ina nufin idan ana wani bayani ko hira, sai ya rika zama rubutu.  Daga: Muhammad Musa, Bachirawa K/Ungogo Fasaha Communication Center.
Wa alaikumus salam. Lallai akwai masarrafa ko manhaja ko na’ura wacce ake jonawa da kwamfuta, don mayar da bayanan sauti ko na bidiyo, zuwa rubutattun bayanai.  Na’urar da ke wannan aiki ana kiranta da suna “Transcription Machine.”  Manhaja ko masarrafar kwamfuta mai wannan aiki kuma sunanta: “Transcription Software.”  Wannan tsari yana da muhimmanci matuka, kuma da shi ne galibin lokuta ake amfani wajen mayar da galibin tarurruka da majalisin ilimi na manyan malaman duniya a yau, zuwa rubutattun littattafai.  Da zarar an shigar wa kwamfuta wannan masarrafa, sai a budo jakar bayanin da ke dauke da wannan bayani, ita kuma nan take kawai sai ta kama rubuce jawaban sautin ko bidiyo.  Daga magana, zuwa gyaran murya, zuwa tari, duk sai ta rubuce.  Daga baya sai a bi su daya bayan daya, a gyara abubuwan da ta rubuce. Wanda ake bukata a bar shi, wanda kuma ba a bukata sai a cire.  Da fatan ka gamsu.

Assalaamu alaikum. Allah Ya taimaki Baban Sadik, amin.  Tambayata ita ce: na ga idan ina hirar ga-ni-ga-ka na facebook (Facebook Chat), sai na ga wani koren digo a gefen sunayen abokaina, wasu kuma in ga alamar wayar salula.  Me wannan ke nufi ne?  Daga: Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Gidan mai mangwaro.  
Wa alaikumus salam Malam Yahuza.  Duk wanda ka ga alamar kore a kusa da sunansa, to alamar ya hau manhajar facebook kai tsaye ke nan.  Don haka kana iya tuntubarsa ku yi hira, in har ba a shagale yake ba.  Haka duk wanda ka ga alamar wayar salula a kusa da sunansa, shi ma yana nan kai tsaye.  Sai dai ya dakile tsarin da ke nuna waccan alama ne don kada jama’a su dame shi.  Ko kuma bai ma san tsarin a kashe yake ba.  Da fatan ka gamsu.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina da wayar nau’in Blackberry, wai dole ne sai na sayi layi kafin in rika saukar da abubuwa daga Intanet (Downloads) da shiga Facebook?  Domin idan na zo shiga yanzu sai a ce mini: “Set up your wi-fi.”  Na gode. Daga: Usman Mu’azu Funtua, Katsina.
Wa alaikumus salam, Malam Mu’azu, muddin kana da kudi a wayar, ya kamata a ce kana iya mu’amala da fasahar Intanet ko da ba ka sayi layin wata ba (Subscription) daga kamfanin waya.  Amma sai dai kudin da ke katin waya ne za su rika zaftarewa babu kakkautawa.  Ta yiwu shi ya sa ba ka iya saukar da wani abu, tunda hakan na bukatar kudi mai yawa a wayarka, ko kuma kana da tsarin mu’amala da fasahar Intanet tsakaninka da kamfanin waya.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.