Amsoshin sakonnin masu karatu (1A)

Kamar yadda aka saba lokaci zuwa lokaci, ga wasu daga cikin sakonninku nan.  Wannan kashin farko ne, a mako mai zuwa, in Allah Ya so, zan turo kashi na biyu.  Don Allah a rika turo sakonni masu ma’ana, kuma a rika rubuto wuri da sunan mai aikowa.  Allah Ya sa mu dace, amin. Malam meye […]

Amsoshin sakonnin masu karatu (1A)

Kamar yadda aka saba lokaci zuwa lokaci, ga wasu daga cikin sakonninku nan.  Wannan kashin farko ne, a mako mai zuwa, in Allah Ya so, zan turo kashi na biyu.  Don Allah a rika turo sakonni masu ma’ana, kuma a rika rubuto wuri da sunan mai aikowa.  Allah Ya sa mu dace, amin.

Malam meye ingancin kwamfuta nau’in HP da DELL wajen rike caji?  Daga: 08073188022
A gaskiya ya danganci abubuwan da kwamfuta ke dauke da su na masarrafai da tsarin babbar manhajar da ke dauke a cikinta.  Amma la’akari da kamfanin da ya kera kwamfuta don gano ingancin batir, ba abu ba ne da zai bayar da kyakkyawan sakamako.  Abin nufi, idan ana son gano karkon batir din kowace kwamfuta, ba a la’akari da kamfanin da ya kera kwamfutar, sai dai a yi la’akari da nau’in babbar manhajar da ke kwamfuta, da yawan masarrafai ko manhajojin da take dauke da su.  Wani abin lura bayan wadannan kuma shi ne tsawon rayuwar batir din tun sadda aka kera shi. Idan babbar manhajar da ke dauke cikin kwamfutar tana da nauyi, sanadiyyar daruruwan manhajoji da masarrafan da ke taimaka mata wajen aiwatar da ayyukanta, wannan na nufin kwamfutar za ta rika zukar makamashi sosai.  Haka idan akwai wasu abubuwa da aka makala mata don sadar da bayanai, kamar ma’adanar filash da faifain CD/DbD da makalutun sadarwa na Intanet (Internet Modem); duk wadannan na jan makamashi, musamman idan kwamfutar ba a jone take da wutar lantarki ba.  Amma la’akari da kamfanin da ya kera kwamfuta kadai ba ya nuna ga batir din ya fi karko.
Idan kana son batirinka ya yi karko, ka rage yawan mu’amala da wasannin kwamfuta (computer games).  Ka cire duk wata na’ura da ka makala wa kwamfutar da zarar ka gama amfani da ita.  Ka rage mizanin sautinta (system bolume).  Idan akwai CD ko DbD  a cikin ma’adanar CD ROM dinka, ka rika cire shi da zarar ka gama amfani da shi.  In so samu ne, da zarar ka sa CD ko DbD mai dauke da sauti ko bidiyo, ka kwafe shi zuwa babbar ma’adanar kwamfutar kawai, don rage mata mizanin makamashi da za ta rika zuka.  Sannan ka rage kaifin hasken shafin kwamfutar (Screen Brightness).  Sannan ka bi duk inda wata masarrafa mai gudanuwa ta karkashin kasa (Background tasks) take aiki, wacce ba ka bukatarta, ka dankwafe ta.  Wadannan, kadan ne daga cikin abubuwan da mai kwamfuta zai yi don rage yawan makamashin da kwamfutar take zuka idan ya zare ta daga kan wutar lantarkai kai tsaye.  Da fatan ka gamsu.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, don Allah wai yaya Facebook suke hada mutum da dan uwansa ko wani wanda ya sani (People you may know)?  Abin yana ba ni mamaki, sai in ga hoton wanda na sani an kawo, ko ma dan uwana na jini; duk da ba ni na nema ba.  Ya abin yake ne?  Daga: Usman Mu’azu Funtuwa, Katsina.
Wa alaikumus salam Malam Usman, barka dai.  Wannan abin da kake gani kuma yake ba ka mamaki ba maita ba ce, ba kuma sihiri ba ne; kintsi ne irin na manhajar kwamfuta ta musamman da hukumar Facebook ke amfani da ita wajen hada alaka tsakaninka da wadanda ka sani ko ka san wadanda suka sansu, ta la’akari da nau’ukan bayanan da ka shigar a shafinka sadda kake bude shafin ko bayan ka bude.  Kada ka mance, a sadda kake bude shafin ka bayar da sunanka, da gari ko wurin da aka haife ka, da jiharka, da kasarka, da addininka, da ra’ayoyinka na siyasa ko addini watakila, sannan ka fadi sunan makarantun da ka yi a baya ko kake kan yi, da wuraren da ka yi aiki a baya ko kake kan yi; wadannan bayanan ne suke amfani da su wajen nemo wadanda bayanansu suka dace da naka, don hada alaka a tsakaninku.  Domin, in har bayanan da kuka bayar  (kai da su) a sadda kuke bude shafinku, sun zo daidai, to babu yadda za a yi a kasa samun alakar sanayya a tsakaninku.  
Wannan shi ne abin da suke yi.  Amma cikakken bayani kan yadda hakan ke faruwa ba abu ba ne mai sauki.  Akwai sarkakkiya sosai cikin lamarin.  A takaice ma dai, a duniyar Intanet ta zamanin yau, samun shafi mai dauke da cunkoson manhajoji, da sarkakkiya ta kwarewa (professional sophistication), ba irin shafin Facebook.  Abin sai wanda ya kware a fannin kimiyyar sadarwa ta zamani zai iya fahimtarsa cikin sauki.  A takaice wannan shi ne abin da hukumar Facebook ke yi wajen bijiro maka da wadannan mutane da kake ganin ka sansu, amma ba ka bukaci a bijiro maka su ba, watakila ma ba ka tunanin ganinsu a shafin.  Da fatan ka gane.

Assalamu alaikum Baban Sadik, tambayata a kan Google ne; shin, ta yaya aka samar da shi, kuma yaya yake ajiye bayanai a cikin kwamfutocinsa, sannan kuma shin, ko akwai hukuma mai kula da wannan shafi?  Daga: Nasiru Dauran, Talata Mafara, Zamfara
Wa alaikumus salam, Malam Nasir barka ka dai.  Shafin Google, ko Manhajar Google, ko Kamfanin Google, duk abu abubuwa ne da suka dunkule zuwa abu daya.  Idan ka ce “Google”, to, hakan na ishara ne zuwa ga dukkan ukun nan, ko biyunsu, ko kuma daya daga cikinsu.  Asali manhaja ce ta zakulo bayanai da wasu samari su biyu suka gina, tun cikin shekarar 2005.  A sannan suna karatunsu na digiri na uku a Jami’ar Stanford da ke Amurka.  Wadannan samari su ne: Larry Page da Sergey Brin.  Sannan shekarunsu duk ba su shige 25 ba a duniya.
Samar da wannan manhaja ta neman bayanai ce ta haddasa kafa kamfani, da gidan yanar sadarwa mai dauke da manhajar, don taimaka wa masu neman bayanai don bincike ko gamsarwa ta ilimi, samun bayanai ba tare da wata matsala ba. Wannan gidan yanar sadarwa na Google (www.google.com) yana dauke ne da wata manhaja mai suna “Google Crowler,” wacce ke yawo a giza-gizan sadarwa ta duniya (World Wide Web) don debo bayanai, ta amfani da rariyar likau (Web Links), tana zuba wadannan bayanai a kwamfutocin kamfanin, a tsarin ABCD…dYZ.  Wannan tsarin adana bayanai shi ake kira “Indeding” a harshen kimiyyar sadarwar zamani.  Da zarar ka shiga gidan yanar sadarwar ka shigar da kalma, nan take sai wannan manhaja ta zakulo maka dukkan bayanai masu alaka da wannan kalma da ka shigar, ta zuba maka su a gabanka; zabi wanda kake so.  Idan ka latsa nau’in bayanin da kake son isa gare su, sai a cilla ka asalin gidan yanar sadarwar da ke dauke da bayanan kai tsaye, ka duba da kanka.
A hakikanin gaskiya babu wata hukuma da ke lura da wannan gidan yanar sadarwa domin na kamfani ne ba na hukuma ba.  Wannan kamfani na Google na kasar Amurka ne, duk da cewa yana da rassa a kusan dukkan nahiyoyin duniya. Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah wace hanya zan bi wajen bude akwatin Imel?  Daga: Baban-Yaya dan Employer, Kwanar-dangora.
Wa alaikumus salam, barka dai.  Bude akwatin Imel abu ne mai sauki.  Sai dai in ba wayar salula mai dauke da babbar manhajar Android kake amfani da ita, sai dai ka yi amfani da kwamfuta wajen yin hakan. Ka shiga wannan gidan yanar sadarwa idan na Gmail kake so: http://mail.google.com sai ka gangara kasa inda aka rubuta “Create An Account,” ka matsa, za a kai ka inda za ka cike fom ta hanyar shigar da dukkan bayanan da ake bukata daga gare ka kafin ka bude. A ciki za a bukaci ka zabi suna (username) da kalmar iznin shiga (password), da dai sauran bayanai.  Idan kuma Yahoo kake so, ka shiga nan: http://mail.yahoo.com, duk tsarin iri daya ne.  Idan wayarka ba Android ba ce, kana iya shigar da wancan adireshi na Google, amma za su bukaci ka shigar da lambar wayarka ne, sai su turo maka shafin da ke dauke da fom da za ka cike.  Da fatan ka gamsu.

Assalaamu alaikum, don Allah ina son a yi mini bayanin yadda zan adana sakon wayata cikin katin ma’adanar waya (Memory Card).  Saboda na ji ka yi bayani a jaridar AMINIYA, kuma ni lokacin da aka yi bayanin ba ni da ita.  Daga Almajirinka: Kabiru Ridwan Sokoto.
Wa alaikumus salam, wannan ba wani abu ba ne mai wahala.  Na farko ka sanya katin ma’adanar wayar a cikin waya, sannan ka je manhajar sakonni (Messages), ka shiga “Options” wato bangaren zabe-zabe ke nan.  Za ka gan shi a bangaren hagu ko dama; ya danganci nau’in wayarka.  A jerin bayanan da ke “Opetions” za ka ga inda aka rubuta “Mark All,”  sai ka matsa.  Hakan zai sanya wa dukkan sakonnin da ke ciki alamar “maki” (wato check mark).  Da zarar an sa musu alamar maki, sai ka sake zuwa “Options” har wa yau, ka latsa.  Daga cikin jerin zabin da ke wurin za ka “Mobe to Memory Card” ko wani abu makamancin haka.  Sai kawai ka zaba, za a kwafe su duka a kai maka su cikin katin ma’adanar wayar ba bata lokaci.  Sannan kana iya kwafe su ma zuwa katin SIM dinka, duk ta wannan hanya, muddin lambobinka ba su cike ma’adanar SIM din ba.

Idan kuma wayar Nokia ce, kana iya saukar da manhajar “Nokia PC” sai ka jona wayar da kwamfutarka, sai ka bi tsare-tsaren da ke ciki, za a ba ka damar kwashe duk abin da ke cikin wayarka zuwa kwamfutarka.  Wannan ma shi ne ya fi sauki.   Da fatan ka gamsu.
Assalamu Alaikum Malam: mene ne bambancin waya nau’in Android da Windows Phone?  Daga: 08052380474
Wa alaikumus salam.  A gaskiya wannan tambaya ta sha maimaituwa a wannan shafi, don haka idan kana bukatar amsa gamsassa, kana iya zuwa shafina da ke Facebook mai suna “Dandalin Kimiyya da Fasahar Sadarwa,” (www.facebook.com/kimiyyadafasaharsadarwa)  za ka ga amsar da na bayar a baya.  Amsa ce mai gamsarwa, domin ta kai shafuka kusan uku.  Wannan zai fi sauki da a ce in sake ba ka amsa a nan.  Da fatan za a yi hakuri!