Amsoshin sakonnin masu karatu (4)

Assalaamu alaikum Baban Sadik, don Allah mene ne bambancin da ke tsakanin wayar salula nau’in Symbian, da Android, da kuma Windows?  Ka huta lafiya.  –  Ibrahim Abba: 08030943253 Wa alaikumus salaam, Malam Ibrahim barka da warhaka.  Da farko dai wadannan  sunaye da ka kawo duk sunayen babbar manhajar wayar salula ne, wato Mobile Phone Operating […]

Amsoshin sakonnin masu karatu (4)

Na’urar kwamfutar tafi-da-gidankaAssalaamu alaikum Baban Sadik, don Allah mene ne bambancin da ke tsakanin wayar salula nau’in Symbian, da Android, da kuma Windows?  Ka huta lafiya.  –  Ibrahim Abba: 08030943253

Wa alaikumus salaam, Malam Ibrahim barka da warhaka.  Da farko dai wadannan  sunaye da ka kawo duk sunayen babbar manhajar wayar salula ne, wato Mobile Phone Operating Systems, wadanda a wannan zamani ake ji da su a matsayin manyan manhajojin da wayoyin salular zamani ke amfani da su wajen aiwatar da sadarwa ta kowace hanya. Babbar Manhajar Symbian (Symbian OS), ita ce babbar manhajar wayar salula da wayoyin salular kamfanin Nokia da Samsung da LG suka yi amfani da ita cikin wayoyinsu a shekarun baya.  Asalin kamfanin da ya gina wannan babbar manhajar waya shi ne kamfanin Symbian Incorporated.  Daga baya kamfanin Nokia ya sayi kamfanin baki daya, har zuwa shekarar 2010, sadda ya fitar da babbar wayarsa ta Nokia N8, inda a karshe ya daina amfani da wannan babbar manhaja, ya koma amfani da babbar manhajar Asha, da Windows Mobile Operating System na kamfanin Microsoft.  Zuwa shekarar 2016 za a daina baiwa wayoyin salula masu amfani da babbar manhajar Symbian tagomashi, saboda an daina kera wayoyi masu amfani da ita.
Babbar manhajar Android kuma na kamfanin Google Incorporated ne da ke kasar Amurka, ta hadin gwiwa da wasu kamfanonin waya da harkar sadarwa kusan 10.  Tana daga cikin shahararrun babbar manhajar wayar salula da ake ji da su a duniya a yau.  Sadda kamfanin Nokia ya saye kamfanin Symbian da ke baiwa sauran kamfanonin waya irin su Samsung da LG da Motorola lasisi, sai suka koma kan wannan babbar manhaja ta Android. Ga dukkan alamu, wannan na daga cikin abin da ya daga su, har a karshe suka shallake kamfanin Nokia a kasuwar wayar duniya baki daya. Nau’in wannan babbar manhajar waya dai ita ce Android Jelly Bean 4.3.
Ita kuma babbar manhajar waya ta Windows Mobile na kamfanin Microsoft ne da ke kasar Amurka, wato babban kamfanin kera manhajar kwamfuta da ya fi kowanne girma da kudi da tasiri a harkar sadarwar zamani a duniya ke nan. Wannan babbar manhaja a halin yanzu tana kan manyan wayoyin salula na kamfanin HTC, da Nokia. Kuma galibin wayoyin salula na kamfanin Nokia da ake ji da su a duniyar yau irin su Lumia 1020, da Lumia 920, da Lumia 720, da Lumia 620, da Lumia 520 duk suna dauke ne da wannan babbar manhaja ta Windows Mobile.  A halin yanzu wannan kamfani na Microsoft ya saye bangaren kera wayoyin salular kamfanin Nokia baki daya. Wannan ke nuna cewa nan gaba duk nau’ukan wayoyin salula masu dauke da sunan kamfanin Nokia za su rika zuwa ne da babbar manhajar Windows Mobile.
Bambancin da ke tsakanin wadannan manhajoji dai a fili yake, duk da cewa akwai abin da ya hada tsakaninsu.  Abin da ya hada tsakaninsu shi ne, dukkansu manhajojin wayar salula ne masu dauke da siffofin da ke baiwa wayar salula dabi’un kwamfuta, wato Smartphone.  Ire-iren wadannan dabi’u kuwa su ne; manhajar Imel dawwamammiya mai iya isar da sakonnin Imel ga mai waya nan take ba sai ya shiga manhajar ba.  Sai manhajar hadawa da tarawa da kuma tura bayanai masu inganci, irin su hanyoyin karanta jaridu, da shafukan abota – irin su Facebook, da Google+, da Instagram da sauransu – da nagartacciyar fasahar Bluetooth, da nagartattun hanyoyin aika sakonnin tes da hotuna da bidiyo, da kuma hanyoyin mu’amala da kwamfuta kai tsaye, musamman ta hanyar tsarin Mini USB Ports, sai uwa uba nagartacciyar hanyar sadarwa ta Intanet.
Abin da ya raba tsakaninsu kuma shi ne; kowanne daga cikinsu na da wasu masarrafai ko tsare-tsare wadanda suka kebanci kamfanin wayar da ya kera su.  Misali, babbar manhajar waya ta Android da ke kan wayar salula na kamfanin Samsung, da wanda ke kan wayar salula na kamfanin LG, asalin tsarinsu daya ne. Amma kowannensu na da wasu masarrafai da tsare-tsare da suka bambanta shi da wayar da wani kamfani daban ya kera ba shi ba.  Haka abin yake a bangaren Windows Mobile, da bangaren babbar manhajar Symbian, duk da cewa an daina amfani da ita a halin yanzu. Duk inda ka ga Symbian a yau, to, a tsohuwar waya ce.
A bangaren babbar manhajar Android, akwai masarrafai nau’uka biyu. Akwai masarrafan babbar manhajar, kamar su rajistar lambobi (Contacts), da manhajar sakonnin tes (Messages), da tsarin kira (Phone), da cibiyar masarrafai – na kyauta da na kudi – (Google Play Store), da dai sauransu. A daya bangaren kuma akwai masarrafan kamfanin da ya kera wayar.  Idan Samsung ce wayar, za a samu cibiyar masarrafar kamfanin Samsung (Samsung Apps), da cibiyar hirar ga-ni-ga-ka (Chat On) da dai sauransu.  Haka abin yake a bangaren wayoyin salula kirar kamfanin LG, da HTC da dai sauransu, wadanda ke dauke da babbar manhajar Android.
Idan muka koma bangaren Windows Mobile kuma za mu samu kusan dukkan masarrafan da ke cikin wayar duk na kamfanin Microsoft ne. Idan ka saba amfani da kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Windows, za ka ga duk manhajojin da ka saba amfani da su a kwamfuta, duk suna nan a cikin wayar, sai dai nau’insu ne ya bambanta. Ma’ana wadanda ke wayar salula an kera su ne don a rika amfani da su a kan wayar.  Sai kuma babbar cibiyar masarrafar kamfanin waya.  Misali, idan Lumia ce, za ka samu babbar cibiyar masarrafan kamfanin Nokia, wato: Nokia App Store.
Bayan wadannan manyan manhajojin wayar salula, akwai Asha ta kamfanin Nokia, da iOS na kamfanin Apple, da BlackBerry OS da BlackBerry 10, duk na kamfanin Research In Motion da ke gab da durkushewa a halin yanzu. Akwai kuma wadanda ake sa ran za su bayyana nan ba da jimawa ba. Daga ciki akwai Firefod OS na kamfanin Mozilla Foundation, da kuma Ubuntu Touch OS na kamfanin Canonical, wadanda suka samar da Ubuntu Operating System na kwamfuta, wanda kyauta ne a halin yanzu.  A baya akwai wadanda suka kwanta dama wajen sama da 50, saboda wucewar zamani.  Da fatan ka gamsu.

Salaamun alaikumu, ina fatan kana cikin koshin lafiya tare da iyali.  Ina daya daga cikin masu yabawa da kuma farin ciki da shafinka na kimiyya da kere-kere (shafi na 32) a jaridar Aminiya.  Ina amfana matuka da dimbin  iliminka da baiwarka, a matsayina na dalibin harshen Hausa kuma mai sha’awar ilimin fasahar sadarwa ta zamani.  Tabbas!  Shafin ya dade da zama makarantar kimiyya da kere-keren AMINIYA ga Amintattun daliban Hausa da masu sha’awar Hausa da kimiyya da kere-kere.  Allah Ya kara sani da daukaka, amin.  –  Aminu M. B. Umar, birnin Zariya: 08081224683

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Aminu. Na gode matuka da wannan sako naka. Kuma ina farin ciki matuka da ya zama abin da nake yi yana yin tasiri ta hanyoyi da wuraren da ban taba tunani ba. Bayan wannan tabbaci naka, a baya na samu sakonni da dama makamantan wannan. Akwai daliban harshen Hausa da ke wasu daga cikin manyan Jami’o’in Arewacin Najeriya da suka bukaci kusan dukkan kasidun da na rubuta a baya kan wasu fannoni, don amfani da su cikin rubuce-rubucensu na karasa karatu. Allah Ya sa mu dace baki daya, Ya kuma amfanar da mu abin da muke karantawa a dukkan fannonin ilimi, amin.  

Assalaamu alaikum, da fatan alheri, da kuma fatan samun babban rabo duniya da lahira.  Don Allah ina son sanin yadda ake neman bayanai ta Intanet; idan na je Google ko Wikipedia misali, zan shigar da kalmar da nake neman bayani ne ko kuwa akwai wani tsari da ake bi?  – Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Tunshama kuarters, Kano: 0809558832

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Yahuza. Lallai neman bayanai a Intanet yana da tsari na musamman.  Abu na farko kuwa shi ne ka san me kake nema? Me kake so?  Wadanne irin bayanai kake nema? Wadanne kalmomi za ka yi amfani da su don samun fa’ida kan haka?  Sannan a ina za ka samu manhajar da za ta saukake maka neman wadannan bayanai?  Dukkan wadannan tambayoyi suna bukatar amsa gamsasshiya, domin da zarar ka kuskure su, tun nan za ka rasa abin da kake so. Da farko dai, bayan ka haddade nau’ukan bayanan da kake nema, sai ka doshi gidan yanar sadarwa na musamman da aka tanada don neman bayanai. Wannan gidan yanar sadarwa yana dauke ne da manhajar neman bayanai cikin sauki, wadda ke iya fahimtar irin abin da kake nema ta hanyar kalmomi ko lambobi ko alamun da ka yi amfani da su ko ka shigar. Shahararre daga cikin ire-iren wadannan gidajen yanar sadarwar neman bayanai kuwa kamar yadda ka sani, shi ne gidan yanar sadarwar Matambayi Ba Ya bata na kamfanin google, wato: Google Search Engine. Idan ka shiga sai ka sa kalma, ko kalmomi, ko jumlar da ke dauke da irin bayanan da kake so. Ka kiyaye, kada ka yi amfani da doguwar jumla, domin ba za ka samu fa’ida ba. Haka idan shafin Babban kamus din Intanet ka shiga, wato Wikipedia, za ka ga inda aka tanadi hanyar shigar da kalma ko kalmomi don tambayar irin bayanan da kake so. Sai ka shigar a wurin, ka matsa maballin “Enter” da ke jikin allon shigar da bayanan kwamfutarka, nan take za ka samu amsa. Allah Ya sa a dace.
Assalaamu alaikum, barka da warhaka.  Allah Ya taimaka.  Don Allah ina so a taimaka a turo mini bayani kan “Samuwar Bacci da Mafarki a Mahangar Kimiyya.”  Ga adireshin Imel dina: [email protected]  –  08037156498

Wa alaikumus salaam, barka da warhaka. Sai ka/ki duba jakar Imel dinka/ki, na tura tuni. Allah Ya sa a dace, Ya kuma amfanar da mu abin da muke karantawa. Na gode.