Amsoshin sakonnin masu karatu (3)
A yau ma ga mu dauke da kashi na uku na sakonninku. Zuwa makon gobe, in Allah Ya yarda, za mu karkare da sakonnin wannan zango, daga nan mu ci gaba da wasu fannonin ilimi, kamar yadda muka saba. Assalaamu alaikum, Don Allah Baban Sadik a min bayani; a Intanet idan na zo saukar da […]
A yau ma ga mu dauke da kashi na uku na sakonninku. Zuwa makon gobe, in Allah Ya yarda, za mu karkare da sakonnin wannan zango, daga nan mu ci gaba da wasu fannonin ilimi, kamar yadda muka saba.
Assalaamu alaikum, Don Allah Baban Sadik a min bayani; a Intanet idan na zo saukar da wani bayani, sai in ga manhajojin sun sha bamban, kamar haka, wani: “jar,” wani “jad,” wani “ede,” wani kuma “pdf.” Mece ce ma’anarsu? – Mu’azzam Suleiman, Kano: 08179705299
Wa alaikumus salaam, Malam Mu’azzam, ai wadannan ramzozi ko sunaye da kake gani, sunaye ne da ke ishara zuwa ga nau’ukan jakunkunan bayanai (File Types) da kwamfuta ko wayar salula ke iya mu’amala da su wajen budewa ko karbarsu, idan manhajoji ne ko masarrafai. Idan ka ga “.jar” da “.jad”, to wadannan nau’ukan jakunkunan bayanai ne masu dauke da dafaffiyar manhajar wayar salula (Mobile Phone Application), wanda idan ka saukar, za ka iya loda wa wayar salularka, iya gwargwadon yadda za ta iya dauka, idan yanayinta ya dace da tsarin manhajar. Manhaja mai wannan ramzi, an gina ta ne da dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming Language) na Jaba. Idan kuma ka ga jakar bayanai ta kare da “.ede”, to wannan kuma dafaffiyar manhajar kwamfuta ce, wato: “System Application.” Ita wannan manhaja da sunanta ke karewa da wannan ramzi, a kwamfuta kadai ake iya loda ta, don amfanuwa da abin da ta kunsa. Ramzin “.ede” na nufin “Edecutable” ke nan. Idan kuma ka ga “.pdf” nau’in jakar bayanai ne mai dauke da tsagwaron bayanai da aka taskance da manhajar “Portable Document Format,” cikakkar ma’anar ramzin “.pdf” ke nan. Kamfanin “Adobe” ne ke da wannan manhaja. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu alaikum, Allah saka da alheri. Shawarata game da dukkan kasidun da aka gabatar a baya tsawon shekaru shida shi ne, a tara su a mayar da su littafi a sayar, kuma a dora a Intanet. – Babangida Kano: 08064821597
Wa alaikumus salaam, Malam Babangida, wannan shawara taka abar dubawa ce. Akwai wadanda suka bayar da shawara makamanciyar wannan a shekaru ko lokutan baya. Kamar yadda ka sani, rubuta littafi ba shi ne matsalar ba. Tallata shi da kuma yada shi yadda kowa zai samu, ta hanya mafi inganci da sauki, shi ne babban aikin. Wannan ba karamin lamari ba ne ga wanda bai taba shiga harkar talifi ba, irina. Zan ci gaba dai da tara wadannan kasidu, zuwa wani lokaci mu ga abin da Allah Zai yi. Na gode matuka da wannan shawara.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, me ya sa idan na tura sakon waya sai in ga “Delibered Report”, da wani suna daban ba sunan wanda na tura masa sakon ba? Kuma shin, wannan ke nuna wanda ya sakkon ya je wajensa ya karanta ke nan? Domin wanda na tura masa sakon yakan ce bai gani ba. Shin yaya abin yake ne? – Usman Mu’azu Funtua: 08106067660
Wa alaikumus salaam, Malam Usman, wannan lamari naka da ban mamaki yake. Abin da zan iya cewa shi ne: ta la’akari da ka’idojin sadarwa daga kan kwamfuta har zuwa wayar salula, ta yiwu wanda ka ga sakon ya je wajensa ne ka tura masa. Watakila ka yi kuskure wajen zaben sunan wanda za ka tura masa sadda kake kokarin zakulo sunansa da lambarsa. A ka’ida, duk wanda ka tura masa sako, idan kamfanin waya ya isar da sakon lafiya kalau, dole ya zama da sunansa ko lambarsa za a sanar da kai, ba ka tura wa wani sako, amma kuma a sanar da kai cewa wani aka tura wa. In har wanda ka tura masa ya ce bai ga sakon da ka tura masa ba, to alama ce da ke nuna cewa lallai lambar wani ka zaba ba tashi ba. Sai ka rika lura, ko ka sake dubawa. Allah sa a dace.
Salaamun alaikum Baban Sadik, don Allah ina son karin bayani a kan wayar HTC Windows 7. Na ga ka ambaci manyan wayoyi, amma ba ka ambace ta ba. Ko karamar waya ce? – Mai Kawo: 08050321406
Wa alaikumus salaam. Ai “HTC” sunan kamfanin waya ne, wanda ke kera wayoyi nau’uka daban-daban, masu dauke da babbar manhaja kala-kala. Daga cikin manyan manhajojin da wayoyin HTC ke dauke da su akwai “Windows 7 Mobile”, wanda kake magana. Su kansu wadannan din ba guda daya ba ne, ban san wanda kake nufi ba. A takaice dai, duk wayar salula mai dauke da babbar manhajar “Windows Mobile” ba karamar waya ba ce. A lokacin da nake ambaton nau’ukan manyan wayoyi na kawo misalai ne da guda biyu, ba wai iyakansu ba ke nan. Da fatan ka fahimta.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, wai me ke sa idan na shiga shafin Facebook wani lokaci ina son in yi tsokaci (Comment), amma ban ganin filin yin hakan? – Aliyu Ibrahim Zawiyya, Gusau: 08067784588
Wa alaikumus salaam. Wannan alama ce da ke nuna cewa babu abota a tsakaninku da mai jawabin da kake son yin tsokaci a kai. Domin sai wanda yake abokinka ne kadai za ka iya yin tsokaci kan abin da ya rubuta a Dandalin Facebook. Idan kana bukatar karantawa tare da yin tsokaci kan jawaban jama’a a Facebook, sai ka nemi abota tsakaninka da su. Allah sa a dace.
Assalaamu alaikum maigida barka da warhaka, da fatan ka wuni lafiya, Allah Ya sa haka amin. Don Allah ina son sanin ma’anar wannan alamar # da nake gani a zancen wasu a Dandalin Facebook ko Twitter; meye amfaninta? Na gode. – Ibrahim Muhammad
Wa alaikumus salaam, Malam Ibrahim barka ka dai. Wannan alama ita ce ake kira “Hashtag” a Turancin kimiyyar sadarwar zamani. An fara amfani da ita ne cikin shekarar 2007, kuma amfaninta shi ne takaita hanyar samun bayanai masu alaka da kalma ko jumlar da aka fare ta da wannan alama. Misali, idan ka ga kalma makamanciyar haka: “#BabanSadik” a Twitter ko Facebook ko Google+, hakan na nuna cewa da zarar ka matsa wannan kalma, za a kai ka inda bayanai ko shafuka masu alaka da Baban Sadik ne kai tsaye. Duk kalmar da aka sa mata alamar # a farkonta, takaitacciyar hanya ce da za ta kai duk wanda ya matsa ta ga dukkan bayanan da suke da alaka da kalmar, kamar yadda misali ya gabata a baya. Bayan Dandalin Facebook da Twitter, akwai Dandalin Google+, da Dandalin Instagram, da Dandalin Orkut, da Dandalin FriendFeed, da Dandalin Tout, da Dandalin Pintrest da ma wasu da dama da ke amfani da wannan alama wajen isar da mai ziyara zuwa ga bayanai masu alaka da kalmar da wannan alama ke sarkafe da ita a farkonta. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, ko akwai wani bambanci a tsakanin waya nau’in Blackberry Z10 da kuma Samsung Galady S4, ta wajen abubuwan da suke dauke da su ko wajen amfani da su ko aikewa da sakonni? – Salisu Sama’ila, Zariya: 08056619781
Wa alaikumus salaam, Malam Salisu, lallai akwai bambanci. Domin kamfanonin da suka kera su sun sha bamban, kamar yadda masarrafansu suka sha bamban. Wayar salula nau’in BlackBerry Z10 tana da hanyoyin sadarwa da suka sha bamban da wadanda Samsung Galady take dauke da su. Wayar BlackBerry Z10 na da hanyar sadarwa ta BB Chat, ko BBM, wanda kamar tsarin Intanet yake; wayoyin BlackBerry kadai ke dauke da shi. Ga kuma tsarin gajerun sakonni wato SMS, da dai sauransu. A nata bangaren, Samsung Galady na dauke ne da masarrafai masu fahimtar tsarin fuska da idanun mai mu’amala da ita. Wadannan masarrafai na taimaka wa mai karatu a shafin wayar ne wajen budo shafin da ke tafe, da takaita hasken shafin idan mai karatu ya kawar da fuskarsa, don tanajin makamashin batir. Wadannan kadan ne daga cikin abubuwan da wadannan wayoyi suke dauke da su. Da fatan ka gamsu.
Assalaamu alaikum, yaya ibada? Na ga ka rubuta wayoyin da suka fi shahara, ka ambaci Z10 da Samsung Galady S4, amma ban ji ka ambaci iPod ba, duk da cewa ta fi wadannan tsada. – Usman Mu’azu Funtua
Wa alaikumus salaam, Malam Usman. Ai wadannan da na ambata wayoyin salula ne, amma ita “iPod” ba wayar salula ba ce, na’urar sauraron sauti ce da taskance hotuna daskararru da masu motsi. Sai dai in “iPad” kake nufi. Ita ma ba wayar salula ba ce, na’urar taskance bayanai ce da mu’amala da fasahar Intanet. Wannan shi ne dalilin da ya sa ban ambace ta ba. Da fatan ka gamsu.
Salaamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya. Don Allah wane tsawon lokaci ne batirin wayar salula zai iya dauka yana ajiye bai lalace ba? Sannan kana iya ajiye shi a cikin na’urar caji na tsawon lokaci don ya cika sosai? – Husseini M. Binanchi da Isa Kwafsi Ba Ka Soyayya, Unguwar Magajin Garin Sakkwato: 08087436699
Wa alaikumus salaam, da fatan kuna cikin koshin lafiya. A gaskiya babu wani lokaci na musamman da aka haddade cewa idan batirin wayar salula ya kai a ajiye ba a amfani da shi zai lalace. Abin da na sani dai shi ne, idan aka yi cajin batiri ya cika, ba a yi amfani da shi ba, to a hankali zai sance, saboda sinadaran da ke cikinsa za su yi rauni, har su zagwanye. Bayan haka, abin da aka fi so shi ne, da zarar batir ya cika a caji, a yi maza a cire shi, domin idan har aka dauke wuta yana like da cajin, muddin a kashe wayar salular take, to cajin na iya zukewa. Sai a kiyaye. Da fatan kun gamsu.
Salaamun alaikum, ina da waya nau’in Sony Ericsson W800i mai dauke da babban katin ma’adanar waya mai fadi (edtended memory card), ban son rabuwa da ita saboda ma’adanar wayar, ko akwai wayar da ke da irin wannan nau’in ma’adana? – 08036799735
Wa alaikumus salaam, a gaskiya har yanzu ban ci karo da wata wayar salula mai dauke da nau’in ma’adanar SonyEricsson W800i ba, domin tsohuwar waya ce. Tun shekarar 2005 aka kera wayar. Haka ma ma’adanar, tsohuwar yayi ce; yanzu an daina kera ire-irensu. A duk sadda kwanaki suka ci gaba da maimaituwa, kayayyakin kimiyyar sadarwa na dada tsukewa ne zuwa kanana, saboda samun saukin mu’amala da su. Da fatan ka gamsu.