Amsoshin sakonnin masu karatu (04)

A yau ga kashi na karshe na sakonnin masu karatu.  A mako mai zuwa, in Allah Ya so, za mu ci gaba da bayani kan samuwar mafarki a mahangar binciken malaman kimiyya na zamani.  A ci gaba da kasancewa tare da mu: Assalamu alaikum, Malam yaya ake hada kwamfuta da kwamfuta a zangon sadarwa (network).  […]

Amsoshin sakonnin masu karatu (04)
Amsoshin sakonnin masu karatu (04)

A yau ga kashi na karshe na sakonnin masu karatu.  A mako mai zuwa, in Allah Ya so, za mu ci gaba da bayani kan samuwar mafarki a mahangar binciken malaman kimiyya na zamani.  A ci gaba da kasancewa tare da mu:

Assalamu alaikum, Malam yaya ake hada kwamfuta da kwamfuta a zangon sadarwa (network).  Daga Zayyanu Yarima, Abuja.
Wa alaikumus salam. Wannan tambaya ce mai girma, wacce ke bukatar darasi mai zaman kansa, kamar yadda na yi a baya.  Hada kwamfutoci don su aiwatar da sadarwa a tsakaninsu a Gajeren Zangon Sadarwa (Local Area Network) abu ne da ke bukatar abubuwa da dama.  Wannan tsari shi ake kira “Networking” a fannin ilimin kwamfuta da sadarwar zamani.  Mafi karancin adadin kwamfutocin da ake bukata dai daga biyu ne, sannan ana bukatar na’urorin aiwatar da sadarwa tsakanin kwamfutoci, irin su “Router,” da “Switches,” da “Network Hubs,” sai kayayyakin aiki irin su wayoyin kebul nau’in “RJ45”, da na’urar gwajin lafiya da ingancin kebul, wato “Cable Tester,” da dai sauran kayayyaki.  Idan ba a bukatar kwamfutocin su jonu da Intanet, to a nan ba a bukatar na’urar “Router.”  
Bayan an tanadi wadannan kayayyaki, sai a yi nazarin irin tsarin da ake so, wato “Netowork Topology.”  Daga nan sai a jojjona kwamfutocin ta amfani da wadancan kayayyaki da bayaninsu ya gabata.  Idan aka gama jojjona su a fili, sai a shiga masarrafar kwamfutar da ke kowace kwamfuta, a hada alaka a tsakaninsu ta yadda za a iya karbar bayanai daga kowace, a kuma iya aika wa kowace.  Amma dole ne a samu guda daya wacce ita ce uwar garke; mai dauke da masarrafar musayar bayanai a tsakanin sauran kwamfutocin, wato “Serber” ko “Host”, sauran kuma sun zama “Clients” ke nan.  
Har wa yau, idan masu amfani da kwamfutocin da ke wannan zango sun sha bamban wajen martabar karba da tura bayanai a tsakaninsu, to dole ne kuma a kayyade kowane a ba shi matsayinsa.  Wannan shi ake kira “Pribiledges.”  Za a yi haka ne bayan an samar wa kowane daga cikinsu suna (username) da kalmar sirri (password), wadanda da su ne zai rika amfani wajen shiga zangon daga kowace kwamfuta ce a wurin.  Babbar manhajar kwamfuta ta ‘Windows’ na dauke da manhajar tsara sunaye da kalmomin iznin shigar masu mu’amala da kwamfutar da ke kowane zango mai suna “Actibe Directory.”  Aikin wannan masarrafa ko manhaja shi ne tsara dukkan bayanan da suka shafi kowace kwamfuta da kowane mai mu’amala da kwamfuta da ke zangon, ba tare da matsala ba.  A nan ne za a daidaita matsayin kowanensu, a canza masa kalmar sirri idan yana so, sannan idan ma ana so a goge sunan wani ko wata kwamfuta da ke zangon, duk ta nan za a yi.  
Wannan a takaicen takaitawa ke nan.  Sauran bayanai kuma ka nemi kasidar da na rubuta a wannan shafi cikin shekarar 2010 mai take: “Tsarin Sadarwa a Tsakanin Kwamfutoci” don karin bayani.  Ko kana iya turo adireshin Imel dinka, sai in ingizo maka kasidar.  Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum, ina so Malam ya yi mini bayani a kan ‘Hotspot’ da ke zuwa a wayoyin zamani.  Daga: Muhammad Abubakar Damaturu, Yobe
Wa alaikumus salam. Kalmar “Hotspot” na ishara ne ga wani takaitaccen “hurumin sadarwa ta Intanet a tsarin wayar iska” da wata wayar salula ke iya bayarwa don wata wayar salula ’yar uwarta ta yi amfani da shi don mu’amala da fasahar Intanet.  Wannan hurumi na samuwa ne a galibin wayoyin salula na zamani; daga wayoyi nau’in Blackberry zuwa ‘Windows Phone’ da ‘Android’, duk sukan zo da masarrafar da ke samar da wannan hurumi.  Kafin wata wayar salula ta iya amfani da wannan hurumi da ke wata wayar salular, dole ne ya zama wayar da ke dauke da hurumin na da tsarin sadarwa ta Intanet, wato “Data Bundle” ko kuma “Data Subscription” idan wayar Blackberry ce.  Har wa yau, samun hurumi na iya yiwuwa idan wayar na jone da tsarin sadarwar wayar iska na wani kamfani, wato “Wi-Fi” ko “Wireless LAN Network.”  
Abu na biyu kuma, sai an kunna ko zaburar (Actibate) da wannan tsari a jikin wayar da ke dauke da shi.  Sannan dole ne ya zama wayar da za ta jonu da wannan hurumi ta mallaki tsarin mu’amala da Intanet ta wayar iska, wato “Wi-Fi,” sannan kuma dole ne mai wayar ya kunna, don neman wani hurumin sadarwa da ke kusa da shi.  Muddin hurumin a kunne yake da zarar ya nemo (Search) zai ga hurumin ta amfani da sunan wayar da ke dauke da shi.  Daga nan sai ya matsa sunan wayar, waccan wayar za ta sanar da mai wayar cewa: “Wance (sunan waya) na neman shiga huruminki na sadarwar Intanet, a bar ta ta shigo?”  Idan mai wayar ya amince, sai ya zabi tsarin da yake so waccan wayar ta bi wajen amfani da hurumin.  Idan yana son tsari ne tsararre (Secured), dole sai ya rubuta wasu lambobi, sannan ya sanar da mai waccan wayar cewa ga lambobin.  Wayarsa za ta sanar da shi cewa: “Wannan hurumi fa tsararre ne, kana da kalmomin sirrin shiga?”  Idan ya ce eh, sai ya shigar.  Da zarar ya shigar sai kawai wayarsa ta samu tsarin sadarwa na wayar iska don mu’amala da fasahar Intanet.  Wannan, a takaice, shi ne abin da ake kira “Hotspot”. Da fatan ka gamsu.
Salamun Alaikum Baban Sadik, da fatan iyali lafiya.  Don Allah akwai hanyar da zan bi in maido akwatin Imel din Yahoo dina da aka rufe min kusan shekara guda, amma kuma ina amfani da shi a Facebook?  Daga: 08028338892
Wa alaikumus salam, barka dai.  Wanann ke nuna cewa an dakatar da wannan akwatin Imel din naka ke nan, wato “Deactibated,” kuma kana iya dawo da shi ne ta hanyar shiga.  Idan ka bukaci shiga, za a sanar da kai halin da akwatin ke ciki.  Galibin gidajen yanar sadarwa masu dauke da manhajar Imel irin su Yahoo!, da Hotmail, da Gmail, sukan bayar da tazara ta musamman kafin su rufe, kuma za su yi ta aiko maka da sako kan haka.  Idan ka share su shi ke nan, sai su rufe.  Gmail kan bayar da watanni 9 ne kafin su rufe.  Hotmail kan bayar da shekara daya ne. A yayin da Yahoo! kuma ke bayar da tazarar watanni 8.   Idan an rufe, a duk sadda ka bukaci a bude maka suna budewa.  Amma idan tazarar lokaci ya wuce shekara, ko shekaru 2 misali, galibi sukan goge akwatin gaba daya (Delete), sai su saki sunan (username) ga duk mai bukata, sai a ba shi.  Wannan shi ake kira “Username Recycling,” kamar yadda kamfanonin waya suke yi su ma, ga duk wanda ya daina amfani da layinsa na tsawon lokaci.  
Duk da cewa an kulle akwatin naka, wannan bai hana ka iya amfani da shi wajen shiga shafinka na Facebook, amma na san ka bude shafin Facebook dinka ne tun kafin a rufe wancan akwatin Imel din naka.  Idan kana son ci gaba da amfani da shi kana iya gyara shi, domin a duk sadda shafinka na Facebook ya samu matsala, kuma kana son ka warware, to, can za su tura maka sakon Imel don gyara matsalar.  Ka ga idan kuma an rufe, sakon ba inda zai je, kuma wannan ke nuna matsalar ba za ta warwaru ba ke nan.  Don haka, ko dai ka cire adireshin wannan Imel a shafinka na Facebook ka sa lambar wayarka ko wani sabon adireshin Imel, ko kuma ka gyara wancan da aka kulle.  Allah sa a dace, amin.
Assalamu alaikum. Ina son karin bayani a kan nau’ukan kwamfutoci na musamman, wato “Specialised Computer Systems.”  Daga: Fahad Musa, Sokoto
Wa alaikumus salam, Malam Fahad barka ka dai.  Su “Specialised Computer Systems” dai nau’ukan kwamfutoci ne na musamman da ake kera su don aiwatar da wasu ayyuka na musamman a fagen binciken ilimi, da fagen sararin samaniya, da fagen harkar lafiya, da fagen yada labarai da dai sauransu.  Kwamfutoci ne, amma galibi ba su da siffofin zahiri da muke ganin ire-iren wadannan kwamfutoci da muke amfani da su.  Galibinsu ma gingimayen kwamfutoci ne, wato “Main Frame Computers,” wadanda wasu hukumomi ko kasashe ko kamfanoni ke amfani da su wajen aiwatar da ayyuka na musamman.  Galibin kwamfutocin da kamfanin kera kwamfuta na IBM ke kerawa duk kwamfutoci ne na musamman.  Daga cikinsu akwai jerin kwamfutocin da ya kera masu suna “Blue Gene” da dukkan nau’ukansu.  Sannan akwai nau’in kwamfuta ta musamman da kasar Sin ta kera cikin shekarar da ta gabata (2013) mai suna “TIANHE-2”, wacce ke dauke da mizanin ma’adana (Storage) mai girman Perabyte 12 (wato Terabyte 12,000), da na’urar “Processor” sama da miliyan daya, sannan a kalla tana bukatar makamashin lantarki da ya kai Kilowat dubu goma sha bakwai (17,000Kw).  A takaice dai farashin wannan kwamfuta ya kai Dalar Amurka miliyan 380, kwatankwacin Naira biliya sittin da shida da miliyan dari uku (N66.3B) ke nan.  Wannan duk kudin kwamfuta guda daya ne, kuma gari guda ne, ba kwamfuta ce da za ka sayo ka dauko a jaka ba.   A duk duniya ita ce kwamfutar da ta fi tsada a halin yanzu.  Da fatan ka gamsu.
Salaamun alaikum, Malam yaya mutum zai yi domin ya kiyaye daga kamuwa da kwayar cutar kwamfuta (birus)?  Daga:  Muhammad Rimaye, Kaduna
Wa alaikumus salam. Abin da ake bukata shi ne, ka sanya mata masarrafar tace kwayoyin cutar kwamfuta, wato “Anti-birus Software,” ka zama mai kiyayewa wajen amfani da ma’adanar shigar da bayanai (irin su Flash Dribe dsr). Bayan haka, idan kai mai yawan mu’amala da fasahar Intanet ne a kwamfutar, ka zama mai kaffa-kaffa wajen wuraren da kake shiga.  Kada ka rika bude makalutun sakon Imel (Email Attachment) sai ka san daga wajen wa sakon ya zo kuma ka amintu da shi.  In da hali, a duk wata ka rika tace bayanan da ke kwamfutar ta amfani da wannan masarrafa, wato “On Deman Scan” ke nan.  Da fatan ka gamsu.
Assalamu alaikum Malam, don Allah me ke sawa a gajeren zangon sadarwa na kwamfuta, wasu kwamfutocin na iya hawa Intanet, amma wasu ba su iya hawa?  Meye dalilin hakan?  Daga: 08036823562
Wa alaikumus salam. Wannan na iya faruwa sanadiyyar cirewar wayar kebul da ke like da kwamfutar, ko cirewar wayar kebul da ke like da na’urar ‘Router’ da ke sadar da zangon da giza-gizan sadarwa ta Intanet, ko kuma daukewar yanayin sadarwa gaba daya daga kamfanin da ke sadarwa da zangon da Intanet, wato “Serbice Probider” ke nan.  Idan dukkan wadannan lafiya lau suke, ana iya duba kwamfutar da  ba ta iya hawa Intanet a gani, watakila matsalar daga kwamfutar ce, ko da kuwa wayar kebul din na makale a jikinta.  Uban zangon sadarwa (Network Administrator), shi ne kadai zai iya yin hukuncin karshe kan matsalar.  Da fatan an gamsu.
Allah gafarta Malam, wai da gaske ne idan aka dora ‘laptop’ a kan cinya hakan kan haddasa wata cuta? Daga: 07031648855
A gaskiya ban sani ba.  Na sha samun tambayoyi makantan wannan, kuma a iyakar bincikena, ban taba cin karo da wasu bayanai masu alakanta hakan da kwamfuta ba kai tsaye daga kwararru kan harkar lafiya da kwamfuta.  Ire-iren wadannan bayanai, galibinsu, jita-jita ne, ciki har da wanda ke cewa yawan amfani da wayar salula na haddasa cutar sankara (Cancer).  Har yanzu babu wani bincike na musamman, abin dogaro a wajen kwararru kan ingancin wannan ikirari.  Da fatan ka gamsu.